Karamin Ministan Tsaro kuma tsohon Gwamnan Zamfara, Mohammed Bello Matawalle, ya kalubalanci ’yan Arewa masu mukami a Gwamnatin Shugaba Tinubu su fito su kare ta daga caccakar da take sha daga jama’ar yankin.
Matawalle ya yi wannan kira ne bayan tsohon kakakin Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Hakeem Baba-Ahmed, ya yi masa martani a Facebook kan ayyana kungiyar a matsayin ’yar amshin shata mai ra’ayin siyasa.
Matawalle ya kira ’ya’yan kungiyar ’yan amshin shata masu ra’ayin siyasa ne, bayan kakakinta, Abdulaziz Suleiman, ya bayyana nadamarsu kan goyon bayan zaben Shugaba Tinubu.
Hakeem Baba-Ahmed, wanda a yanzu shi ne mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa a ofishin mataimnakin shugaban, kasa ya ce, “Zai fi kyau Matawalle ya fito ya tallata kyawawan ayyukan Tinubu ta ofishinsa na ministan tsaro.”
- Muna Nadamar Zaɓen Tinubu — Dattawan Arewa
- Zargin Rashawa: APC ta dakatar da Ganduje
- Masu iƙirarin dakatar da Ganduje ba ’yan Jam’iyya ba ne —APC
Da alama dai wannan shawara ta Hakeem ba ta yi wa Matawalle dadi ba, lura da yadda ya bayyana cewa ya zama wajibi duk wani mai rike da mukami a Gwamnatin Tinubu ya fito ya bayyana matsayarsa.
Ya ce, “Da alama bayyana matsayata a kan kalaman kakakin Kungiyar Dattawan Arewa game da Gwamnatin Shugaban Tinubu, ba su yi wa Dokta Hakeem Baba-Ahmed dadi ba, wanda ya taba rike mukamin kakakin kungiyar, tun da har yana cewa in fito in bayyana abububbuwan alherin da gwamnatin ta yi.
“Alakar Baba-Ahmed da kungiyar Dattawan Arewa sananniya ce. Maganar gaskiya a yanzu shi ne ya zama wajibi a gare shi ya yi aiki tukuru domin ganin gwamnatin da yake cikinta ta yi nasara, ya yi kokarin kare ta daga masu kalamai na kabilanci da rura wutar bangaranci da kuma kalaman hamayyar siyasa.
“Ya da ce duk wanda Shugaba Tinubu ya nada ciki har da Dokta Baba-Ahmed, ya sani cewa gwamnati na da babban nauyi a wuyarsa na bayyana ayyukan alherinta da kare martabarta daga makiya masu son ganin ta fadi.
“A matsayinmu na ’yan Arewa masu mukamai a wannan gwamnatin, ya zama wajibi kowa ya fito fili ya bayyana matsayarsa a game da wannan gwamnatin kuma ya goyi bayanta domin kaiwa ga gaci.
“Yanzu ba lokaci ba ne da za mu zuba ido muna gani ana ci wa sabuwar gwamnatinmu mutunci da bata mata suna.
“Dole ne mu bayyana kokari da nasarorin da Shugaba Tinubu ya samu, domin muna cikin gwamnati,” in ji Bello Matawalle, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara.