✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Sojoji suka nemi kashe ni yayin juyin mulkin Dimka – Abdulkarim Albashir

Alhaji Albdulkarim Albashir daya ne daga cikin fitattun ’yan jarida da kasar nan ta samu da ya yi aiki a kafofin watsa labarai da dama…

Alhaji Albdulkarim Albashir daya ne daga cikin fitattun ’yan jarida da kasar nan ta samu da ya yi aiki a kafofin watsa labarai da dama ciki har da Rediyon Tarayya na Kaduna. Fitaccen dan jaridan dan garin Bazza da ke Jihar Adamawa, mai shekara 70, kwararre ne wajen rubuta sharhin bayan labarai, kuma ya taba zama Editan jaridar The Democrat. Ya bayyana gwagwarmayar da ya sha a aikin jarida ciki har da yunkurin kashe shi shi da sojoji suka yi lokacin yunkurin juyin mulkin su Dimka:

Yaya aka yi ka zama dan jarida?
Bayan na kammala makarantar horon malamai a 1966 sai na shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a 1969 na kammala a 1973. Na karanta Tarihi da Kimiyyar Siyasa da Aikin Jarida. Amma tun ina makarantar firamare nake sha’awar aikin jarida don yayana Ambasada Mahmud Bashir, Allah Ya jikansa, yana da karamin rediyo, inda nake kunnawa don jin labarai, sannan in mahaifinmu ya dawo gida muke yi hira. A 1973, bayan na kammala karatu sai na nemi aiki a kamfanin buga jaridun New Nigerian (NNN) da kuma gidan rediyon jihar arewa, (BCNN), wanda ya koma FRCN. Bayan kwana uku muna ta yin jarrabawar daukar aiki, sai aka dauke ni a matsayin mai dauko rohoto mataki na 2. Na yi matukar jin dadin aiki da rediyo domin na samu kwarin gwwiwa da kyautatawa ga aiki. Don ana sayar mana da kayan abinci lokaci-lokaci sannan mu biya a hankali. Mun yi aiki da Tajudeen Akanbi da Azeez Alodunmoye da Sani Sambo da dahiru Modibbo, wanda muke kira (Boss), wanda yake darajta ni. Don yana daukar shawarata. Yakan dauki shawarata bayan sun fito mitin na manya lokacin ina matakin albashi na 8. Wasu lokuta yakan aiko da mota da yamma a dauke ni zuwa gidansa don mu tattauna na awa biyu ko uku a dandamalin gidansa.
Yaya aka yi ka zama mai rubuta sharhin labarai?
Wata rana da safe dahiru Modibbo ya shigo ofishina ya ce “Na lura kana da son rubutu, don haka ka rubuta sharhi na minti biyar, amma zai iya daukarka lokaci mai tsawo kafin ka rubuta don za ka yi bincike.” Yadda aka yi na fara ke nan.
Don me ka bar FRCN ka koma jaridar Democrat?
Aiki hudu aka nemi da su a lokaci guda, FRCN, bON, Rediyon Adamawa da kuma Democrat. FRCN na so in ci gaba da aiki a Kaduna, sannan gidan rediyon Muryan Najeriya (bON) na so na da aiki a Legas, duk a matsayin Babban Darakta. Sannan gidan Rediyon Jihar Adamawa, jihata ke nan, na so na da aiki a Yola a mukamin Janar Manaja. Sannan jaridar Democrat na nema na a matsayin Edita.
 Janar Ibrahim Babangida ya zo FRCN Legas ya same ni ya ce Gurup Kyaftin Jonah Jang na nemana a Yola. IBB ya yi dariya ya ce masu zawarcina sun yi yawa, suna neman su yaga ni. Ya ce wanne nake so. Na ce na zabi zuwa gida don aiki a Yola, sai IBB ya ce sumul kalau ina iya tafiya.
 Don me aka hade BCCN da FRCN sannan aka rage masa karfi?
 Ministan Watsa Labarai ya zo BCNN sannan ya wuce gaisuwar ban girma ga Gwamnan Kaduna Guruf Kyaftin Usman Jibrin. Ina wurin yayin da Ministan ya ce karfin BCNN ya yi yawa, don haka za su rage shi daga mai dogon-zango zuwa mai gajeren-zango. Sai Usman Jibrin ya ce sai dai ya cire kakin soja ya bar aiki don bai yarda ba domin kamfani ne na gwamnatin Jihar Arewa ba na tarayya ba. Daga karshe dai aka yi rigima tsakanin Obasanjo da Usman Jibrin. Da ya bar aiki sai aka rage karfin gidan rediyon inda a da ana jin sa a duk yammacin Afirka ta Yamma. Aka kwashe tiransmita wato na’urar yada labarai uku aka koma amfani da wadanda ba za su wuce Arewacin Najeriya ba.
