✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na shafe kwana 16 a hannun wadansu mutane a daji – Dalibi

Muhammad  Abubakar Kabir shi ne dalibin Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna a fannin kwanfuta da ya bace kwana 16 da suka gabata a kan…

Muhammad  Abubakar Kabir shi ne dalibin Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna a fannin kwanfuta da ya bace kwana 16 da suka gabata a kan hanyarsa ta zuwa makaranta. Aminiya ta zanta da shi bayan iyayensa sun aika da Naira dubu 20 kudin mota ga mutanen da suka rike shi da suka ce wai tsintarsa suka yi a daji:

Yaya aka yi aka sace ka, ko ka bace mako biyu da suka wuce?

Abin da zan iya tunawa shi ne na baro gida da misalin karfe 6:30 na safe da nufin zuwa makaranta. Na hau Keke NAPEP daga kofar gidanmu zuwa Bakin Ruwa, na biya su kudinsu bayan na tsallaka na sake shigar wani Keken da zai kai ni hanyar Unguwar Sanusi. Tun daga nan ba sake sanin inda nake ba.

Da ka shiga Keke NAPEP din akwai mutane ne a ciki?

Eh, akwai mutum uku a ciki har da mai tuka keken. Kuma tun da na hau ne ban sake sanin inda nake ba. Domin ko makarantar ban isa ba.

To, daga nan sai ina kuma?

Tashi kawai na yi na gan ni a cikin daji a wani gida mai daki uku. Na tambaye su me na zo yi nan suka fada min wai tsintata suka yi cikin daji. Suka ce min ko akwai lambar waya da zan iya bayarwa domin su kira gidanmu, na ce, eh. Sai na ba su lambar wayar babanmu suka kira shi, suka yi masa bayani.

Kwana nawa ka yi a hannunsu?

Na kwashe kwana 16 da bacewa amma sun ce min wai mako daya na yi.

Suna ba ka abinci?

Eh, suna ba ni abinci ba tare da wata matsala ba kuma babu cin zarafi ko duka.

Akwai matansu ne a cikin gidan da aka ajiye ka?

Eh akwai mata sai dai babu yara kuma su mazan ba zu cika zama a gida ba.

Mazan na rike ne da makamai:

Eh, na ga bindigogi biyu a cikin dakin da nake. Amma bayan nan ban ga kowa a gidan ba, wanda aka tsare.

Kuma ba su bukaci a ba su kudin fansa ba?

Ni dai ba su tambaye ni kudi ba kuma kamar yadda na ce ne ba su buge ni ba kuma suna ba ni abinci.

Yaya aka yi suka dawo da kai gida?

Sun kira babanmu ne suka fada masa cewa sun taimake ni. Don haka za su dawo da ni gida. Aka tura musu da Naira dubu 20 kudin mota. Bayan mun fito daga dajin har mun shiga mota a tasha ana cikin tafiya sai aka kira su a waya sai suka ce a tsaya su za su sauka. Sai suka karbi lambar wayar direban suka ce ya kai ni Kaduna. Shi direban ne ya kawo ni Kawo.

A wani gari suka sauka?

Gaskiya ban san garin da suka sauka ba, amma dai an yi tafiya mai nisa kafin su sauka.

Kai a tunaninka sace ka suka yi?

Yadda dai na ga suna kulawa da ni ban yi tunanin su suka sace ni ba domin har kaya suka saka min a cikin jaka iri biyu da takalmi kafin in tafi. Sun ce wai tsintata suka yi amma dai ba su fada min inda suka tsince ni ba.

Wadanne irin mutane ne kuma suna rufe fuskokinsu ne?

A’a, ba sa rufe fuska sannan kuma ni ba su yi min kama da Fulani ba.

To, yanzu yaya ka ji bayan ka dawo gida?

Gaskiya na ji dadin dawowata gida sai dai idan na ji ana labarin mutanen hankalina tashi yake yi.

Saboda me?

Haka kawai sai inji zuciyata na bugawa saboda tsoro.