Mutane da ba yawansu bai taka kara ya karya ba ne suka tarbi Shugaban Buhari a ziyarar aiki da kai a Jihar Kano ranar Liinin.
Sabanin yadda a baya Kanawa kan yi dandazo don tarbar Buharin, a wannan karon mutanen gari sun ci gaba ne da harkokinsu na yau da kullum, ba tare da mayar da kula ziyarar tasa ba.
- DSS ta cika hannu da ma’aikatan bankin da ke cuwa-cuwar sabbin kudade
- Wata Sabuwa: Dabdalar da ta wakana a Kannywood a makon jiya
Hasali ma, a wannan karon, ’yan tsirarun da suka fito kan tinuna, yawancinsu kananan yara ne almajirai da kuma ’yan makarantar firamare.
Buhari ya je Kano ne domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin jihar da ta tarayya suka kammala a sassan jihar.
Tun kafin zuwan nasa, da farkon gwamnatin jihar ta shawarce shi da ya dakata saboda dalilai na tsaro, amma ba a jima ba, aka samu labarin cewa zai je jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa tun a jajibirin ziyarar shugaban kasar aka tsaurara matakan tsaro a birnin Kano domin kaddamar da ayyukan.
Sabanin yadda a baya Buhari kan yi zagaye a cikin jerin gwanon motoci, ziyararsa ta ranar Litinin ta zo da sabon salo, inda ya rika shawagi a cikin helikwafta zuwa wasu daga ckin uraren da ya kaddamar da ayyuka.
Aminiya ta gano cewa manema labarai ba su samu cikakken bayanin jerin yadda zai kai je wuraren kaddamar da ayyukan ba, sai dai kirdado maneman labarai suka rika yi.
Ayyukan da shugaban ke kaddamarwa sun hada da cibiyar kula da masu fama da cutar kansa da ke Asibitin Kwararru na Muhammadu Buhari da ke Giginyu, Tashar Jiragen Ruwa ta Kan Tudu da ke Dala.
Sauran Tashar Wutar Lantarki mai karfin Megawat 10 da ke Zawaciki, da kuma Cibiyar Bayanai ta Jihar Kano da ke Sakatariyar Audu Bako, da kuma Rukunin Gidajen Gwamnatin Tarayya a Gandun Sarki.