✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda tsadar haraji ta sa ’yan Najeriya komawa sayen motocin da suka yi hatsari

A wani bincike na musamman da Aminiya ta yi, ta gano karin kudin harajin shigo da motocin da aka yi amfani da su a kasashen…

A wani bincike na musamman da Aminiya ta yi, ta gano karin kudin harajin shigo da motocin da aka yi amfani da su a kasashen waje ya tilasta wa diloli komawa shigo da wadanda suka yi hatsari.

Dilolin dai sun bayyana mana cewa an rubnaya kudin harajin motocin kan na baya ne tun a watan Janairu, sakamkon dabbaka sabon tsarin bada lambar shaidar motoci ta VIN da hukumar Kwastam ta yi.

To sai dai wannan tsari, a cewar Shugaban Dilolin Motocin ketaren na kamfanin  United Berger, Cif Metche Nnadiekwe, wannan tsarin an kirkire shi ne kawai domin hana masu karamin karfi mallakar mota a kasar.

“Idan ba haka ba, ta yaya motar da harajinta a da bai fi N600,000 ba yanzu za a ce sai ka biya masa N2.5m, kuma idan aka samu jinkiri a bayar da VIN ma ta samu matsala, kai za ka biya mata kudin gyara?

“Ka ga idan ka hada da kudin gyara da na haraji fa ya zama N2.6m ke nan, to nawa za ka kara ka sayar mutane su iya siya?

“Shi ya sa yanzu sai ka yi wata ma ba ka yi ciniki ba, saboda mota ta yi dan karen tsada”, in ji shi.

Shi ma dai wani dillalin mota na cikin gida Ademola Lukman, ya ce ’yan Najeriya tuni suka koma sayen motar da aka yi hadari da ita saboda saukinta.

“A hankali muatne sun fara komawa wadanda aka yi hatsari da su, don sun dan fi saukin kudi, ka ga alama ce ta gwamnati ta sake duba wannan dokar, saboda al’ummarta”, in ji shi.

A nasa bangaren, Kakakin Hukumar Kwastam din na Kasa, DC Timi Bomodi, ya ce harajin hukumar na kunshe cikin dokokin Gwamnatin Tarayya, dabbakawa ne kawai nasu.

“Daga cikin sabuwar dokar, bayan batun haraji ma, akwai na hana shigo da motocin da aka yi amfani da su fiye da tsawon shekaru 10, kuma dilolin nan da kansu suka bukaci tsarin biyan ya zama ta na’ura.

“Don haka ban ga dalilin wannan koke ba.
“Duk mai korafi ya je ya mika shi ga gwamnati, ba mu ba”.