✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wani matashi ya rataye kansa a Jigawa

Matashin ya yi amfani da wandonsa wajen yin igiyar da ya rataye kansa.

Wani matashi mai shekara 25 a duniya da ke kauyen Zangon Maje a Karamar Hukumar Taura a Jihar Jigawa, ya rataye kansa.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar, ASP Lawan Shi’isu Adam ne, ya tabbatar wa da manema labarai faruwar lamarin a garin Dutse, a ranar Talata, inda ya ce lamarin ya faru ne ranar Litinin.

Kakakin ya ce matashin an yi tsammanin ya bata tun farko, sai daga bisani aka hangi gawarsa rataye a jikin wata bishiya, inda yayi amfani da wandon jikinsa a matsayin igiya.

Hakimin Kwalam, Alhaji Mutakka Uba ne, ya fara shaida wa jami’an ’yan sandan Jihar faruwar lamarin, inda su kuma suka je wajen don gudanar da bincike.

Matashin ya bar gida tun da safiyar ranar Litinin, inda ba a san inda ya shiga ba.

Shi’isu ya kara da cewa daga bisani ne aka gano matashin ya rataye kansa a bayan garin Zangon Maje.

Kakakin ya ce da samun wannan labari aka tura jami’an ’yan-sanda suka je wajen, inda suka dauko gawar suka kai ta babban asibitin Ringim, inda likita ya tabbatar da rasuwar matashin.

Kazalika, kakakin ya kara da cewa daga baya sun mika wa ’yan uwan mamacin gawar domin yi masa jana’iza.

Har wa yau, ya ce suna gudanar da bincike, amma ya zuwa yanzu ba su gano hannun wani a mutuwar matashin ba.