Dakarun sojin Najeriya da sun ragargaza mayakan Boko Harma da suka kai hari a garin Marte, Jihar Borno.
Maharan da suka kwashi kashinsu hannun sojojin da suka yi musu kofar rago, sun kai harin ne kimanin wata guda bayan komawar mutanen garin gidajensu daga gudun hijirar da suka yi na shekara shida a Jamhuriyar.
- Tsoron iyayenmu na hana maza neman aurenmu —’Yan matan barikin soja
- An kama kwarto ya haka ramin da ke kai shi gidan auren tsohuwar budurwarsa
- Mutane sun tsere yayin da sojoji da Boko Haram ke gwabza fada a Borno
Mukaddashih Daraktan Yada Labaran Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Birgediya Bernard Onyeuko, ya ce dakarun rundunar Operation Tura Takaibango da jiragen yakin Rundunar Operation Lafiya Dole “sun tarwatsa motocin yaki bakwai na Boko Haram a lokacin da suke yunkurin kai wa sansanin sojin hari a Marte.
“Bayan samun rahoton harin, sai sojojin suka janye, suka yi wa mayakan kwanto a wani wuri, inda suka jira maharan suka kuma bude musu wutar da ta kai ga nasarar, ” inji sanarwar ta ranar Asabar.
Ga wasu daga cikin hotunan yadda sojojin suka yi fata-fata da mayakan Boko Haram din.