✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda nake amfani da lantarkin hasken rana a gidana da motata – Isma’il

Injiniya Isma’il Musa Ahmad (ISMAH) ya shaida wa Aminiya cewa rashin wutar lantarki da tsadarta suka sa ya koma da amfani da hasken rana domin…

Injiniya Isma’il Musa Ahmad (ISMAH) ya shaida wa Aminiya cewa rashin wutar lantarki da tsadarta suka sa ya koma da amfani da hasken rana domin samar wa gidansa da wurin sana’arsa da motar hawarsa wutar latarki ta amfani da hasken rana.

Me ne tarihinka?

An haife ni ranar 15 ga Satumban 1950, shekara 67 ke nan a birnin Kano. Na yi karatun firamare a Rimi daga na wuce Cibiyar Bunkasa Ilimi ta Jihar Kano (KEdC) a 1969 inda na kammala a 1974. Na yi aikin a Kwalejin Horar da Malamai Mata (WTC) da ke Kano da Kamfanin BEMCO da kuma Kamfanin Ado Yau. Na bar aiki na koma birnin Landan domin karo ilimi a matakin difloma a fannin ilimin kimiyyar lantarki a Kwalejin Ilimin Kimiyya da Kere-Kere da ake kira Elephant and Castle da ke birnin Landan. Amma saboda karancin kudi na Fam din Ingila 105 na bar karatun. daga nan na nufi kasar Japan inda na koyi ilimin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana. 

Me ya sa ka ce a cire maka wayar wutar lantarki a gidanka ka koma amfani da ta hasken rana?

Ina zaune ne a Hotoro cikin birnin Kano na ga ana ta kara min kudin wutar lantarki amma ba a samun wutar. Na lura Hukumar NEPA, wadda ta koma Kamfanin PHCN sannan ya koma KEdCO/dISCO wato na ’yan kasuwa, sai na ce lallai ne in samo mafita. Nan na hada kaya na sa wa gidana wutar lantarki har da na na’urar talabijin da samar da ruwan sanyi.

Yaya kake da ma’aikatan wadannan kamfanoni na PHCN da KEdCO/dISCO?

Idan an yi sauyin manaja na ma’aikata masu kula da bangaren gidana sai su ce don me za a wuce wannan babban gida? Sai ma’aikatan su yi dariya su ce a kira ni, sai in ce masa ya nuna min wayar da ta shiga gidana, sannan sai in ce masa ya zo ya gani cikin raha, sai ya ga ai ina amfani da na’urar ‘sola’ mai amfani da hasken rana ne ba ruwana da KEdOC/dISCO. Sai ya ba ni hakuri ya ce ya gane.

Ban da gidanka me kake amfani da shi ta hanyar hasken rana?

Ina da mota da na daina sayen man fetur domin ya yi tsada sai na hada mata na’urar samar da hasken wutar rana da batir da sauran na’urorin don tafiyar da motar kira Toyota Starlet. Sannan akwai Keke NAPEP da na kera mai taya uku wanda na taba zuwa Abuja da shi wurin taron baje kolin kere-kere na kasa bayan na baje koli a Kasuwar duniya ta Kano. 

Nawa ka kashe don kera Keke NAPEP din?

Na kashe Naira dubu dari ne kuma a cikin mako biyu don kera motar. Kuma na kwashe kwana biyu daga Kano zuwa Abuja da motar mai taya uku. da zan je Abuja, na tsaya na kwana a Kaduna, washegari na wuche. Ita Toyota Starlet din na daina amfani da injin ne na hada mata na’urar samar da hasken rana.

Mene ne burinka?

Sunan kamfanina ISMAH Solar kuma ina fatan gwamnati ta tallafa wa mu masu basira na cikin gida don ciyar da kasa gaba. Ya dace a rika turo mana matasa muna koya musu wannan ilimi domin a sama wa gidaje da makarantu da asibitoci da sauransu wutar lantarki da hanyar hasken rana ba tare da an dogara da kafar samar da lantarki daya ba, kuma hakan zai sama wa matasa ayyukan yi.