✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda tuffa ke gyara fata

Shan tuffa guda daya a rana na magance cututtuka da dama, kuma yawan shan ta na jinkirta zuwan tsufa. Idan ana so a jinkirta tsufar…

Shan tuffa guda daya a rana na magance cututtuka da dama, kuma yawan shan ta na jinkirta zuwan tsufa.
Idan ana so a jinkirta tsufar jiki ba sai an kashe kudi mai yawa a kan mayukan da suke jinkirta tsufa ba, maimakon haka sai a sayi tuffa a rika sha. Yin hakan zai jinkirta tsufar jiki da ta fuska.
Tiffa na dauke da sinadarin bitamin C da na A.
A wannan makon mun muku yadda za ku yi amfani da tuffa don jinkirta tsufar fuska da ta jiki.
· Tuffa da zuma: Ku markada ko daka tuffa, sai ku zuba zuma cokali biyu, sannan ku kwaba sosai. Daga nan ku wanke fuska da sabulu kafin ku shafa a fuskarku ko jikinku. Sai ku wanke bayan minti 30. Yawan shafa wannan hadin zai sanya hasken fata.
· Ayaba da tuffa: Ayaba na dauke da sinadarin da ke gyara fata, tana kuma dauke da sinadaran bitamin A da B da kuma C. Don haka ne ayaba yake gyara fata mai gautsi. Ku bare ayaba, daga nan ku jajjaga ta, sannan ku hada ta da markadaddiyar tuffa, sai ku kwaba su sosai, daga nan ku shafa a fuska. Za ku iya zuba zuma ko kindirmo kadan a wannan hadin. Za ku shafa zuwa tsawon minti 30 kafin ku wanke.
. Lemon tsami da tuffa da kindirmo: Wannan hadin na sanya laushi da santsin fuska. Ku markada tuffa, sannan ku matsa ruwan lemon tsami da kindirmo, daga nan ku gauraya sosai. Bayan kun gauraya sai ku shafa a fuska da wuya, sannan ku wanke bayan minti 20. Wannan hadin zai sanya fatarku ta yi haske.