Kashi na biyu na rage karfin gidan rediyon shi ne lokacin mulkin IBB inda Ministan Labarai Farfesa Jerry Gana ya so a rage karfin gidan rediyon don kada a ji shi a Arewacin kasar nan sai dai a Jihar Kaduna kadai. Don na ji cewa gwamnati ba ta son yadda ake jin rediyon a nesa. Gidan rediyon na tarayya na Kaduna shi ne kadai wanda aka yi wa wannan karan-tsaye don ba a yi wannan a Inugu da na Ibadan ba. Domin Obasanjo ya biya su kudinsu diyya na rage musu karfi da aka yi. Kuma ba a kwace musu na’urorin yada labarunsu ba. Bayan haka, lokacin da Obasanjo ya bar mulki ya zo taro nan Kadnua inda ya ce an rage karfin FRCN ne don yana yada labaran karya. Nan take ni tare da wasu muka ce ya fadi labari guda daya na karya da aka taba yadawa. Amma ya kasa. Na san lokacin da FRCN ta ceci rayukan ’yan kasa daga fadawa cikin mummnan rikici, Don lokacin ina kamfanin Democrat sai Muhammed Suleiman ya kira ni don an aiko da wani labari daga Legas, cewa an kashe ’yan Arewa da yawa a Legas, inda har wasu da yawa suka fada teku. Sannan wasu ’yan Arewa sun fara gudun hijira tare da iyalansu dage Ikko zuwa Arewa. Labari ne daga wakilinmu daga Ikko, don a gabansa aka yi aika-aikar. Sai na yanke shawara na ce in an dauki wannan labarin, ba mu san inda ’yan Kudu da ke Arewa za su zamo ba, don ana iya daukar fansa. Aka a je labarin ba a karanta ba. Amma da gaske abin ya faru a 1995. Don ya fi sauki a boye labarai a ceci jama’a a zauna lafiya, maimakon a fadi gaskiya a rasa rayuka.
 Me ne mummunan abin da ya faru da kai a wannan aikin?
Na shiga gidan rediyo sai wani ya ce min an yi juyin mulki. Wato juyin mulkin su Kanar Dimka. Na shirya labarai, na kuma shaida wa Babban Darakata Abba Zoru cewa ya duba kafin a yada. Sai ya ce ina ruwansa da duba labarai. Ya ce ‘in na kasa aiki za a rage min matsayi. Sannan dai ya karanta kuma ya ce in ba mai karantawa a na kasa da ni, to ni in karanta.’ Sai kwatsam wasu sojoji uku suka shigo suka nuna min bindiga suka ja ni a kasa. Gida ya hargitse. Sai Abba Zoru ya shigo ya ce wa ya ba sojojin damar kama masa ma’aikaci ba tare da saninsa ba, sannan su fadi laifin da ya yi. Suka ce an ba su umarni ne. Shi ma ya yi musu tsawa cewa shi ma an ba shi umarni ne ya yi aiki. Sai ya ce kada a bari su tafi da ni. Sai ya yi wa Kwamandan Runduna ta daya da ke Kaduna Janar IBM Haruna waya cewa don me ya tura sojoji su kama masa ma’aikaci. Sai ya turo wasu sojojin suka kama wadannan ’yan tawaye da Kanar Dimka ya tura suka ja ni a kasa su uku. Rigimana da sojoji ya sa aka hana soja shiga gidan rediyo da damara. Na taba jin an samu hargitsi yayin da wasu sojojoi suka shiga gidan rediyon da damararsu. Akwai kuma lokacin da Birgediya Abba Kyari ya yi ziyarar ba-zata da safe a gidan rediyon inda ya ce don me bai ga ma’aikata ba. Sai na gaya masa cewa aikin jarida, aiki ne na karban-ni-in-karbe-ka, wato akwai ma’aikatan safe da na rana da na yamma. Don ba aiki suke irin na sauran ma’aikatan ba daga safe zuwa yamma. Sai ya ba da hakuri ya yi gaba.
Ko yaranka sun gaje ka?
Eh, ’yata Sa’adatu Albashir yanzu tana aiki da FRCN.
 Yaya aka yi ka juye daga gidan rediyo zuwa na jarida?
Wani mutum ya same ni a Yola ya ba ni hakuri. Don ya ce ya zuga Gwamna Madaki cewa ban san aikin jarida ba sai na rediyo. Amma Gwamna Madaki ya ba ni aikin jaridar Weekly Newscope don lokacin da na koma Yola wato tsohowar Jihar Gonogola ina Janar Manaja ne na Rediyo kuma ina gudanar da jaridar Weekly Newscope inda na daga yawan cinikin da muke yi daga 7,000 zuwa 100,000.
Wane ciwo ke damunka har aka yanke kafarka ta dama?
Ciwon daji ne, amma ba ciwon suga ba. Yanzu ina tafiya ne da sandar guragu.