✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na zama biloniya – dangote

‘Mutumin da komai ya taba a harkar kasuwanci sai ya zama dukiya’ Mun hadu da hamshakin attajiri cikin watanni kadan, amma dimbin ayyukan da suka sha…

‘Mutumin da komai ya taba a harkar kasuwanci sai ya zama dukiya’
 Mun hadu da hamshakin attajiri cikin watanni kadan, amma dimbin ayyukan da suka sha mini gaba suka hana ni yin bayani a kan wannan al’amari. Ranar farko da na samu izinin ganawa da Aliko dangote, a ofishin sa da ke Apapa, sai da na jira tsawon sa’a guda kafin  in samu isa wajen sakatariyarsa, wadda ta sanar da ni cewa shugabant ana cikin ofis yana ganawa da wani, kuma ya ce kada a dame shi. Sai aka sake sanya mini wata rana, sai dai a wannan karon ni ne na ki zuwa, saboda yakin Tekun Fasha ya barke da safiyar da muka yi alkawari, don haka dimbin ayyuka sun taru a teburina, inda nake bibiyar al’amuran da ke wakana. Daga bisani na koma bayan kwana biyu, don neman afuwa, da bukatar a sake sanya mini wata rana.
Wani abu da ya jefa ni cikin mamaki shi ne, an yi mini tarba mai kyau, inda sakatariyarsa ta yi mini iso har cikin ofis, ya kuma ba ta umarnin ta deakatar da duk wasu kiraye-kirayen waya, har ma da masu ziyara. Domin dangote ya fi son kammla aikin da ke gaban sa kafin ya shiga wani.
A cikin wani katafaren ofis na alfarma, wanda ke da bangare uku (daya na dauke da teburin shirya taron tattaunawa, wani kuwa da wurin zaman baki kawai); teburin yana can da nisa, a wata kusurwa, inda  tsawonsa ya yi nesa daga masu hange ta kofa. Za dai a yi tattaski sosai kafin a isa inda yake, al’amarin da ke bai wa wannan matashin hamshakin attajiri damar yin nazarin bakinsa, su ma bakin su samu damar kallon wannan wuri mai ban sha’awa.Tsawon lokaci na yi in kallon kwalbar koka-kola da ke kan teburin sa, inda miyauna ya guda har na yi fatan  ya ba ni wannan abin sha. Sai dai wani abin mamaki , ashe wannan kwalbar lemu da na gani, kan abin wayar tarhon da yake amfani da shi wajen kran sakatariyarsa! Baya ga wannan dai shi mutum ne mai karamci, koyeka an killace shi, saboda a loikacin da na fara zubo masa tambayoyi, sai muka manta da duk wata nima da kawar da ke cikn fishin sa. Sai dai abin da kawai ba manta ba, shi ne, yadda a karancin shekaruna (da baya son bayyanawa, na dai san na girmeshi) ya zama hamshakin attajiri a rukunin attajran Najeriya!
Da farko dai ya fara gwada sa’ar sa a kamfanin sufurin kawunsa mna tsawon shekara guda, sai kuma kakansa na wajen uwa, Alhaji Sanusi dantata, ya saya masa manyan motoci uku, a lokacin yana da shekara 19, don ya dogara da kansa.. Baya ga harkar sufuri, ya shiga cikin harkar gine-gine, lokacin da ake bayar da kwangilolin gina makarantu a karkashin tsarin ilimi na UPE da aka aiwatar a shekarun  1970. Harkokinsa sun bunkasa ne a shekarar 1977, a daidai lokacin day a yanke matsaya wajen mayar da ofishinsa Legas daga Kano. Kakansa ya soki lamirin wannan dabara, amma da ya samu aminan kakansa suka lallame shi, sai ya kyale Aliko ya yi wannan kasada, duik da karancin shekarun sa da rashin gogewarsa. Wanda ya zama sanadiyyar motsawata, Alhaji Usman dantata, kawuna mai yawan kurda-kurdca a wurare daban-daban, kuma tuni ya gano cewa, Kudi na Legas ba Kano ba.
