A ranakun Talata zuwa Juma’a na makon jiya ne aka gudanar da babban taron kungiyar Bunkasa Adabin Gargajiya Ta Najeriya, a zauren taro na Musa Abdullahi da ke harabar Jami’ar Bayero, Kano.
Taron, wanda ake gudanar da shi kowace shekara, shi ne na goma sha daya a bana kuma an yi masa take ne da: ‘Bunkasar Tatsuniya: Jiya Da Yau Da Kuma Gobe.’ Haka kuma, an sadaukar da taron na bana ne ga shugaban kwamitin farfado da kungiyar, Dokta Bukar Usman, wanda kwararren marubuci ne a fagen Adabin Gargajiya.
Da yake jawabin maraba ga mahalarta taron, Shugaban Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ya bayyana cewa Adabin Gargajiya zai iya bunkasa tattalin arzikin Najeriya, domin kuwa wata hanya ce ta samar da kudaden shiga.
“Adabin Gargajiya yana bukatar mu ba shi muhimmanci fiye da wanda muke ba shi a yanzu.” Inji shugaban, wanda ya bayyana rashin gamsuwarsa game da abin da ya kira rikon sakainar kashin da jama’a suke yi wa sha’anin adabi da al’adu. Haka nan ya ja hankalin mahalarta taron a game da barazanar da ya ce bakin a’adu na zamani suke yi ga al’adunmu na gargajiya.
Daga nan sai ya kalubalanci iyaye da gwamnatoci da shugabannin gargajiya da sauran masu fada a ji da su hada karfi da karfe wajen farfado da al’adu da adabi ta hanyar cusa wa kananan yara da matasa kyawawan al’adunmu na gargajiya. Ya ce adabi ne yake bayyana mu a matsayin ’yan Najeriya ko ’yan Afirka.
Shugaban Jami’ar ya bayyana shirin jami’arsa na ci gaba da bunkasa adabin na gargajiya, inda ya ce tuni jami’ar ta kirkiro da kwas, domin nazarin Adabin Gargajiya kuma har ma jami’ar ta gina masa mazauni na dindindin a cikin jami’ar. Kamar yadda ya ce, kwas din zai zauna ne a karkashin Sashin Nazarin Yarukan Najeriya. (Centre for Research in Nigerian Languages and Folklore).
Haka shi ma a jawabinsa a wajen taron, Farfesa dandatti Abdulkadir ya bayyana cewa adabi yana da fadin gaske har fiye da yadda mutane suka dauke shi, domin ya fi karfin tatsuniya, ya hada da labarai da sauran abubuwa da dama na gargajiya.
A nasa jawabin, tsohon Babban Sakatare a Gwamnatin Tarayya, Dokta Bukar Usman, wanda kuma aka shirya taron don martaba shi, ya bayyana farin cikinsa da gamsuwarsa da karrama shi da aka yi wajen shirya taron da sunansa, inda ya sha alwashin ci gaba da bayar da gudummawarsa wajen yin rubuce-rubuce don bunkasa adabi.
Shi kuwa babban malami a Jami’ar Jihar Delta, Farfesa G. G. Darah, a matsayinsa na Babban Bako Mai Jawabi, ya gabatar da takardarsa, wacce ta yi bayani mai gamsarwa kuma mai tsawo game da rikidewar tatsuniya zuwa kirkirarren labari. Duk da cewa bai samu zuwa da kansa ba amma dai ya turo wakili, wanda ya karanta takardar tasa tun daga farko har zuwa karshe.
Babban malamin, wanda a baya ya taba rike mukamin shugabancin kungiyar, ya nuna irin muhimmancin da ke tattare da Adabin Gargajiya, kamar yadda ya ce tubali ne na gina al’umma, wanda ta hanyarsa ake samun ilimi, tarbiyya da kuma bunkasuwar tattalin arziki.
A nata jawabin godiya, Farfesa Asabe Kabir ta Jami’ar Usman danfodiyo Sakkwato, a matsayinta na daya daga cikin membobin kwamitin farfado da kungiyar ta Bunkasa Adabin Gargajiya, ta yi godiya ta musamman ga Dokta Bukar Usman da shugabannin Jami’ar Bayero da Farfesa dandatti Abdulkadir da kuma daukacin mahalarta taron.
