Sojojin Najeriya sun aika kwamandojin ISWAP 50 lahira a wani harin ramuwar gayya da suka kai wa kungiyar.
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce sojojin Bataliya ta 115 ta Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya sun yi wa mayakan kungiyar asubanci da luguden wuta ne a yankin kauyen Leho da kewaye a jihar Borno.
- Gumi ya bude wa makiyaya makaranta a Kaduna
- Najeriya A Yau: A karon farko ta’addanci ya ci Janar din soja a Najeriya
Kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya ce, “Sojojin Operation HADIN KAI (OPHK) sun kashe kwamandojin ISWAP akalla 50 tare da lalata makamansu a harin ramuwar gayya da suka kai wa kungiyar a Karamar Hukumar Askira Uba ta Jihar Borno.
“A harin ne sojoji suka tarwatsa motocin kungiyar masu sulke da wasu motoci 11 da aka girke manyan bindigogi a ciki gami da wasu manyan bindigogi,” masu matukar hari.
Harin da sojojin suka ka kashe kwamandojoin kungiyar ramuwar gayya ce kan kisan Kwamandan Runduna ta 28, Birgediya-Janar Dzarma Zirkusu da wasu sojoji uku da ke karkashinsa da kungiyar ta yi a Askira Uba.
A ranar Asabar ne mayakan ISWAP suka yi wa sansanin Runduna ta 28 ta Sojin Kasa hari a Askira/Uba, inda a musayar wuta Janar Dzarma Zirkusu da sojojin suka kwanta dama.
Bayan sojoji sun daklile harin ne suka mayar da martani ta hanyar bin mayakan kungiyar har maboyarsu inda suka rika yi musu luguden wutar da suka hallaka kwamandojin kungiyar akalla 50.
Mayakan kungiyar ta ISWAP sun kwashi kashinsu a hannu ne bayan sojojin runduna ta 115 sun yi musu asubanci da luguden wutar.
Nwachukwu ya ce an kuma tsinci gawar wasu mayakan kungiyar uku a hanyarsu ta tserewa, harsasai 2,589 da suke zubar.