Fitaccen matashin nan a kafofin sadarwa, Umar Umar Alhassan, wanda aka fi sani da King Indara ko Sarki Mai Daraja, ya jawo ce-ceku-ce bayan ya bayyana kafar TikTok a matsayin wajen wasan yara da rashin tarbiyya.
King Indara ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da Aminiya ta gani lokacin da yake tattaunawa da wani gidan rediyo a Kano, inda a ciki ya ce duk wanda ya isa Facebook da Tiwita yake zuwa.
- Messi ya kulla yarjejeniyar shekara 2 da Inter Miami
- Kofin Duniya 2026: Yadda kasashen Afirka za su fafata wajen neman tikiti
A cewarsa, “Ni ban dauki mai yin TikTok a matsayin fitacce ba. Na dauki TikTok wajen wasan yara ne.
“Duk wanda yake TikTok ban dauke shi fitacce ba, kawai na dauke shi mutum wanda yake zuwa yana wasan yarinta, kuma wuri ne na rashin kamun kai.
“Don haka idan so ka nuna kai fitacce ne, ka lallabo Facebook ka nuna iyawarka, sannan ka je Twitter.”
Da aka shaida masa cewa akwai wadanda suka yi fice, har ana kallon bidiyonsu sau miliyoyi, sai ya ce, “Ai mashiririta ne,” inda ya kara da cewa malamai ne kawai suke wallafa bidiyoyi masu amfani.”
Matashin, wanda shi ne Shugaban Gudauniyar Matasa Foundation ya kuma rubuta a shafinsa na Instagram cewa, “Ita kanta TikTok din na riga ta suna a duniya ballanta ’yan cikin TikTok din.”
Wannan lamari ya haifar da ce-ce-ku-ku-ce, inda aka rika samun mabambanta ra’ayoyi, wasu na yabonsa, wasu na sukarsa.
A dai kafar TikTok akwai matasa wadanda a can ne suka yi fice, har aka san su, irin su Murja Ibrahim da sauransu.
Wani mai suna Muhammad Sani, mai suna mansanii_ cewa ya yi, “In dai za ka ci gaba da magana ta kaifin basira haka, to tabbas zan rika dangwala maka likes.”
Ita kuma fitacciyar mai koyar da hanyoyin samun kudi da kasuwanci ta Intanet, Maryam Bichi cewa ta yi, “Muna TikTok, muna abin alheri a Tiktok, kai TikTok ni abin da ya sa ni na yi fice a TikTok, na kalubalanci masu shashanci ne, inda na samu goyo baya daidai gwargwardo, kada ka yi jam’u, kowace kafa akwai shashashu amma kowacce akwai masu hankali.”
A wani martani da Murja Ibrahim Kunya ta yi, ta bayyana King Indara da kawarta, inda a ciki ta rika nuna King Indara da Queen Indara.
A cewar Murja, “Kawata ashe rai kan ga rai? Ni dai rabona da ke tunda muka rabu a Instagram lokacin muna ta fadi-tashi muna neman suna.
“Kin tuna lokacin na ce miki ni fim zan shiga. Na samu na lallaba TikTok din nan na samu na yi fice, ashe har yanzu kuna nan kuna ta Instagram din.
“Yanzu wa yake daura miki dan kwali? Shegiya King Indara. Kin san ni tsakanina da ke wasa ne, in ce miki Queen Indara. Allah sarki kawa. Queen Indara tsakanina da ke babu cin mutunci.
“Kin gan mu a TikTok din ne muka rage ta, mu ne hauka, mu ne zagezage saboda neman suna muke yi.”
A karshe Murja ta ce da Indara ya san neman suna yake da ya kira ta ce, “Kawa Indara da sai ki kira ni ki ce kawata Murja don Allah kin ga sunana ya kwanta, kuma na san ki tun da can, yanzu ina son sunana ya dawo a soshiyal midiya, kin san zan miki kawata. Amma da kika tashi ke babu natsuwa kawai kika fito kika saki baki a cikin ’ya’ya maza.”
A karshe dai Murja ta ce kawai a bar maganar, kawai Indara ya kira ta, ta san yadda za a yi ta dawo da maganarsa, sannan ta rika yin wasu abubuwa irin na ’yan daudu, tana cewa ai dole ta ci wa mutanen TikTok mutunci ne za a san da ita.
Shi ma Mai Wushirya, wanda na hannun damar Murja ne ya magantu, inda ya ce ya ji Indara yana cewa su yaran ne, inda shi ya bayyana cewa, “Wallahi so yake ya haukatar da ku. Bayan wancan bidiyon ya sake yin wani hirar ya ma ce ku yaransa ne da jikokinsa.
Kai Indara da na zo a danka da na jawo maka hukuncin rataya. Kai ni iya tashin hankalina a zuba a faranti aka ce maka ka fito a sa cokali, kai ko hannu za ka iya sakawa?”