✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda na zama dillalin mota daga sayar da katin waya’

Aminiya: Me ya sa ka bar sayar da katin waya ka shiga harkar kasuwancin mota?Da farko dai sunana Sabitu Ahmad Ibrahim. A baya ina sayar…

Aminiya: Me ya sa ka bar sayar da katin waya ka shiga harkar kasuwancin mota?
Da farko dai sunana Sabitu Ahmad Ibrahim. A baya ina sayar da kayan waya ne wato katin waya da sauransu, sai wani abokina wanda ya amince da ni kuma Alkali-Kotun Majistare mai suna Ibrahim ya kawo mini motarsa kirar Honda Cibic 2002 ya ce na yi dillancin ta. Sai na sa namban waya ta a jikin motar kamar yadda ake yi a Abuja domin duk mai so ya kira ni. Sai ko akai gamo da katar har na samu mai so, bayan ciniki ya kaya, sai na ce ya tura kudin zuwa asusun bankin mai motar. Da mai motar ya ga kudi ya shiga ta alamar sakon karta kwana na wayyar hannu, sai na ba da makullan motan.
Ba na cewa nawa za a ba ni. Idan na sayar da mota duk abin da mai mota ya ba ni karba nake na ce nagode. Haka dai ina dillancin mota, ina sayar da katin waya.
Ana cikin haka sai hukumar tsabtace birnin Abuja ta rushe mini shagon sayar da kati da kayan waya, sai na ci gaba da dillancin mota. A takaice ina iya cewa wannan rushe mini shago ya zama mini gobarar Titi don sai aka ci gaba da kawo mini motoci da yawa a ban farashi. Ana kawo mini mota da masu tsada da masu arha don na yi dillancinsu.
A yanzu na shekara bakwai a unguwar Kado ina sayar da mota, sannan na shekara uku da fara zuwa garin Kwatano na Jamhuriyar Benin don sayo mota nawa na kaina.
Aminiya: Ya kake yi da motocin idan dare ya yi?
Daga nan bakin titi, akwai gidan da nake kai wa na aje su har sai gari ya waye, sai ni da abokina mu dauko su mu kawo su nan.
Aminiya: Ya aka yi ka fara safara don sayo mota ta kanka?
Daga abin da ake ba ni ne na yi tattali har na fara sayen na kaina a kasar Benin wato birnin Kwatano. Akwai wani abokina Bashir, shi ya fara kaini Kwatano inda muka hau mota daga nan zuwa Legas, shi ya nuna mini hanya har na fara sayo mota na zo nan Abuja na sayar.
Aminiya: Wace irin mota ka fara sayo wa?
Na fara sayo mota kirar Honda Cibic wacce ake cewa Panadol-Estira ko Mai-Idon Kifi. Kuma a yanzu ina hada dillancin mota da na gidaje don na kara samin kudin shiga don na rufa wa kaina asiri. Kuma har yanzu ina zuwa ina sayowa don na saida.
Aminiya: Yanzu ka bar harkan kayan waya ke nan?
Eh, na bari domin kuma an rusa mini shago. Yanzu na fi karfi a wannan harka ta dillancin mota da gidaje.  Domin a yanzu akwai motoci biyar, biyu nawa, sannan uku na mutane. Kuma ban da matsala da kowa don ina da kokarin rike amana.
Aminiya: Idan mutum ya ce yana son mota ya kake yi?
Za mu yi yarjejeniya, ya ba da kudi a sayo masa mota, idan an kawo mota ta yi masa shike nan, idan ba ta yi ba sai ya jira mu saida sannan mu musanya masa.
Aminiya: Ya kake da sadarwan zamani a harkan ka?
Idan an zo sayen mota a wannan zamani, ni ina nan Abuja zan yi magana da wanda yake Kwatano sai ya turo mini hoton motan, cikin da wajenta ta wayar hannu tsarin WhatsApp sannan in nuna wa mutum, idan ta yi masa, sai ya ba da kudi a sayo masa. Don a yanzu ba sai na je Kwatano da kaina ba don sayo mota.