✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rigimar Matawalle da Gwamna Lawal ta jefa ma’aikata cikin tsaka mai wuya a Zamfara

Ba siyasantar da lamarin muka yi ba, tantance ma’aikata muke yi a halin yanzu.

Akalla ma’aikatan Gwamnatin Zamfara 100 da suka karbi mukaman siyasa a tsohuwar gwamantin jihar suke fama da kuncin rayuwa, bayan da suka kwashe kimanin wata bakwai zuwa takwas ba tare da albashi ba.

Dalilin fadawarsu wannan yanayi shi ne, gwamnatin tsohon Gwamna kuma Minista a Ma’aikatar Tsaro Alhaji Bello Matawalle, ya dauki wasu ma’aikatan jihar ya ba su wasu mukamai na siyasa.

A al’adance kamar yadda suka bayyana wa Aminiya a kowace gwamnati a Jihar Zamfara tun daga Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura har zuwa Bello Matawalle, akan dauko ma’aikatan gwamnati a ba su mukaman siyasa daga bisani kuma idan gwamnatin ta kare sai su koma wuraren aikinsu na baya.

Sai dai akwai bayanai da suka ce zuwa wannan gwamnati, sai ta ce duk wanda ya karbi mukamin siyasa daga cikin ma’aikatan gwamnatin tamkar ya ajiye aikinsa ne.

Shin wane hali wadannan tsofaffin mukarraban tsohon Gwamna suke ciki a yanzu? Kuma yaya suke kallon dokar da ta ce duk wanda ya karbi mukamin siyasa tamkar ya ajiye aikinsa ne baki daya?

Aminiya ta tuntubi wasu daga cikin irin wadannan ma’aikata da ba su san makomarsu a yanzu ba.

Jamilu Haruna Karale, tsohon Babban Darakta a Hukumar Bunkasa Harkokin Wasanni ta Jihar Zamfara, ya shaida wa Aminiya cewa kafin a ba shi mukamin siyasa yana ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar ne.

Game da shafe wata bakwai ba su da albashi ya ce “Gaskiya babu dadi ko kadan domin idan aka ce wannan ma’aikaci ne ko kana da wata sana’a albashi ne babbar madogara ta farko kafin wata madogara ta biyu ta zo.

“Watannin da muka yi can baya lokacin gwamnatin da ta wuce ta Matawalle mun yi wata uku ba a biya mu albashi ba, sannan yanzu an yi wata hudu ga shi za mu shiga wata na biyar a wannan gwamnati ta Dauda Lawal babu albashi.

“Yanzu ka ga an koma makaranta yaranmu ba su iya zuwa makaranta wasunmu da yawa suna da iyalai mata daya, biyu, har hudu.

“Wasu manyan malamai ne daga cikinmu, ba mu iya daukar nauyin iyalanmu akwai rauni sosai, wannan rashin albashin ya tauye mu matuka wajen gudanar da harkokin rayuwarmu.”

‘Doka ta ba mu dama mu jingine aiki mu karbi mukamin siyasa’

Game da cewa idan mutum ya jingine aiki ya karbi mukamin siyasa tamkar ya ajiye aiki ne, Jamilu Karale, “ya ce a ka’ida ta aikin gwamnati koda kana da wani matsayi wata gwamnati ta ba ka, ko da ba ta jiharka ba ce, in ka tafi koda kamfani ne, doka ta ba ka dama ka rubuta hutu ba tare da albashi ba, cewa za ka tafi na wani lokaci, shekara hudu ne ka’ida kuma ana iya kara maka da shekara guda, wato shekara biyar.”

Ya ce akwai kuma wani abu makamancin haka, “za a yarje maka ka je wani wuri aiki na shekara biyu kuma ana kara maka wasu shekara biyu a karo na biyu.

“Idan ka cika shekarar nan hudu, to doka ta ba ka dama ko dai ka dawo in ba ka aiki, ko kuma a yi ma canjin wajen aiki ka koma can baki daya.

“To mu gwamnatin jiha ta ba mu aiki kuma ita muka yi wa aiki, don haka ita ya kamata ta biya mu amma ba a biya mu albashin wata bakwai a halin yanzu,” in ji shi.

