Burodi yana cikin abinci mafiya saukin sarrafawa ko samu ga talaka a kasar nan.
Wannan ya sa tsadarsa a daidai wannan lokaci da tsadar kayan abinci da na masarufi ke hauhawa take dada jefa talakawa a cikin kunci.
A wajen Olatunde Alausa, da yake gidajen burodi biyu; daya a Pleasure, daya kuma a Oke Odo a babbar hanyar Legas zuwa Abeokuta, abubuwa hudu ne suke jawo hauhawar farashin burodin.
“Dole tsadar kayan sarrafa burodin ta jawo tsadarsa,” inji shi, inda ya ce yanzu ribar da ake samu ta yi kasa da kashi biyar saboda tsadar kayan sarrafa burodin.
Ya ce, “Hakan na faruwa ne saboda babu ka’ida wajen sayar da burodin.
“Ya zama dole mutum ya ci gaba da gudanar da harkokinsa yadda suke kawai.
“Amma babbar matsalarmu ita ce ba mu da ka’idoji a harkar, kowa zai iya bude gidan burodi, ya fara kasuwancinsa,” inji shi.
Ya kara da cewa dole ya daina ba wasu burodi saboda ya rage yawan basussukan da yake bi.
“Mu da muke sayar da burodinmu kai-tsaye ga mutane, muna dan samun sauki idan aka kwatanta da manyan gidajen burodin da suke ba ’yan kasuwa su sayar.
“Nakan ba wadanda suke son fara harkar burodi shawara cewa su rika sayar da burodinsu kai-tsaye saboda babu riba sosai, sannan a lokuta da dama ’yan kasuwar ba sa dawo da kudaden cikin lokaci.
“Sai matsalar ta zama biyu; ga ta tsadar kayan hada burodin, ga kuma ta ’yan kasuwa,” inji shi.
Ya ce tuni ya rage nauyin burodinsa saboda tsadar.
Ya ce tsadar man dizel ma ta taimaka wajen tsadar burodin, inda ya ce, “A farkon bana, muna kashe Naira 7,000 ne kullum wajen sayen man dizel, amma yanzu muna kashe Naira 40,000 a kullum.”
Ya ce idan gwamnati ta magance matsalar wutar lantarki, za a samu sauki a wannan bangare.
Sai dai ya ce bai taba rage ma’aikata ba, amma ya tabbatar da cewa mutane da dama da suke sayen burodi a da, yanzu sun daina saboda tsadarsa.
Wannan matsalar ba Alausa kadai ta shafa, kusan dukkan masu gidajen burodi da Aminiya ta zanta da su, sun bayyana yadda tsadar kayan sarrafa burodin, irin su fulawa da sukari da man bota da sauransu suke jawo tsadar burodin.
Binciken Aminiya ya gano cewa a Jihar Legas da wasu manyan biranen kasar nan, farashin kayan sarrafa burodin ya yi matukar hawa zuwa kashi 150 ko 200 a tsakanin bara da bana.
A bara, ana sayar da kilo 50 na buhun fulawa a Naira dubu 19 ne, amma yanzu ya kai Naira dubu 29.
Sannan a daidai lokacin da fulawa ke kara tsada, haka sukari ma ke kara tsada. Haka bokitin man bota da ake sayarwa Naira dubu 10 a bara, yanzu ya koma Naira dubu 27.
Wannan tsadar ce ta sa Kungiyar Masu Gidajen Burodi da Kasuwancinsa ta The Premium Bread Makers Association of Nigeria (PBAN), ta so gudanar da yajin aikin sarrafa burodi da kasuwancinsa a watan Yulin bana, inda ta ce za ta yi hakan ne don nuna rashin jin dadinta kan hauhawar farashin kayan sarrafa burodin.
Shugaban Kungiyar, Emmanuel Onuorah da Kakakin Kungiyar, Babalola Thomas sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta daina karbar harajin kashi 15 a kan fulawa.
