✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda tsohuwar gaba tsakanin Tibi da Jukun ta hana Taraba zaman lafiya

Mutane da dama aka hallaka a farkon watan da muke ciki sakamakon wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilun Tibi da Jukun a wasu…

Mutane da dama aka hallaka a farkon watan da muke ciki sakamakon wani sabon rikici da ya barke tsakanin kabilun Tibi da Jukun a wasu kauyukan hanyar Wukari da Kwatan Sule a Karamar Hukumar Wukari da ke Jihar Taraba. A yayin rikicin an kone gidaje da dama da yin munanan raunuka a tsakanin kabilun biyu.

Daga bisani rikicin ya fantsama zuwa makwabciyar Jihar Benuwai inda aka kashe mutum 10 a wani sabon harin da aka kai kauyen Baase da ke Karamar Hukumar Ukum. Kauyen da ke kan iyakar Benuwai da Taraba. Kabilun biyu kusan kullum suna fada da juna ne a kan kasar noma da kuma siyasa tun kimanin shekara 70 da suka gabata ba tare da an samo hanyar warware rikicin ba.

 

Dalilan da suka haddasa rikicin na yanzu

Ricikin baya-bayan nan a tsakanin kabilun guda biyu kamar yadda binciken Aminiya ya gano ya faro sakamakon sabanin da aka samu a tsakanin matasan kabilar Tibi da Jukun a garin Kente da ke Karamar Hukumar Wukari a ranar Litinin 2 ga Afirilun nan. Kabilar Jukun sun yi zargin cewa wadansu matasan kabilar Tibi sun kai wa wata mace ’yar kabilar Jukun farmaki yayin da matar ta keta wani umarni da matasan kabilar Tibi suka bayar na hana kawo kowane irin kaya domin cin kasuwar garin na Kente don sayarwa. An rawaito cewa yayinda matasan kabilar Jukun suka yi yunkurin daukar fansa sai rikicin ya sauya salo inda ya janyo asarar rayukan mutum biyu daga nan ne rikicin ya fantsama zuwa makwabtan kauyuka.

Wasu bayanan da Aminiya ta samu sun ce kowace kabila daga cikinsu tana da mayakan da suke dauke da miyagun makamai. Kuma rikicin ya munana ya koma babbar fafatawa na wasu awanni, inda aka kone gidaje da dama ciki har da ginin Makarantar Sakandaren Jeka-ka-Dawo ta Gwamnati da ke Kente sannan maharan suka sace wasu kayayyaki da suka hada da amfanin gona da dabbobi, labarin da Shugaban Karamar Hukumar Wukari, Mista Daniel Adi ya tabbatar da aukuwarsa. Kuma ya ce an kashe mutum 10 sannan an kone kauyuka da dama kurmus.

Mayakann kabilun biyu daga baya sun koma ga hare-haren sari-ka-noke da junansu. Kuma Aminiya ta samu rahoton cewa wasu kauyuka 10 da suke karkashin Mazabar Kente an kone su kurmus, haka zalika ’yan bindigar sun toshe hanyar da ta tashi daga Wukari zuwa Kwatan Sule a Jihar Benuwai.

 

Adadin rayukan da aka rasa    

Wakilinmu ya ce yana da wuya a tabbatar da adadin mutanen da aka hallaka a yayin rikicin na bayan nan. Amma gaggauta tura jami’an tsaro da akayi ta taimaka wajen rage asarar rayuka a tsakanin kabilu biyu. Wata majiya ta shaida mana cewa akalla mutum 20 sun rasa rayukansu a rikicin kuma mutane da dama sun jikkata a tsakanin kabilun biyu.

 

Martanin shugabanni

Wani sannanen dan asalin garin Kente Cif Dibid Kente ya ce abin takaici ne a ce kabilun da aka san su da zaman lafiya, sun dauki makamai suna yakar junansu.

Ya cigaba da cewa tun bayan rikicin da ya faru a tsakanin kabilar Tibi da Jukun a 1991 suna zaune da juna lafiya, ya ce rikicin da ya faru abin takaici ne kwarai da gaske.

Cif Kente ya ce mutane da dama sun rasa muhallansu saboda rikicin yayin da wadansu suke cikin matsananciyar bukatar taimakon kayyayaki da maganguna. Ya yi kira ga Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa da gwamnatin Jihar Taraba su kai dauki ga wadanda rikicin ya rutsa da su.

Shugaban Matasan Kabilar Jukun na Kasa Kwamared Zando Hoku, yayin da yake tattaunawa da wakilinmu a kan rikicin da ya faru ya ce rikicin ya samo asali ne a kan fili (gonaki). Ya ce ’yan kabilar Tibi daga Jihar Benuwai sun kasance suna zuwa gonakin ’yan kabilar Jukun sannan daga bisani su yi kokarin mallake gonakin.

Zando ya ce ’yan kabilar Jukun koyaushe mutane ne da suke son zaman lafiya da makwabtansu, amma ba za su amince da mamaye musu gonaki da kabilar Tibi ke kokarin yi ba.

Sanata mai wakiltar Kudancin Taraba Mista Emmanuel Bwacha, ya bayyana alhininsa a kan wannan bala-hira, inda ya ce koda yake rikicin ba yaki ba ne da ya taba faruwa a baya tsakanin kabilun biyu, ya ce wadansu mutane ne da ba sa son zaman lafiya suke amfani da wannan dama domin su sace dukiyoyin jama’a.

Shugaban kabilar Tibi Mista Dibid Oche, ya yi watsi da zargin da ake yi wa ’yan kabilarsa a kan rikicin da ya faru ta hanyar farmaki da aka ce an kai wa wata mata ’yar kabilar Jukun. Ya ce rikicin ya samo asali ne daga siyasa a tsakanin kabilun biyu tun a 1950. Ya ce rikicin yana da alaka da siyasa. Ya ci gaba da cewa kabilar Jukun suna kokawa dangane da yawan ’yan kabilar Tibi a Jihar Taraba wannan dalilin ne ya sa kabilar Jukun tayar da rikici.

Ya yi kira ga shugabannin kabilar Jukun da gwamnatin Jihar Taraba su tsawatar musu, inda ya ce ’yan kabilar Jukun ne suke kashe ’yan kabilar Tibi sannan su sace musu dukiyoyinsu. Ya ci gaba da cewa an tilasta wa ’yan kabilar Tibi kimanin dubu 20, ficewa daga Wukari zuwa gudun hijira a Jihar Benuwai da ke makwabtaka da jihar.

A cewar Mista Oche, duk ’yan kabilar Tibi da suke garin Wukari a hanyar Ibbi sun tsere sun bar gidajensu, yayin da aka lalata gidajen kuma aka sace dukiyoyinsu. Ya ce ’yan kabilar Jukun sun debo hayar sojojin haya domin kashe ’yan kabilar Tibi a garin Bisia yayin da aka kashe ’yan kabilar Tibi da dama.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Taraba, DSP Dibid Misal, ya ce komai ya lafa a yankunan da rikicin ya yi tsamari, ya ce an tura jami’an tsaro yankunan da rikicin ya faru domin gudanar da sintiri na tsawon awa 24, yayin da sarakunan gargajiya da ke garin Wukari hade da shugabanni kabilar Tibi da wadansu manyan jami’an gwamnatin Jihar Taraba suka hadu a garin Wukari domin tattauna hanyar da za a samar da dawamamman zaman lafiya a yankin.

Ya ce ba su da wata masaniya ko an kama wadansu daga cikin wadanda ake zargi, inda ya ce ahalin yanzu ’yan sanda sun dukufa wajen dawo da zaman lafiya a yankin.