Sai ya ce a halin da ake ciki yanzu na rashin tsaro wannan zai kara jefa al’umma cikin masifa da bala’i, domin wanda ya rasa abin da zai yi lalura ta yau da kullum in bai kai zuciya nesa ba komai zai iya faruwa.

“Saboda haka da daukar ma’aikata a kai a kai, da biyan su albashi cikin lokaci da kyautata musu na da kyau domin kawar da su daga abubuwan da ba su dace ba,” in ji shi.

Ya ce, “Saboda haka ina kira ga gwamnati ta duba halin da muke ciki ta dubi yiwuwar biyanmu albashinmu na wadannan watanni domin wa gwamnatin Jihar Zamfara muka yi wa aiki ba Matawalle ba, ba Gwamna Dauda Lawal ba. Gwamnatin Jihar Zamfara ita muka yi wa aiki.”

Shi kuwa Lukuman Majidadi tsohon Mai ba da Shawara ga Gwamna a Hukumar ba da Tallafin Karatu ta Jihar Zamfara, kuma malami a Kwalejin Harkar Noma da Kimiyyar Dabbobi ta Jihar Zamfara, ya ce suna cike da mamaki ganin cewa duk inda aka fito ba a taba wani yunkuri na siyasa tare da aikin gwamnati ba, irin wannan karo.

Ya ce “Duk inda aka fito ana bai wa ma’aikata dama duk wanda Gwamna ya ji yana ra’ayi ko gwamnati mai ci ta ji tana ra’ayi da wani ma’aikaci ya zo ya yi mata aiki, a matsayin mai ba da shawara ko makamancin haka, to takan gayyato shi kuma tunda dai duk aiki ne na jiha.

“Kafin mutum ya je sai ya rubuta cewa ya tsayar da albashinsa a ma’aikatar da yake sannan ya zo ya yi wa gwamnati aiki a inda aka tura shi.

“Wannan abu ne da aka saba yi tun zamanin Yariman Bakura zuwa ga Gwamna Lawal. Kuma duk wanda ya tafi yakan dawo.

“Kamar shi ma Gwamna yanzu akwai ma’aikatan da ya dauka ya yi wa mukamai na siyasa.”

Lukuman Majidadi ya ce a bangaren tattalin arziki, “Muna cikin mawuyacin hali, idan ka dubi rayuwar mai karɓar albashi yaya rayuwar take? Balle a ce mutum ya yi kusan wata bakwai babu albashin.

“A tsohuwar gwamnati mun yi wata uku ba albashi, sannan yanzu kuma wata hudu babu.

“Yanzu masu albashi sai su kwatanta yadda suke kashe kudinsu wajen hidimar abinci, kudin makarantar yara da sauransu.

“To mu da ba ma karba wane yanayi muke ciki ke nan?”

Ya ce wannan doka da ake magana a kanta duk labari ne domin ba su san da ita ba.

“Duk maganar da muke har yanzu babu wanda ya zo ya ce mana mun taka wata doka ko mun saba wata ka’ida, hasali ma zuwa aka yi aka tantance mu aka tabbatar da cewa duk lafiya muke za a fara biya.

“To kuma sai muka ji shiru bayan an tantance mu za mu koma bakin aiki.

“Abin ya zama al’ada a Jihar Zamfara duk wata gwamnati in ta zo sai ta yi kokarin ganin cewa ta tantance ma’aikata, don haka mu ma an tantance mu.

“An ga lokacin da aka ba mu wadannan mukaman mun rubuta wa hukumominmu, kuma hukumomin sun rubuto mana takardun cewa sun gani suna mana fatar alheri, sun ba mu dama mu je mu yi wannan aiki tunda duk aiki ne na ci gaban jiha, idan mun gama mu dawo.

“Ita ma wannan gwamnati ta dauko wasu daga gwamnatin jiha da ta tarayya kuma in sun kare ana sa ran su koma ma’aikatunsu,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Don haka mu ma haka muke zato tunda ga dokar aiki (civil service rules) tun daga kowane mataki mun san cewa kana iya daukar aiki na siyasa ko leave of absence ko study leave ko ka je ka yi aiki da wata kungiyar da ba ta gwamnati ba, ko ka je ka yi wa gwamnati aiki a wani mataki na daban.