Sannan sun bukaci Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) ta rage kudin tara ta Naira dubu 154 da take karba idan gidan burodi ya yi nawar sabunta lasisinsa, sannan ta bukaci gwamnati ta ba mambobinta tallafi don bunkasa harkokinsu.
Yadda lamarin yake a jihohi
A Jihar Kano kamar sauran jihohin, gidaje da dama suna amfani da burodi domin karin kumallo saboda saukin hadi da kuma saukin farashinsa a da.
An saba ganin yawancin magidanta suna sayen burodi da daddare idan za su koma gida domin amfani da shi da safe.
Wannan ya sa mutane da dama suka shiga harkar burodin, ko dai a bangaren mallakar gidan burodin ko aiki a gidan burodin ko kasuwancinsa saboda yadda yake da matukar farin jini.
A titunan Kano da gidaje, akwai gidajen burodi da dama da masu kasuwancinsa da masu sayar da shayi da suke saukaka wa mutane wajen hada musu karin kumallo, su kuma suke samun kudin hidimarsu.
Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa yanzu burodi ba kamar yadda aka san shi a baya ba ne, domin gidajen burodi da dama ko dai sun daina aiki, ko sun rage yawan burodin da suke yi.
Haka shagunan sayar da burodi da wajen masu shayi da a da ake ganinsu cike da iri-irin burodi yanzu sun rame matuka.
Bello Muhammad, mai gidan burodin Glory Special Bread da ke ’Yankaba a Kano, ya ce tsadar kayayyakin sarrafa burodi ta sa wasu daga cikinsu sun fara cire rai daga harkar, domin a cewarsa kadan daga cikinsu ne za su iya ci gaba da harkar.
Ya ce abokan cinikinsu da dama sun daina ko kuma sun rage sayen burodin, wanda hakan ya tilasta musu rage aiki tare da rage ma’aikata.
Haka kuma ya ce sauran ma’aikatan da suka rage ma an rage musu albashi da kusan rabi.
“Muna cikin matsalar da ba mu taba ganin irinta ba. Mun rage aiki da kusan rabi tun lokacin annobar Kwarona.
“A da mukan murza buhun fulawa 8, amma yanzu da kyar muke yin buhu 3 da rabi “Kusan dukkan kayan da muke amfani da su farashinsu ya yi kusan ninkawa.
“Kafin annobar Coronavirus, muna sayen buhun fulawa a Naira dubu 9,300, amma yanzu ya kai Naira dubu 29.
“Man dizel da muke sayen lita Naira 200, yanzu Naira 850 ne, haka sukari da muke sayen buhu Naira dubu 13, yanzu ya koma Naira dubu 30,” inji shi.
Wani mai sayar da burodi, Bashir Abdulsalam ya ce kafin farashin kayayyakin burodi ya yi sama, yakan sayar da burodin Naira dubu 400 a kullum, amma yanzu da kyar yake iya sayar da na Naira dubu 200 a kullum.
“Shekara 20 ke nan ina kasuwancin burodi. Na samu arziki sosai a wannan harka, inda yanzu haka ina da mata biyu da ’ya’ya 11 kuma duk da wannan kasuwanci nake daukar dawainiyarsu, amma a yanzu na fara tunanin canja kasuwaci domin na fara asara,” in ji shi.
Wani mazaunin Kurna da ke Kano, Sulaiman Abubakar Sulaiman ya ce duk da cewa yana sayen burodina kullum, yanayin tsadarsa na damunsa.
“Kullum ina sayen burodi na gidana da na iyayena. A da burodin Naira 500 yana isan gidajen biyu, amma yanzu ko na 1,000 ba ya isa, kuma mai saukin ba ya da inganci kuma babu dadi,” inji shi.
Shi ma Nazifi Sani ya ce dole yanzu ya koma amfani da koko domin karin kumallo a gidansa saboda tsadar burodin. “Yanzu na daina sayen biredi saboda tsadarsa ya fi karfina,” inji shi.
A Jihar Gombe, a daidai lokacin da masu sayen burodin suke babatu, masu kasuwancinsa murna suke yi saboda karin riba.