A tsawon taron na kwanaki uku, an gabatar da takardun nazari sama da guda sittin. Fitattu daga cikin wadanda suka gabatar da takardun sun hada da Farfesa Nkem Oko, na Jami’ar Fatakwal da Farfesa Zikky Kofoworola da Farfesa Segun Adekoya na Jami’ar Obafemi Awolowo, Ife da Farfesa Sa’idu Ahmad babura na Jami’ar Bayero Kano da Farfesa Angela Miri.
Sauran wadanda suka gabatar da takardun sun hada da Farfesa Salisu Ahmad Yakasai na Jami’ar Usman danfodiyo Sakkwato da Malam Khalid Imam na Kwalejin Kimiyya Ta Mata da ke Garko da sauransu da dama, ciki har da Baturen kasar Poland, Dokta Mariusz Krasniewski.
Taron dai bai kammala ba sai da aka gabatar da Kundin Tsarin Mulkin kungiyar, wanda Kwamitin Farfadowa ya samar kuma aka buga shi a takaitaccen littafi mai dauke da shafi 16. Dukkan mahalarta taron, wadanda suka kasance membobin kungiyar sun nuna gamsuwa da amincewa da kundin, wanda aka bayyana cewa shi ne zai zama jagoran tafiyar da harkokin kungiyar.
Haka kuma an gudanar da kwarya-kwaryan zaben shugabannin da za su tafiyar da kungiyar na tsawon shekaru biyu masu zuwa. Wadanda aka zaba a mukamai daban-daban sun hada da Dokta Bukar Usman, a matsayin Shugaba, sai Farfesa Olusegun Adekoya na Jamiu’ar Obafemi Awolowo, Ife a matsayin Mataimakin Shugaba na daya, sai kuma Farfesa (Uwargida) Asabe Kabir Usman, ta Jami’ar Usman danfodiyo Sakkwato a matsayin Mataimakiyar Shugaba ta Biyu.
Sauran zababbun sun hada da Farfesa Sani Abba Aliyu na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, a matsayin Babban-Sakatare. Wanda aka zaba a matsayin Ma’ajin kungiyar shi ne Farfesa Abdu Yahaya Bichi, na Jami’ar Bayero, Kano. Sakataren Kudi: Dokta Aloy N. Obika na Jami’ar Madonna, Okija. Jami’in Hulda Da Jama’a: Dokta A. B. Kofa, na Jami’ar Jihar Kaduna. Editan Al’amuran kungiya kuwa ya kasance Farfesa Mkem Okoh na Jami’ar Fatakwal. Mataimakin Edita: Farfesa Maikudi karaye na Jami’ar Bayero, Kano. Mataimakin Sakatare kuwa ya kasance Dokta Bosede Afolayan, na Jami’ar Legas. Wanda aka zaba a mukamin Manajan Kasuwanci kuwa shi ne Dokta Daniel Omatsola na Jami’ar Abuja. Mai Binciken Kudi kuwa shi ne Farfesa Ademola Dasylba na Jami’ar Ibadan.
Haka kuma an kafa kwamitin amintattu na kungiyar a karkashin Shugabancin Farfesa G. G. Darah. Sauran membobin kwamitin sun hada da Farfesa dandatti Abdulkadir da Farfesa Bade Ajuwon, na Jami’ar Obafemi, Ife da Mista Ben Tomoloju da Farfesa Zikky Koforowola, na Jami’ar Ilorin da Farfesa Angela Miri, ta Jami’ar Jos da kuma Farfesa Afam Ebeogu, na Jami’ar Jihar Abiya.
A matsayinsa na sabon zababben Shugaba, Dokta Bukar Usman ya nemi zababbun shugabannin kungiyar da sauran membobi da su hada hannu domin yin aiki wurjanjan da nufin daga martabar kungiyar. Ya ce a iya lokacin da za su gudanar da al’amuran kungiyar, za su gudanar da tsare-tsare masu muhimanci, wadanda za su taimaka wajen bunkasa Adabin Gargajiya. Ya yi alkawarin cewa kungiyar za ta yi kokarin fara buga ingantattar mujallar nazari, wadda za ta kunshi takardun bincike da nazari daga masana, kamar kuma yadda ya ce za a kafa jaridar da za ta rika bayyana labarun aikace-aikace da al’amuran kungiyar.
An dai kammala taron lafiya, da nufin sake hallara a shekara mai zuwa, idan Allah Ya kai mu.
Yadda taron kungiyar Bunkasa Adabin Gargajiya na bana ya gudana
A ranakun Talata zuwa Juma’a na makon jiya ne aka gudanar da babban taron kungiyar Bunkasa Adabin Gargajiya Ta Najeriya, a zauren taro na Musa…