“Amma abin da ba a yarda da shi ba ka hada ayyuka biyu a lokaci daya.

“A Jihar Zamfara duk wanda yake ma’aikaci ne ya san ana irin wannan abin ka je wani wuri ka yi aiki da kawo, ba ma a Zamfara kadai ba dukkan jihohin kasar nan.

“Abin da muka sani na doka shi ne idan za ka yi takara to dole sai ka ajiye aikin gaba daya.

“Kuma mun bi duk hanyoyi da matakan da suka kamata mun bi domin a mayar da mu bakin aiki.

“Har ma mun je ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar Zamfara ya tabbatar mana da cewa in yau Gwamna Dauda Lawal ya ce ya tura a Ma’aikatar Kudi a biya mu zai tura.

“To ka ga a kaikaice ana nuna mana cewa Gwamnan Jiha ne ake jira a biya mu.

Sai shi ma ya yi kira Gwamna Dauda Lawal ya duba halin da suke ciki ya dubi yanayin da hakan ya jefa iyalansu a ciki sanadiyyar wannan.

“Na biyu, Gwamna Dauda Lawal ya duba ya tabbatar da cewa ya kira duk wadanda abin ya shafa ya ba da umarni nan take a mayar da kowa bakin aikinsa a biya shi albashinsa a ci gaba da tafiya.

“Na uku shi ne ya duba albarkacin aikin gwamnatin da yake kokarin gyarawa, idan aka yi haka lallai an sunnanta wani abu ga aikin Jihar Zamfara wanda yake zai zama illa wadda ba a taba yi ba.

“Kuma tarihi ba zai taba cewa gare shi aka fara zuwa in ka rubuta a hukumance cewa ka tafi wani aiki kuma in ka dawo a ki mai da ka.

“Duk wani gyara da fasali da za ka yi wa aikin gwamnati idan ka karya wannan lagwan to tabbas ka yi illa ga aikin gwamnati Jihar Zamfara.

“Wannan shi ne kirana ga Mai girma Gwamna Dauda Lawal Dare,” in ji shi.

Muna bincike da tantance ma’aikatan — Gwamnatin Zamfara

A bangaren gwamnatin Jihar Zamfara ta musanta zargin da ake mata na siyasantar da lamarin, inda ta ce yanzu haka tana kan tantance ma’aikatan jihar.

Mustafa Jafaru Kaura, Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar kan Harkokin Labarai shi ya bayyana haka a hirarsa da Aminiya.

“Dama ita Jihar Zamfara takan samu irin wadannan matsaloli, idan aka gama tantance ma’aikata, idan aka gano wasu suna karbar albashi biyu, za ka ga mutum yana karbar albashin ma’aikatar da ya baro da kuma karbar albashin muqamin siyasa da aka yi masa a lokaci daya.”

Ya ce ba siyasantar da abin aka yi ba, “Yanzu haka akwai wasu mutanen da suka fi wadannan da suke koken cewa an hana su hakkokinsu masu yawa, su ma ba sa samun albashi, saboda matsalar da suka samu a wani wurin, to ka ga su wadannan ba wai sun taba rike wani mukamin siyasa ba ne a gwamnatin da ta gabata, ka ga ke nan wannan matsala ba su kadai ta shafa ba.”

Jafaru ya ce “Don haka su sani cewa Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, ba ya da wata manufa ko kudiri na siyasantar da lamarin, don sun rika mukaman siyasa a gwamnatin da ta gabata.”

Mustafa Kaura ya ce wannan batu ba ya da wata dangantaka da gwamnatin Matawalle, “kawai dai akan samu wasu matsaloli ne na daban bayan an gunadar da bincike, wato ko dai matsalar BVN ko a samu mutum yana karbar albashi biyu.

“Bayan wannan kuma akwai matsalar manhajar tattara bayanan ma’aikata wato (Data Capture) da muke fama da ita wadda tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Abdul’aziz Yari ya samar domin tantance ma’aikata, wadda ita ma wasu lokutan tana kawo tsaiko wajen biyan albashi.

“Idan ya kasance a lokacin da ake tantancewa da kuma shigar da bayanan ma’aikata, mutum ya samu akasin rashin zuwa ko kuma makamancin haka, wannan zai yi masa cikas a wurin samun hakkokinsa,” in ji shi.