✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda taba sigari ta jawo gobarar da ta kone shaguna 200

Shugaban kungiyar Masu Sarrafa Katako reshen Jihar Legas, ya ce karar taba sigari ce jawo gobarar da ta tashi a kasuwar Unguwar Ebute Meta da…

Shugaban kungiyar Masu Sarrafa Katako reshen Jihar Legas, ya ce karar taba sigari ce jawo gobarar da ta tashi a kasuwar Unguwar Ebute Meta da ke jihar, a farkon makon nan.

Alhaji Abdulganiyu Onikeku ya shaida wa manema labarai cewa da wani da ba a gano shi ba ne ya jefar da tabar a kasuwar, sakamakon hakan ya haddasa gobarar da ta tashi da tsakar daren ranar Talata tare da janyo asara dukiya mai yawa.
“An gaya mini cewa wani mutum da ba mu gano ko wane ne ba tukuna, shi ya sha taba kuma ya jefar da sauran tabar a kasuwar shi ne abin da ya janyo gobarar da ta tashi. Da ma mun sanya doka kan haka, kuma muna gargadin mambobinmu dangane da tayar da wuta a kasuwar. A yanzu zancen da nake yi da ku shaguna kimanin 200 sun kone tare da yin asarar miliyoyin naira. Har yanzu muna ta kiddiddige asarar da aka yi. Kuma muna ci gaba da bincike don gano wanda ya ya yi sanadin tayar da gobarar tare da daukar matakin ladaftarwa a kansa,” inji shi.
Ya kara da cewa daruruwan mutane da ke yin sana’a a kasuwar sun rasa ayyukan yi sakamakon gobarar.
Shugaban ya nuna takaicinsa dangane da kokarin da suka rika yi don gwamnati ta taimaka musu, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
“Mun sha neman taimakon a wurin gwamnati na gobarar da kasuwannimu suka rika yi a baya amma ba mu samu taimako ba. Wasu daga cikin mutanenmu bashin banki suka karbo wasu kuwa daga wurin danginsu suka karbo bashi don su ci gaba da yin kasuwancinsu amma duk sun yi asarar komai nasu. Ka ga idan ba a taimaka musu ba sai su shiga wani hali,”inji shi.
Daraktan ’Yan Kwana-Kwana na Jihar Legas, Mista Rasak Fadife, ya ce tuni suka tura tankokin ruwa daga tashoshinsu da ke unguwar Iganmu da Onikan don su kai dauki wurin, inda aka kashe wutar da misalin karfe takwas na safiyar shekaranjiya Laraba.
Ya bayyana cewa gobarar ta kone shagunan da ake sayar da falankin katako da kayan gine-gine a kasuwar.
Ya kara da cewa dalilin da ya sa gobarar ta yi kamari shi ne mafiyawancin shagunan an gina su ne da katako da kuma tsafaffin karafina.
Wannan shi ne karo na hudu da gobara ta tashi a kasuwar katako ta Ebute Meta don a cikin watan Agusta a shekarar da ta gabata da cikin watan Janairu da watan Maris na bana shaguna masu yawa sun kone a kasuwar sannan wata mata ta rasa yara uku a gidajen da ke kusa da kasuwar.