✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sinadarin girki na ONGA ya ciri tuta a bikin aure

Mohammad B. Umar Hankaka, Jami’in shirya bukukuwa na kamfanin Promasidor, masu yin sinadarin girki na ONGA da madarar Cowbell,  ya ce kamfaninsa ya saba tallafa…

Mohammad B. Umar Hankaka, Jami’in shirya bukukuwa na kamfanin Promasidor, masu yin sinadarin girki na ONGA da madarar Cowbell,  ya ce kamfaninsa ya saba tallafa wa amare a wajen bikin aure, tun daga bin da ya shafi kamu zuwa ranar daurin aure.
Ya ce ONGA ya ciri tuta wajen tallafa wa bukukuwa aure a Arewa, yayin da yake taimaka wa taron mata na watan Agusta (August Gathering) a yankin Kudu-maso-Gabas.
Aminiya ta tattauna da jami’an sashen kasuwanci na ONGA da suka halarci daurin auren Ahmad Yakubu da amaryarsa Zainab Yakubu da aka gudanar a masallacin Jami’ar Bayero ta Kano ranar Asabar da ta gabata.
Jami’ai da manyan manajojin kamfanin Promasidor, wadanda aka dora wa alhakin tallata haja da kasuwancin ONGA, sun bayyana wa Aminiya cewa, duk bikin da suka amince za su halarta suna bayar da gudunmuwar da ba ta gaza kwali 10 zuwa 15 na ONGA da Naira dubu 20 da buhun shinkafa, har ma da kaji 30 zuwa 40 ba.
Ango Malam Ahmad, wanda ma’aikaci ne a Kamfanin Media Trust masu buga jaridar Daily Trust da Aminiya, ya tabbatar da cewa an bai wa amaryarsa gudunmawa ta kayan abinci da kwalayen ONGA.
“Amaryata ta karbi kwalayen ONGA da kayan abinci. Sannan na ga wakilan ONGA sun halarci bikinmu. Mun ji dadi, mun gode kwarai,” inji shi.
Shi kuwa manajan kasuwanci na yankin Arewa, Mohammad Ebije, cewa ya yi, akwai bikin auren da ba ya jan hankalin jama’a, saboda haka a irin wadannan bukukuwan mukan taimaka wa amarya ne kawai. “Idan kuwa muka samu labarin wani babban mutum zai halarci bikin, musammman sarki ko malami, sai mu garzaya; mu bayar da gudunmawa mu kuma tallata hajarmu,” inji shi.
Wani jami’in kasuwanci na Kano, wato Mista Monday, cewa ya yi, irin wannan gudunmuwar aure da kamfanin Prosimador ke bayarwa kashi-kashi ne, ya kuma dangata ga irin al’adun da mutanen yanki suka fi bai wa muhimmanci.
A cewarsa: “A Arewa muna taimaka wa bikin aure, kamar yadda a yankin Kudu maso Gabas muke tallafa taron watan Agusta na mata.”
Manyan manajojin kamfanin irin su Alhaji Ibrahim Yarima da makamantansu sun halarci wannan daurin aure da sauran bukukuwa don tabbatar da an yi amfani da kayansu, musamman sinadarin girki na ONGA don shirya abinci taryar baki.
Makadan  ONGA sun cashe a tsallaken titi, daura da masallacin Jami’ar Bayero ta Kano, yayin bikin.