Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta amsa cewa jirgin yakinta ne ya kai hari kan fararen hula a kauyen Buhari da ke Karamar Hukumar Yunusari na Jihar Yobe bisa kuskure.
Rundunar ta kuma ce tuni ta kafa kwamitin bincike domin lalubo makasudin harin da ya yi sanadiyyar kashe mazauna kauyen kimanin su tara.
- Mayakan Ansaru sun kafa tuta a kauyukan Kaduna guda 2
- Yadda ake hada baki da ’yan uwa a sace mutane a Zariya
Aminiya ta rawaito yadda aka zargi jirgin yakin rundunar da kai harin tare da kashe mutum takwas, amma kakakinta, Air Commodore Edward Gabkwet, ya musanta tun da farko.
Sai dai a wani mataki mai kama da yin mi’ara koma baya, Edward, a cikin wata sanarwa ranar Alhamis ya amince cewa jirgin yakinsu ne ya yi harbi a kauyen.
Ya ce a lokacin, ’yan ta’addan Boko Haram da na ISWAP suke kokarin kai wa harin, inda ya ce ya karyata labarin tun da farko ne saboda jiragen ba sa dauke da bama-bamai.
Ya ce, “Bayan samun rahotannin sirri kan karakainar ’yan Boko Haram da ISWAP a kan hanyar Kogin Kamadougou bangaren Jihar Yobe, jirgin yaki na sashen rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai ya kai hari kan wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne a kan iyakar Najeriya da Nijar da wajen misalin karfe 6:00 na safiyar ranar 15 ga watan Satumba.
“Jirgin yayin da yake shawagi ya ga wani motsi da bai yarda da irinsa ba, wanda kwatankwacin na ’yan Boko Haram ko ISWAP ne, musamman a lokacin da suka ga jirgin soji.
“Hakan ya sa direban jirgin ya yi harbi a yankin. Amma ya kamata a fahimci cewa yankin fa dama ya yi kaurin suna wajen ayyukan ’yan ta’adda. Sai dai muna takicin samun labari daga bisani cewa an kashe wasu fararen hula a bisa kukure,” inji kakakin.
Ya ce sanarwar da rundunar ta fitar tun da farko wacce ta karyata labarin ta yi la’akari ne da bayanan da aka bata, inda ya ce tuni ta kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin harin.
A wani labarin kuma, Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe, Dokta Muhammad Goje ya tabbatar da cewa yawan mutanen da suka rasu a harin ya zuwa yanzu ya kai tara, yayin da wadanda suka jikkata suka kai 23.