“Abin da ya kawo ni Legas a karo na farko, cikin shekarar 1976, wani kawuna ne, Usman dantatata da yake bukatar kudi, Naira dubu 18, kuma babu wanda zai ba shi a Kano. Ina da kudin, don haka na rnta masa, sai ya ce in je Legas in karbi kudin.Da isata Legas Usman ya ba ni Suminti, maimakon kudi, amma da na sayar da shi ba uwar kudin kawai na samu ba, har ma da ribar dubu shida. Da wuya mutum ya samu irin wannan gwaggwabar riba a Arewa, a wancan zamanin. Domin a lokacin ana sayar da Marsandi kirar 600 kan kudi N aira dubu 70. Sai na ce, ashe haka mutane ke samun kudi a nan wurin!”
Daga nan kowa zai iya hasashen abin da dangote.  Ssai kawai dangote ya koma Ikko (Legas) da zama “Da farko, Usman dantata ya ba ni suminti cike da motoci biyu, amma saboda cunkuson da aka samu a tashar jirage ruwa, kuma masu kwangilar gine-gine suna biyan kudin su tun kafin a sauke kayan. A watanni biyun farko na fara samun ribar Naira dubu biyu da 500 a kowace rana, har ma da ranakun hutun karshen mako. Sai ma na daina amfani da kudi. Domin jarin da taho da shi Naira dubu 50 ne, sannan na ranto Naira dubu 50 daga kakana. Sai ya kasance na mallaki abin da ya fi karfin bukatata don tafiyar da wannan kasuwancin. A wasu lokutan mutane na biyan kudin sumintin na tsawon wata uku kafin isowarsa,” a cewarsa.
Ayyukan gine-gine da suka rika bunkasa, suka sanya harkar shigo da suminti ta kara habaka, tashar jiragen ruwa ta kara cunkushewa, har t akai ga harkar hada-hadar suminti da durkushe a shekarar 1978. Aliko ya ce daga nan sai ya sauya akalar kasuwanci shigo da kayayyaki, al’amarin da ya hada da kayan gyara mota da motoci da kayan daukar kida da shinkafa da man girki da fulawa. Kai har ma da kusan komai da ake iya sayarwa. A lokacin shi kadai yake harkarsa, amma daga bisani sai kanensa Sani ya shigo harkar kasuwanci lokacin da ya gama makaranta.
dangote ya karyata labarin da aka rika yayatawa, cewa, ya samu dimbin arzikinsa ne a lokacin mulkin Shagari, sa’adda aka bayar da lasisin shigo da kayayyaki da kuma hada-hadar canjin kudi. Ya ce samun lasisin shigo da kayayyakin ya kawo wa harkar kasuwancinsa cikas, saboda ya sha wahalar samunsa, inda ya biya kudin kamasho mai yawa ga msu kai kawo a tsakani. “Ban karyata cewa, na samu dimbin kudi ba, a lokacin siyasa; ba kuma ina nufin cewa, gwamnatin shagari ba ta tallafa mini ba. Tabbas a kasashe masu tasowa, amma a lokacin siyasa ba lallai ne mu iya samun wani abu mai tsoka ba, domin cikas din mu na tattare da karancin shekaru, saboda akwai wadanda ke ganin cewa, matukar shekarunka ba su kai 40 zuwa 50 ba, bai kamata ka samu kudi ba.
dangote ya ce, bai  shiga cikin harkokin ’yan siyasar jamhuriya ta biyu  da yawa ba. Don haka bai samu matsala da Gwamnatin mulkin soja ta Buhari da Idiagbon ba, musamman lokacin da suke kokarin kama ’yan kasuwar da aka hada kai da wasu wajen aikata cin hanci da rashawa. Y ace yana aikin hajji lokacin da Buhario ya yi juyin mulki, amma sai ya dawo gida, kuma ba a kama shi ba, ballanta gwamnati ta dakatar da wasu harkokin kasuwancinsa. Duk da cewa bai samu matsinlamba ba a lokacin da Gwamnati Buhari ke kokarin gyaran tarbiyya, ba zai iya boye cewa, tsarin gwamnati na yi wa tattalin arziki garambawul (SAP) ta yi masa alfanu ba.
“Tsarin gwamnati na yi wa tattalin arziki garambawul (SAP) ya yi aiki ba tare da sakin hajar sayarwa a kasuwa ta nema wa kanta kimar daraja a kasuwa (deregulation) ba, tunda mutane irina ba su taba tunanin mallakar banki ba. Ya kasance shugaban bankin kasuwanci na Liberty (Liberty Merchant Bank). Babu wani wuri a fadin duniya da ake samun dama irin Najeriya,” inji shi.
Wannan makala an taba bugata a mujallar Citizen, ta ranar 17 ga watan Yunin 1991.