✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda tankar mai ta kife ta kama da wuta

Wata tankar mai dauke da lita 40,000 na man dizal (AGO) a safiyar Alhamis ta fashe a kan babbar hanyar Oshodi-Apapa da ke Jihar Legas.…

Wata tankar mai dauke da lita 40,000 na man dizal (AGO) a safiyar Alhamis ta fashe a kan babbar hanyar Oshodi-Apapa da ke Jihar Legas.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:15 na safe kamar yadda Babban Jami’in Hukumar Agaji ta Kasa (NEMA) a Jihar Legas, Ibrahim Farinloye ya bayyana.

An gano cewa tankar man ta tuntsure ne a daura da ofishin Hukumar Kashe Gobara inda kan motar ya rabu da jikinta.

Ibrahim Farinloye ya tabbatar da cewa jami’an kwana-kwana sun yi kokari wurin kashe wutar. Babu tabbacin asarar rayuka, inji shi.

‘Yan kallo a lokacin da matar ta fadi sannan ta kama da wuta
Yadda wuta ke ci a kan titi tare a bakin hayaki bayan motar ta kama da wuta
Daga nesa, bakin hayaki ya turke sama a inda wutar ta shi a ka hanya.
Wani jami’in kwana-kwana yana fesa ruwa domin kashe wutar
Jama’ar gari sun yi dafifi suna kallon yadda ake kokarin kashe gobarar
Jami’an kwana-kwana na ta kai-komo a lokacin aikin kashe gobarar