Gidauniyar Ilimi ta Hukumar bunkasa yankin Arewa maso Gabashin Najeriya (NEDC-EEF) ta yi alkawarin yakar jahilci da fatara a yankin.
Kwamitin Amintattun gidauniyar ya ce zai samar da sana’o’i da kwarewa a yankin ta yadda jam’a za su samu ci gaban rayuwa da karfin tattalin arziki.
“Za mu ba wa iyalai ilimi daga matakin gunduma zuwa mazabar dan Majalisar Dattawa a kowace jiha sunnan mutum 2,400 da ke ci gajiyar shirin samun ilimi a cikin amicin (SSI) za su karo ilimi a manyan makarantu.
— Daukar nauyin ilimin marayu
“Marayu da ’ya’yan talakawa da ba sa cikin SSI za su samu damar shiga ciki”, inji Shugaban Kwamitin Amintattun gidauniyar, David Kente.
Ya ce NEDC-EEF za ta dauki nauyin yara masu hazawa a fannin wasanni kuma za ta kafa makarantar kwarewa a kan wasanni na yankin.
Ya yi alkawarin ne bayan shgugaban Hukumar Bunkasa yankin (NEDC), Janar Paul Tarfa ya kaddamar da shi da sauran ‘yan kwamitin.
— Kwasakwasai kan sana’o’i
Kente ya ce hukumar za ba da “gajerun horo masu zurfi kan sana’o’i ga daliban da rikicin Boko Haram da wasu matsaloli suka hana yin karatu.
“Hakan zai yi tasiri sosai wajen yakar talauci da jahilci da suka fi tsanani a Arewa maso Gabas fiye da sauran yankunan Najeriya”, inji shi.
— Tsananin talauci a Arewa maso Gabas
Ya ce rahoton Hukumar Kyautata Rayuwar Dan Adam ta Duniya (UNDP) na 2018 ya nuna karfin ci gaban rayuwa a yankin ya gaza abun da ake bukata.
“Idan aka hada alkaluma mafiya yawa na 0.4286 a Taraba da mafi karanci na 0.3238 a Bauchi ba su kai rabin na Legas mai 0.6515 wanda shi ne mafi yawa a fadin kasar.
Kente ya yi alkawarin aiki tare da tsare-tsaren ilimin yankin a dukkan matakai da kungiyoyin agaje domin cimma manufar ilmantar da jama’ar yankin.
“Mun yi amannar cewa hakan zai sauya yanayin da ilimi ke ciki a yankin”, kamar yadda ya bayyana.