Wani abin da ya zama kamar al’ada bayan kowanne babban zabe a Najeriya shi ne komawar Gwamnonin da wa’adinsu na mulki ya kare zuwa Majalisar Dattijai a matsayin Sanatoci.
A cewar wasu jama’a, Majalisar ta dauko hanyar zama matattarar tsofaffin Gwamnonin da za su dawwamar wa kansu kudaden alawus da na fansho ribi biyu.
- Shugaban Karamar Hukuma ya gwangwaje Hakimai 5 da motoci a Kaduna
- LABARAN AMINIYA: An kama Ike Ekweramadu da matarsa a Landan
Wasu kuma na ganin cewa hakan ba zai ba su damar samar wa da talaka dokokin da suka shafe shi ba. Saboda kare muradunsu kawai su ke yi.
Tuni dai wasu kungiyoyi ke ta kiraye-kirayen dakatar da wannan kaka-gidan da gwamnonin ke yi a majalisar domin ba wasu dama su ba da ta su gudunmawar ta gina kasa.
Aminiya ta yi nazarin jerin sunayen tsofaffin Gwamnonin da a yanzu suke a majalisar dattijai da Jihohin da suka fito;
- Kalu Orji – Abiya
- Gabriel Suswan – Binuwai
- Kashim Shetima – Borno
- Samuel Egwu – Ebonyi
- Nnamani Chimaroke – Enugu
- Danjuma Goje – Gombe
- Ibrahim Shekarau – Kano
- Kabiru Ibrahim Gaya – Kano
- Adamu Alliero – Kebbi
- Ibukunle Amosun – Ogun
- Aliyu Wammako – Sakkwato
- Ibrahim Geidam – Yobe
- Rochas Okorocha – Imo
Ga kuma jerin sunayen Gwamnoni masu ci da suke zawarcin kujerar Sanatocin da zaran wa’adinsu na nulkin ya kare.
- Okezie Ikpeazu – Abiya
- Ifeanyi Ugwuanyi – Enugu
- Dairus Ishaku – Taraba
- Gbenga Daniel – Ogun
- Abubakar Sani Bello – Neja
- Simon Lalong – Filato
- Samuel Ortom – Binuwai
- Dave Umahi – Ebonyi
- Aminu Tambuwal – Sakkwato
- Atiku Bagudu – Kebbi
Wannan kuma jerin sunayen wasu tsofaffin Gwamnonin da su ka yi Gwamnoni a da, da kuma Jihohin da suka fito.
- Umar Tanko Almakura – Nassarawa
- Saminu Turaki – Jigawa
- Adams Oshiomhole – Edo
- Ibrahim Dankwambo – Gombe
- Ali Modu Sheriff – Borno
- Rabiu Musa Kwankwaso – Kano
- Abdullahi Adamu – Nasarawa
- Ahmed Makarfi – Kaduna