✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wasan dambe ke gudana a Zariya

Aminiya ta ziyarci gidan wasan dambe gargajiya wanda ake yi a kowane yammaci a filin wasan kwallon kafa da ke layin Club Street a karamar…

Aminiya ta ziyarci gidan wasan dambe gargajiya wanda ake yi a kowane yammaci a filin wasan kwallon kafa da ke layin Club Street a karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna. Wakilinnamu ya tarar da masu sha’awar kallon wasan dambe sun yi layi suna karbar tikitin shiga filin wasa don su kashe kwakwatar idanu.  Ga yadda ya kalato mana labarin:  

Gidan damben ya tara shahararrun ‘yan wasa daga bangaren Arewa da kuma yankin Kudu, kuma manyan ‘yan wasa ne daga sassan biyu suka goge raini a tsakaninsu.   Wasan farko an yi shi ne tsakanin Autan Fafa daga Arewa da Shagon Kunnari daga Kudu, kuma tun a zagaye na farko aka yi kisa a wasan, inda Shagon Kunnari daga Kudu ya kashe Autan Fafa daga Arewa.

Sai wasa na biyu a tsakanin shugaban tawagar ’yan wasan daga Kudu mai suna Ali kwara, da kuma shugaban tawagar ’yan wasa daga Arewa mai suna Bahago Sogo daga Kudu. Wasan ba kisa domin wasan ya tashi a karshe ne da kokuwa. 

Bayan kammala wasan wakilinmu ya yi hira da ’yan wasan daya bayan daya kuma ga abin da suke cewa:   Na farko, “Sunana Ali kwara wanda aka fi sani da dan kwara mai dambe kuma ni asalina mutumin Jihar Barno ne kuma na kammala makarantar sakandire, kuma ni dambe ba gado na yi ba da rana tsaka na shiga wasan dambe saboda sha’awa, kuma na fara harkar  dambe a shekaru sha biyar da suka wuce watau a 2003 ga shi ya zame mun jari, kuma duk kasar nan babu inda ban shiga ba a harkar dambe, kuma na wakilci Jihar Jigawa a shekarar 2011. An je bikin nuna al’adu (Festibal) da ni a garin Fatakwal.  A  wasan damben kasa kuma na lashe lambar yabo (Medal) domin na kashe Bahagon Nabacirawa a dambe na na farko, kuma na biyu na kashe dan Kankiya, Allah Ya ji kansa ya rasu.   Sai dambe na uku kuma muka yi cin kunaman kwadi da Dangurumada na kashe shi aka ce ba kisa ba ne saboda suna da daurin gindi. To na samu lambar yabo (Medal) hakan ta sa na yi hannu da Gwamna Alhaji Sule Lamido na Jihar Jigawa ya ba ni kyautar kudi Naira dubu dari tare da sa ni a cikin wadanda ke karbar albashi a Jihar na tsawon shekara biyar.

Haka kuma Aminiya ta sake jin ta bakin Shugaban tawagar Arewa mai suna Bahagon Sogo ya ce,’’ Ni dan Kaduna ne kuma ina wakiltar Arewa ne, kuma a harkar dambe kusan na zagaye Najeriya a sai dai Allah bai sa na taba lashe wata kyauta ba a duk wasannin da na buga sai dai ina sa ran samun nasara a nan gaba, kamar yadda Hausawa kan ce in da rai, da rabo.

Mai masaukin ’yan damben Muhammadu Anas wanda aka fi sani da Anas Sadauki dan Sarkin Fawa, kuma mai mukamin  Ma’ajin kungiyar ’yan dambe na kasa  ya shaida wa wakilinmu cewa:  “Harkar dambe a yanzu ba wai ta zama abin sha’awa ba ce kawai a’a harkar dambe ta koma harkar sana’a domin in ka duba za ka ga a yanzu dan dambe ya mallaki iyali, tare da gina gida, har ma da mallakar mota. A harkar kuma ga nishadantarwa. Ya kara da cewa yanzu an inganta harkar dambe domin gaba daya yanzu an dunkuleta waje daya mun zama abu daya. Akwai shuagabanni na kasa, kuma duk bayan wata uku ana zagayawa jiha-jiha domin haduwa da juna ana wasa kuma ana sa gasa mai tsoka sannan ga sada zumunci a tsakani.