Abel Danjuma matashi ne a kauyen Zankan Sarki da ke masarautar Godogodo a karamar hukumar Jama’a ta jihar Kaduna, kuma baya ga noma ba shi da wata sana’a da ta fi farauta.
Ranar Talata da rana ya shiga daji don yin farauta, sai kwatsam ya ga wasu ’yan bindiga sun tare wata mota a kusa da garin Jagindi.
“Motar karama ce daga direban sai ’yan mata guda biyu a ciki”, inji Dagacin Zankan, Christopher Madaki.
Bayan sun tare motar ne mutanen, wadanda Abel ya yi zargin masu satar mutane don neman kudin fansa ne, suka fito da ’yan matan suka shiga da su daji, bayan da direban da ke jansu ya samu ya tsere.
Ganin haka sai Abel ya yi waya kauyensu ya shaida wa wasu abokansa abin da ke faruwa.
“Mun samu labarin abin da ke faruwa ne”, inji wani dan uwan Abel, Bitrus Jatau, “lokacin da ya bugo waya bayan ya ga abin da ke faruwa”.
A nan ne matasan Zankan din suka yi gangami Abel ya yi musu jagora dauke da adduna da sanduna suka bi sawun masu satar mutanen; suka kuwa yi sa’a suka same su suna waya da dangin ’yan matan suna cewa sai an bayar da Naira miliyan 10 za su sake su.
A nan ne fa matasan na Zankan Sarki suka fatattaki barayin suka kuma kubutar da ’yan matan wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa Gombe daga Abuja.
Bayan faruwar wannan lamari ne dai da yamma Abel da abokansa biyu, Waje Henry Christopher da Dennis Christopher, wadanda ’yan uwan juna ne, suka koma dajin don su ci gaba da farautar su, sai barayin nan suka dirar musu da harbi da sara.
A nan dai Abel ya ce ga garinku nan bayan da aka harbe shi, abokan nasa kuma suka tsira da raunukan saran adda, yanzu haka kuma suna kwance a asibiti.
Ranar Alhamis ne dai shugaban karamar hukumar Jama’a Peter Danjuma Averick, ya bayyana Abel da cewa gwarzo ne, sannan ya jinjina wa matasan saboda sadaukar da rayukanasu da suka yi.
Shugaban karamar hukumar, wanda ya yi tir da abin da ya faru, ya kuma yi kira ga al’ummarsa da su samar da ’yan sintiri a tsakaninsu wadanda za su hada kai da jami’an tsaro don samar da muhimman bayanan da za su taimaka wajen kama ’yan bindigar da ke yawan kai hare-hare da sauran masu munanan ayyuka a yankin.
“Dole ne al’umma ta hada kai da jami’an tsaro mafi kusa da su don yakar masu aikata miyagun laifuffuka”, inji shi.
Mista Averick ya kuma ziyarci asibitin da aka kwantar da Henry da Dennis inda ya duba su.
Yankin da lamarin ya faru dai ya yi kaurin suna wajen kai hare-hare da satar mutane don neman kudin fansa.Bayan jajantawa iyalan, shugaban karamar hukumar ya kuma bayyana shi a matsayin gwarzon da ya rasa ransa a yayin kokarin wasu ‘yan mata biyu da wadanda ake zargi da masu garkuwa da mutane ne su ka shige daji da su inda ya gamu da ajalinsa bayan nasarar kwato ‘yan matan.