✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda shaye-shaye da kwallon kafa ke hada kan Musulmi da Kirista

Kwallo za ta iya magance rikicin addini da kabilanci.

Jihohin Kaduna da Filato suna cikin jihohin da suka dade suna fama da rikice-rikicen kabilanci da na addini.

Yawancin yankunan Filato da Kaduna kabilunsu suna magana ce da Hausa a matsayin harshen sadarwa a tsakanin mabambanta kabilun.

Kuma irin shiga da al’adun jama’a a wadannan jihohi duk suna kama da juna. Wannan yana nuna yadda Hausawa da kabilun suka taso tun tale-tale tare da juna.

Faruwar rikice-rikicen a tsakaninsu

A baya-bayan nan Jihar Kaduna ta fara zama cibiyar rikce-rikice ce bayan rikicin Zangon-Kataf a 1992 a tsakanin kabilar Atyap wadanda yawanci Kirista ne da Hausawa wadanda Musulmi ne.

An fara rikicin ne a kan kasuwa, inda aka kashe Musulmi, su ma suka dauki fansa, inda lamarin ya kazance.

Tun lokacin ake zaman dar-dar, kafin a shekarar 2000 aka yi wani rikicin lokacin da Gwamnatin Jihar Kaduna, karkashin Gwamna Ahmed Muhammad Makarfi ta yi yunkurin fadada aiki da shari’ar Musulunci ga Musulmin jihar.

Bayan wannan, an sake rikici a shekarar 2002, lokacin da wata marubucin jaridar ThisDay, Isioma Daniel ta yi batanci ga Manzon Allah bayan gasar Sarauniyar Kyau ta Duniya.

An kuma yi rikice-rikice da dama kamar na zaben 2011 da sauransu, wadanda yawancinsu rikicin kabilanci ne suke rikidewa tarzoma su koma na addini, da suke jawo kashe-kashe da barnata dukiya mai yawa da kuma jikkata mutane da dama.

Kaduna ta rabu biyu

Saboda yawan rikice-rikicen, hatta babban birnin jihar ya rabu biyu, bangaren Musulmi da Kirista da kowa ya koma inda yake ganin ’yan uwansa sun fi yawa.

Hakan ya dada haifar da hadari ta yadda alakar zaman tare da ake da ita a tsakanin kabilu da mabambantan addini ta dada nisa tare da dada kyamar juna.

Mutanen da suka yi rayuwa a tare a baya duk da bambancin kabila da addini, sun bayyana wa Aminiya cewa rayuwar tasu ta da ta fi ta yanzu dadi da armashi.

Yadda ake zaman tare a da Wani mazaunin Unguwar Hayin Banki da ke Kaduna ta Arewa, Danjuma Rasheed ya bayyana cewa lokacin da suka taso, suna zaman lafiya tare da Kiristocin da suke unguwar.

Ya ce, “Muna kanana, mu ne muke kai wa abokan zamanmu sauran tuwo su ba al’adunsu.

“Sannan muna zuwa gidajensu, suna zuwa namu.

“Har coci ina raka su, sannan lokacin Islamiyya suna raka ni.

“Haka muka zauna lafiya har muka girma. Amma yanzu mun rabu. Da yawansu ma ban san inda suke ba.”

Unguwar Hayin Banki na cikin manyan unguwanni da suka hada Kirista da Musulmi da kabilu da dama a birnin Kaduna.

Wani mai suna Adamu Muhammad, ya bayyana yadda suka gudo daga Kasuwar Magani ana bin su, inda ya ce ba zai taba mantawa da lamarin ba.

“A can na taso cikin Kirista. Amma ina ji ina gani, aka koro mu, muna gudun neman tsira. An kashe mana ’yan uwa da dama. Ai ko da kudi ba zan koma yankin ba,” inji shi.

Shi kuwa Rabi’u Buhari da ke zaune a yankin Rigasa, ya ce sun zauna a Kudancin Kaduna, kafin su dawo Rigasa bayan an kona musu gida, kuma an kashe musu mutane.

“Akwai wadanda ma ko gawarsu ba mu gani ba,” inji shi.

Haka lamarin yake a bangaren Kiristocin da suka rayu a tsakiyar Musulmi, bayan rayuwa mai dadi su ma an kashe na kashewa an kuma kori na kora.

‘Yadda shaye-shaye da kwallo ke hada kanmu’

A duk lokacin da rikice-rikicen nan suka taso, an fi alakanta lamarin ga matasa masu shaye-shaye, marasa aikin yi.

Sai dai duk da cewa ana rikici da juna, ana kashe juna, Aminiya ta lura har yanzu matasan Musulmi da Kirista suna haduwa a wajen buga kwallo da wajen shaye-shaye, kuma ba sa rikici a tsakaninsu.

Ke nan su ne suka rura wutar rikicin, sannan su koma gefa su zauna tare suna harkallarsu ba tare da rikici ba a tsakaninsu?

Musa wani matashi ne da ke zaune a cikin Kaduna a matsayin Musulmi, amma da yamma ya koma yankin Sabo, da ke Kudancin Kaduna a matsayin Kirista.

