✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda shagalin murnar dawowar Buhari ya gudana a Katsina

A makon jiya ne matashin dan siyasa Injiniya Muntari Sagir ya jagoranci dinbin masoya Shugaba Buhari na Jihar Katsina da kewaye, domin gudanar da gangamin…

A makon jiya ne matashin dan siyasa Injiniya Muntari Sagir ya jagoranci dinbin masoya Shugaba Buhari na Jihar Katsina da kewaye, domin gudanar da gangamin shagalin murna da farin cikin dawowar Shugaba Muhammadu Buhari gida Najeriya, bayan kwashe kwanaki 103 a birnin Landan yana jinya.

Gangamin ya hada al’umma daban-daban daga sassan Jihar Katsina, kamar kungiyoyin sa kai da kuma shuwagabannin Jam’iyyar APC reshen Jihar Katsina. An gudanar da tattakin daga babban ofishin Jam’iyyar APC na Jihar Katsina zuwa fadar mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman. Daga nan aka yada zango a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina.

Gangamin al’ummar ya sami tarba ta musamman daga Gwamna Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da mataimakinsa, Alhaji Mannir Yakubu da Shugaban Ma’aikata na Gidan Gwamnati, Alhaji Bello Mandiya tare da sauran mukarraban gwamnatin jihar.

A jawabinsa, Gwamna Masari ya jawo hankalin al’ummar Najeriya da su kara dukufa wajen ci gaba da yi wa Shugaba Muhammadu Buhari addu’o’in kara samun lafiya tare da samun nasarar tafiyar da harkokin jagorancin da ya rataya a wuyansa. Ya nuna farin cikinsa dangane da irin soyyayar da al’ummar Jihar Katsina suke nuna wa Shugaba Buhari.

A karshe, gwamna ya yi addu’ar Allah Ya kara wa Shugaba Buhari lafiya, Ya kuma zaunar da kasarmu Najeriya lafiya. Amin. An kammala gangamin lami lafiya ba tare da wata hatsaniya ba!