✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda tuhumar Babban Jojin Najeriya ta tada kura

A ranar Litinin da ta gabata ce Kotun Da’ar Ma’aikata ta dage zamanta na sauraron shari’ar tuhumar da ake yi wa Babban Jojin Najeriya Mai shari’a…

A ranar Litinin da ta gabata ce Kotun Da’ar Ma’aikata ta dage zamanta na sauraron shari’ar tuhumar da ake yi wa Babban Jojin Najeriya Mai shari’a Walter Onnoghen, kan kin  bayyana dukiyarsa.

Mai shari’a Walter Onnoghen wanda bai halarci kotun ba ana tuhumarsa ne da laifuffuka shida da suka shafi dukiyar da ya mallaka da yadda bai bayyana wadansu daga cikin kadarorinsa ba kamar yadda doka ta tanada.

A ranar da aka saurari karar, manyan lauyoyi 47 ne suka wakilce Babban Jojin.

Lauyoyin sun ce bai bayyana ba ne saboda ba a mika wa mutumin da suke karewa takardar sammaci a hannunsa ba. Wanda hakan ya sa kotun ta dage zamanta zuwa ranar Talata 22 ga Janairu

Alkalin Kotun Mai shari’a Danladi Umar, ya ce dole sai ya bayyana a gaban kotun da kansa, kafin a fara sauraron karar.

Ko da yake lauyoyinsa sun ce kotun ba ta da hurumin sauraron karar. Sun ce ba a bi ka’ida ba wajen gurfanar da shi kamar yadda BBC ya ruwaito.

A ranar 10 ga Nuwamban 2016 ne Shugaba Buhari ya rantsar da Onnoghen a matsayin Babban Jojin Najeriya.

Mun mika masa takardar sammaci a hannunsa- Jami’an Kotun CCT

Wani jami’in Kotun Da’ar Ma’aikata (CCT) wanda ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatar da cewa sun mika wa Babban Jojin takardar sammacin a hannunsa. Jami’in ya ce Babban Jojin Najeriyar ya amshi takardar sammacin, ya sa hannu a kai a ofishinsa da ke harabar Kotun Kolin, inda ya bayyana musu cewa dama yana jiransu.

Ya kara da cewa lokacin da za su kai masa takardar, sun samu rakiyar ’yan sanda domin saukake shiga inda yake domin mika sammacin, inda ya ce kila haka ne ya jawo rade-radin cewa Hukumar EFCC ta mamaye gidansa saboda ganin ’yan sanda a gidansa.

Kuma daga bisani Hukumar EFCC ta fitar da sanarwa cewa, “An jawo hankalin EFCC kan labarin karya da ake watsawa a shafukan sada zumunta cewa EFCC ta kama Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a Walter Onnoghen. Wannan ba komai ba ne face zuki-ta-malle daga wurin masu yada labaran karya. Muna so a san cewa EFCC ba ta je gidan Babban Jojin domin ta kama shi ba, kuma ba ta aike masa da gayyata game da hakan ba,” inji sanarwar.