Wani mai shago a Tudun Wada da ke cikin garin Gombe mai suna Umar Juma Abubakar ya ce, “Har yanzu mutane suna zuwa sayen burodi saboda har yanzu yana cikin abinci masu sauki duk da tsadarsa.
Kawai ruwan shayi da sukari kake bukata ka hada da shi ka ci.
“Ka san yanzu mutane sun daina sayen fulawa domin hada wasu abubuwa a gida saboda tsadarta, amma gaskiya suna sayen burodi saboda saukin da yake da shi wajen sarrafa shi ya zama abinci,” in ji shi.
Sai dai ya ce mutane da dama da suke sayen burodi biyu ko uku a da, yanzu sun koma sayen daya saboda yanayin tsadar rayuwa.
Wani mai kasuwancin burodin, Abdullahi Bappale ya ce tsadar burodin ta taimaki wasu, ta kuma karya wasu.
Bappale, wanda ya ce ya kwashe shekara 25 yana kasuwancin burodin, ya ce, “Taimakon da ya yi wa wasu shi ne ribarsu ta karu, sai dai kuma masu saye sun ragu.
“Ni dai zan iya cewa na fi cin riba yanzu da ya yi tsada, sai dai kawai abokan cinikina suna raguwa.”
Habibu Muhammad mai ’ya’ya biyar da ke zaune a yankin Tabra a cikin Gombe ya ce yanzu mara karfi da kyar yake iya ciyar da iyalansa.
“Burodin da muke saya Naira 200 yanzu ya kai Naira 400. Gaskiya muna shan wahala,” in ji shi.
Wani karamin ma’aikaci mai suna Umar Abdulhamid ya ce, “Ina da mace da ’ya’ya biyu.
“A da nakan sayi burodin Naira 400 ne kuma mukan yi mako daya da shi. Amma an rage masa girma, kuma ya kara tsada.
“Burodin da nake saya Naira 400, yanzu ya kai Naira dubu daya, kuma ba ya kai mu kwana uku.”
A Jihar Binuwai, duk da cewa farashin burodin bai hau sosai ba, kamar a sauran jihohi, mutane da dama da aka zanta da su sun ce sun koma amfani da wasu nau’o’in abinci domin karin kumallo.
A Jihar Taraba, masu gidajen burodi da masu sayar da shayi sun ce suna taba ciniki duk da tsadar burodin.
Wani mai gidan burodi mai suna Musa Mai Burodi ya bayyana wa Aminiya a shekarun baya yana murza buhu 10 na fulawa, amma duk da tsadar kayan sarrafa burodin, kasuwancin kara habaka ya yi, inda yanzu yake murza buhu 25 saboda karuwar bukatarsa.
Sai dai ya ce yana kai burodinsa kauyuka ne, inda a cewarsa an fi bukatarsa, sannan ya ce burodin da yake sayarwa Naira 200, yanzu ya kai Naira 500 saboda tsadar kayayyakin sarrafawa.
Shi ma wani mai gidan burodi da ke Jalingo, Haruna Sama’ila ya ce ba sa samun riba sosai yanzu saboda kudaden da suke kashewa wajen aiki, amma dole suka ci gaba da harkar saboda har yanzu akwai masu saya.
Ya kara da cewa masu sayar da shayi ma na kawo musu matsala domin yawancinsu bashi suke karbar burodin, sannan su ki kawo kudin.
Wani mai sayar da shayi, Haruna Lawal ya ce duk da tsadar burodin, yana ci gaba da kasuwancinsa ne saboda mutane da dama sun gwammace shan shayi da burodi a kullum a matsayin abinci.
Masu rahoto: Isiyaku Mohammed; Fidelis MacLeva Abdullateef Aliyu( Lagos); Magaji Isa Hunkuyi, (Jalingo); Zahraddeen Yakubu Shuaibu(Kano); Haruna Gimba Yaya (Gombe) & Hope Abah Emmanuel (Makurdi)