“Shaye-shaye yake kai ni yankin, kuma saboda tsananin sabo da muka yi, sai suka nuna wa abokansu na can, cewa ni Kirista ne. Nakan yi kwanaki a can muna shaye-shayenmu, muna zuwa kwallo.

“Wata rana an fara rikicin Kaduna ina Kawo a yankin Musulmi, sai wadansu a can suka kira ni, in yi maza in dawo.

“Su asalin abokaina ne kawai suka san ni Musulmi ne, amma kuma duk runtsi ba su taba bayyana ni ba.

“Maganar gaskiya ban taba ganin rikici a tsakaninmu (mashaya) ba, saboda bambancin addini da kabila.

“Idan rikici ya rutsa da waninmu, ana boye shi ne, har rikici ya lafa ya tafi gida. Kuma za ka sha mamaki, ana can ana rikicin, muna can a boye muna shaye-shayenmu.

Simon, shi kuma Kirista ne da ya taso a cikin Musulmi, duk da iyayensa sun tashi sun koma wajen gari, har yanzu kullum yana cikin Musulmi a mattattarar shaye-shaye.

“A nan abin sha ba ya min wahala. Ko ba ka da kudi za ka sha.

“Maganar gaskiya Hausawa sun yi min komai, ba zan taba iya rabuwa da su ba. Babu maganar addini ko kabila a ‘jungle’ wato wajen shaye-shaye. Shaye-shayen ne ke hada mu, kuma muna zaman lafiya.

“Akwai lokacin da rikici ya rutsa da ni, iyayen wani abokina mai suna Abdulrasheed ne suka boye ni, har lokacin da aka gama rikicin, aka sa doka, sai babansu ya dauke ni a babur ya kai ni yankinmu,” inji shi.

Ya yi kiran a samar wa matasa aikin yi, wanda hakan a cewarsa zai sa su daina tunanin rikicerikice.

Salis, mawaki ne da yake zuwa wuraren masha’a daban-daban a Kudancin Kaduna, inda ya ce ya fi rayuwa a yankin.

Ya ce shi kulob yake zuwa rawa da shaye-shaye kuma yana tafiya da Hausawa maza da mata, kuma har mamaki ma yake yi idan ya ji ana rikicin addini ko kabilanci.

“Tabdi! Idan muna shayeshayenmu ba wanda yake tambayar addini ko kabila. Kuma idan ka je, kulob kananan wanduna da riguna matan ke sakawa, don haka ba a gane Musulmi da Kirista, kuma da dare ne ma a yawancin lokuta.

“Duk macen da ta yi maka za ka jawo ta ku yi rawa. A gama rawa, a je gefe a ‘cake’ sannan a watse.

“Babu ruwanmu da rikicin addini ko kabila,” inji shi.

Ba ya ga shaye-shaye, Aminiya ta gano cewa kwallon kafa ma na hada kan matasan kabilun da addinan sosai.

Aminiya ta lura idan magoya bayan kungiyar kwallon kafa suka hadu, babu ruwansu da kabilanci ko addini, inda akan yi fada tsakanin magoya bayan kungiyoyin, sannan su taimaki junansu a fadan ba tare da la’akari da bambancin addini ko kabila ba.

Ko a makon da aka kashe Deborah, dalibar da aka ce ta yi batanci ga Annabi (SAW) a Sakkwato, Aminiya ta ga matasa Musulmi da Kirista sun hadu a wajen kallon kwallon kafa, kuma ba a samu labarin inda rikici ya barke a tsakaninsu ba.

Haka duk rikice-rikicen da ake yi a Kaduna da sauran yankunan kasar nan, ko ana dokar hana fita, idan aka samu dama, matasa Musulmi da Kirista suna zuwa ko dai buga kwallo ko kallon kwallon tare, kuma ba a rikici a tsakaninsu.

Wani matashi da ya bayyana sunansa da Auwalu, ya ce shi magoyin bayan Kungiyar Manchester United ce, kuma babu ruwansa da wannan bambancin a wajen kallon kwallo.

“Ai kallon kwallo ka ce. Nan babu maganar bambanci. Ai su ma ’yan kwallon ba addininsu daya ba. Ko bambancin launi dan wasa ya nuna, sai an ci shi tara, ballantana bambancin addini,” inji shi.

Kwallo za ta iya magance rikicin addini da kabilanci -Koci

Wani kocin kwallon kafa a Kaduna, Bala Ibrahim ya ce idan gwamnati za ta sa hannu a kwallon kafa, za a iya rage yawaitar rikice-rikicen kabila da na addini.

Ya ce, “Da wahala ka ga dan kwallo yana fada.

“Kwallo yare daya ne, da duk duniya ana ji. Matasanmu da yawa sun fi son kungiyoyinsu sama da kabilunsu da kungiyoyin addinin da suke bi.

Addinin ne kawai ba za ka saka shi sama da kwallon ba. Kuma ga shi kwallon tana samar wa matasa aikin yi.”