✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Sallar bana ta zo wa mutane

Yara sun saba muna zuwa wurin shakatawa amma ba na zaton a wannan Sallar za mu iya zuwa.

Bahaushe kan ce, ‘Sallah bikin daya rana’. Bayan ta wuce kuma a rika cewa, ta wuce ta bar wawa da bashi.

Kowace shekara kan zo da irin nata matsaloli da kalubalen a duk lokacin da ake fuskantar wata hidima ko wani sha’ani musamman lokutan bukukuwan Sallah da azumi ga Musulmi ko na Kirsimeti ga Kiristoci.

Sallar bana ta zo ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya suke farfadowa daga sumar da sauyin takardun kudi ya jefa ’yan kasar a ciki, bayan sun sha fama da matsalolin tabarbewar tattalin arziki da masassararsa da kuma kullen cutar Coronavirus a baya.

A Jihar Kaduna, Malam Haladu Abdu, mai sayar da kayan gwari a Kasuwar Kafanchan ya ce kayan sun fara sauka sai dai matsalar rashin wadatar kudi a hannun mutane na takaita ciniki.

Shi kuwa Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Nakasassu ta Jihar Kaduna, Malam Sulaiman Abdul’aziz ya ce lamarin ba a cewa komai musamman ga ’ya’yan kungiyarsu ’yan Allah-baku-mu-samu.

Malam Sulaiman ya ce, “Bar ma Sallah ba, azumi ma mun fuskanci kalubale sosai musamman kan batun takaita amfani da takardun kudi domin yawancin mutanenmu nakasassu ba su da asusun ajiya a banki.

“Mu ba ma batun hada-hadar Salla ce a gabanmu ba, muna batun abin sakawa a bakin salati ne tukunna.

“Ka ga mutumin da yake neman abin da zai ci yaushe yake batun kayan Sallah ga iyali da abinci da naman Sallah?”

Ya ce da zarar gari ya waye suna cikin dimuwar ina za su fara rayuwa ne, wanda hakan ya sa mutanensu bazama garuruwa don neman abinci.

Musa Muhammad, wani tela a Kasuwar Kafanchan, ya shaida wa Aminiya cewa sun fahimci mutane na cikin matsi musamman ganin yadda azumi ya kare Sallah ta gabato amma ba su samu dinki mai yawa kamar bara da sauran shekarun baya ba.

Shi ma wani tela, Malam Abdulkarim Dayyabu ya ce ga telan da yake samun dinkin Sallah goma a bara to bana da kyar ya samu biyar saboda mutane ba ta dinki suke ba a yanzu.

Wani magidanci Ado Jume, ya ce batun dinkin Sallah ga mai ’ya’ya sai wane da wane, saboda tsadar rayuwa da tsadar kayayyaki da ake ciki.

Ya bayyana kananan ma’aikata da matsakaita a matsayin wadanda su ma abin ya shafe su.

Wani magidanci mai sayar da takalma Malam Adamu Muhammad Lawal ya ce su ma suna fuskantar kalubale a kasuwancinsu kamar sauran takwarorinsu, inda ya ce idan aka kwatanta da bara, kasuwancinsu ya yi kasa matuka.

Yawancin wadanda Aminiya ta zanta da su, sun alakanta matsalolin da batun sauyin kudi da aka yi a bana.

A Jihar Legas, Malam Kabiru Yusuf wanda dan jarida ne, ya ce Sallar bana ta zo wa al’ummar Najeriya da matsaloli da dama na rashin wadata.

Ga karancin kudi da rashin kudin a hannun jama’a.

Shi ko Malam Rabi’u Dan’azumi mazaunin garin Idi Araba a Legas cewa ya yi, Sallar ta zo a wani irin mawuyacin hali duba da burbushin matsalar da ta biyo bayan sauya fasalin kudi, “Amma duk da haka wasu sun yi iya kokarinsu, an yi wa yara kayan Sallah daidai gwargwado.

“Bukatun an yi wadanda suka samu wadanda kuma ba a samu ikon yi ba an hakura,” in ji shi.

Malam Danladi Mustafa ma’akaci da ke zaune a Ikeja, Legas ya shaida wa Aminiya cewa bana Sallar ta zo wa ma’aikata a tsakiyar wata duba da yadda ta zo, kasa da lokacin da mafi yawan ma’aikatu da kamfanoni da ma gwamnati ke biyan ma’aikatansu albashi.

A kasuwanni da dama da Aminiya ta zagaya a Jihar Legas da suka hada da Kasuwar Kayan Abinci da ke Mil 12 da ta Ilepo da Kasuwar Sutura ta Idimota, ’yan kasuwa sun koka da rashin ciniki, sun kuma alakanta rashin cinikin ne da karancin kudi da kuma rashin albashi ga ma’aikata.

A bangaren teloli da Aminiya ta zanta da su a jihohin Legas da Ogun sun ce suna samun ciniki sosai.

Malam Abubakar Fulani tela ne a garin Sabo Abeokuta a Jihar Ogun ya ce ya samu dinkin jama’a fiye da yadda ya zata.

Mafiya yawan mutanen da Aminiya ta zanta da su sun ce a cikin matsalolin rashin isassun kudi a hannun jama’a da rashin gudanar al’amuran kasuwanci za su yi Sallar ta bana.

Wani magidanci a Damaturu ya ce, “Ni yanzu ba ta bikin Sallah nake yi ba, ina ta kaina ne wato ina fafutikar yadda zan samu masarar da za mu ci ne.”

Shi kuwa Malam Muhammad Bello na Unguwar Nainawan da ke Damaturu cewa ya yi babu abin da za su ce sai godiya ga Allah, “Domin azumin ma a daddafe muka yi saboda matsalar rayuwa ballantana hidimar Sallah da ke bukatar yi wa iyali suturu da sauran kayayyaki,” in ji shi.

Shi kuma Malam Muhammad Maiyadi cewa ya yi, “Babu kwatanci tsakanin Sallar bara da ta bana a kan ciniki, domin bara an yi ciniki matuka, amma bana sai dai godiya ga Allah.”

Da Aminiya ta tuntubi Malam Abdulmumini mai kayan miya a Kasuwar Damaturu kan ko yaya yanayin cinikin Sallah bana, sai ya ce kasuwarsu ba ta ci yadda suka saba gani ba.

“Tun lokacin da aka ce za a canza fasalin Naira al’umma suka fada cikin mawuyacin hali kuma har yanzu sai dai kawai a ce sun fara samun sauki,” in ji shi.

A Jihar Kano, za a iya cewa ana cikin halin kai kuka ne, nitagumi, saboda sauya fasalin takardun kudi ya taba harkokin kasuwanci a jihar.

Duk da cewa yanzu rashin takardun kudi ya ragu, sai dai inda gizon ke sakar shi ne irin yadda mutane suke kokarin ganin sun gudanar da bikin Sallah kamar yadda suka saba.

Hajiya Ummi Bala ta shaida wa Aminiya cewa ba kamar yadda suka saba gudanar da Sallah ba.

Ta ce, “Sai nake jin kamar ba Sallah za a yi ba, domin a yanzu haka ’ya’yana mata ko kayan Sallah daya ba su da shi a hannu, domin kuwa kayansu na wurin tela kasancewar ba a sayi kayan da wuri ba.

“Wannan ya faru ne saboda halin da aka samu kai a ciki.

“A da mun saba kafin a fara azumi mun kammala sayen duk kayan Sallah kuma a wancan lokacin ba guda daya kawai ba amma a yanzu da kyar aka sayi dayan wanda kuma sai a makon nan ne aka saya.

“Sauran kayan kwalliya na yara kuma sai a hankali.”

Wata matar aure da ke da ’ya’ya biyar da ta nemi a boye sunanta ta shaida wa Aminiya cewa.

“To mu dai babbar godiyarmu ga Allah ita ce muna da rai da lafiya.

“Amma batun Sallah sai dai a yi maleji domin yanzu farashin kowane kaya ya tashi.

“Na shiga kasuwa don saya wa yara takalma da su ’yan kunne amma farashin kayan ya sa ban samu sayo su duka ba. Sai dai yara su yi hakuri a wannan karo.”

Wata mai sana’ar lalle mai suna Asiya Magaji ta ce ba kamar yadda aka saba ba domin, “A gaskiya na yarda mutane babu kudi a hannunsu, saboda a da idan ya rage kwana shida zuwa biyar Sallah ake fara zuwa yin lalle.

“Amma bana ina ganin sai a ranar Talata na fara samun masu zuwa.

“Kuma ba kamar da ba da zan yi wa mutane masu yawa a yanzu kuwa babu wannan yawan.

“Kin ga wannan soron da tsakar gidanmu da a baya ne a cike za ki same su da mutane, amma yanzu ki duba bai fi mutum uku ne suke kan layi ba.”

Aminiya ta tattauna da wata uwa Maman Aarif kan rashin zuwan lallen sai ta ce, “To yanzu ta kai ake yi.

“Yaushe za ki dauki makudan kudi ki kai wa mai lalle.

“Kin san su ma yanzu masu lallen sun kara kudi. Ko yarinya za a yi wa lalle sai ki ji an ce Naira dubu daya za a biya.

“To ni mai yara biyar kin ga dubu biyar ke nan bayan nawa wanda watakila sai Naira dubu biyu.

“Shi ya sa na sayo lallena na sayo salatif dan yanka za mu yi a gida.”

A bangaren ma’aikata a jihar kuwa sun ce ba su sa rai da samun albashi kafin Sallah ba don haka ba su yin dokin zuwan Sallar.

Malam Alkasim Bashir ya ce za su yi bikin Sallah ne a yadda ta zo musu kawai.

“To ina mutum zai yi dokin zuwan Sallah bayan ba ya da kudi a hannu.

“Abin da ake kokari yanzu shi ne a sama wa yara dan sabon kayan da za su sa su je Sallar Idi.

“Ni da matata kuwa sai dai mu hakura. Kin ga ko a bara ma ba mu yi Sallah da albashi ba.

“Haka muka yi a takure. Sai dai a gaskiya bara ta fi bana, domin a wancan lokacin tsadar rayuwar ba ta kai haka ba,” in ji shi.

Wata ma’aikaciya ta ce ba ta zaton Sallar za ta yi armashi duba da rashin kudi a hannun mutane.

“Kin ga na farko akwai tsadar rayuwa dama ga matsalolin da muka shiga iriiri a kasar nan, to ta yaya za mu iya samun kudin da za mu yi hidimar Sallah?

“Kin ga a da, baya ga wadata yara da kaya su ’yan kunne da sarkoki da nake yi, idan ya rage kwana biyu Sallah nakan yi cincin da zan raba wa baki idan sun zo gaisuwar Sallah.

“Amma a bana da na yi lissafi na ji kudin da yawa sai na ajiye batun yin cincin.

“Haka yara sun saba ina daukar su mu je wurin shakatawa a lokacin Sallah wanda kudi ake biya.

“Ba na zaton a wannan Sallar za mu iya zuwa duba da halin da muka samu kanmu a ciki.”