Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a karo na farko ya bayyana halin da ya tsinci kansa yayin da yake jinyar cutar coronavirus a cibiyar killace wadanda suka kamu.
El-Rufai, wanda aka gano yana dauke da cutar a ranar 28 ga watan Maris, ya zama mutum na farko da aka tabbatar yana dauke da ita a jihar ta Kaduna – inda aka killace shi na tsawon kwana 26 kafin daga bisani ya murmure aka kuma sallame shi daga cibi yar – bayan an yi masa gwajin da ya nuna ya warke.
Gwamnan, wanda ya yi wata ganawa ta kai-tsaye cikin harshen Hausa da wasu zababbun gidajen rediyo a Kaduna ranar Talata da maraice, ya ce ya sha fama da ciwon kai mai tsanani tare da zazzabi a makon farko bayan killace shi.
Sai dai ya ce bai san takamaimai ko a ina ko kuma ranar da ya harbu da cutar ta coronavirus ba, amma yana tunanin kamar a Abuja ya kamu da ita – inda ya halarci taruka daban-daban.
El-Rufai ya kuma ce: “Na ji jiki sosai. An killace ni na tsawon kwana 26 ba tare da na hadu da matana da ‘ya’yana ba, kai in takaita maka zance ba na ganawa da kowa illa jami’an lafiya.
“Ba na iya ganin matana da ‘ya’yana, ina zaman kadaici har na tsawon kwana 26 cikin daki. Ko da mutumin da ke kawo mini abinci ma, yana sanye da kayan kariya sosai – wai saboda kar na harbe shi da cutar.
“Kullum ina ta shan magunguna, wani lokacin ma sau biyu a rana.”
Ya nunar da cewa bai ji wasu alamun tari ko kuma matsalolin numfashi ba; amma dai ya sha fama da matsanancin ciwon kai da kuma zazzabi – wanda a cewarsa ko makiyinsa ba zai masa fatan ya gamu da irin shi ba.
Gwamnan ya ce babu wani daga iyalinsa na kusa da ya harbu da cutar, amma ya harba wa wani abokin aiki da direbansa da wani hadiminsa da kuma wani abokinsa na kusa.
Ya ci gaba cewa, “Na yi fama da mura kafin a yi mini gwajin. Sai dai na sha magani na kuma ji saukin murar, in ban da ciwon kan da yaki tafiya.
“Ko a lokacin da na yi gwajin ma, mataimakiyar gwamna Dokta Hadiza Balarabe ta duba ni inda ta ce akwai gajiya tattare da ni kuma ina bukatar samun hutu, sai ta rubuta mini wasu magunguna, kwana guda bayan nan na samu sauki, illa iyaka dai ciwon kan nan…”
Ya ce ya samu sararawa a kwana biyun farko da ya yi a killace, amma a kwana na uku sai ya fara jin zazzabi mai zafin gaske na kwana biyu zuwa uku wanda ya sa ba ya iya karatu ko yin komai har ta kai ga da kyar yake yin sallah ma.
“Bayan makon farko, na samu sauki inda na fara karanta duk wani bayani a kan cutar coronavirus ta intanet, har na kusan zama wani kwararre a fagen… sa’annan na yi amfani da lokacina wajen yin addu’o’i ina karatun Al-Kur’ani; sannan daga bisani na fara halartar tarukan da mataimakiyar gwamna ke jagoranta”, inji shi.
El-Rufai ya ce akwai lokutan da likitoci suka kwace wayoyinsa, wanda ya yi zargin matansa ne suka kitsa hakan, “inda suka hada baki da mataimakiyar gwamna domin ganin na daina amsa waya, sai dai kawai ina karatu daga iPad dina”.
Da yake magana a kan dalilinsa na aske gemun da ya tara yayin da yake killace, gwamnan ya ce an tilasta masa da ya yi hakan bayan ya samu umurni daga mahaifiyarsa.
“Ta tambaye ni ko me ya sa nake saka takunkumin fuska, ganin cewa ba na dauke da cutar?
“Hakan ya faru ne saboda ba a sanar da ita cewa na kamu da coronavirus ba, kawai an sanar da ita ba ni da lafiya ne, to a lokacin ne na gaya mata cewa na kamu da cutar kuma har na warke,” inji shi.
Gwamnan ya ce yayin da yake biyayya ga umurnin mahaifiyarsa na ya cire takunkumin, “a lokacin ne ta fahimci ina da gemun inda ta tambaya cewa: ‘Mene ne wannan?’
“Sa’annan ne na fada mata cewa ban yi aski ba har na tsawon wata guda inda nan da nan ta umurce ni da in gaggauta aske shi, ta kuma tunatar mini cewa mahaifina bai taba ajiye gemu ba har ya koma ga mahallici kuma idan har wana shi ma ba ya ajiye gemu, to me zai sa in ajiye?”
Sai dai ya nunar da cewa ya fara jin dadin ajiye gemun kuma ya so ya dore da hakan, amma lallai ne ya yi biyayya ga umurnin mahaifiyarsa domin ya zauna lafiya da ita.
A karshe ya bukaci jama’ar jihar Kaduna da su kara hakuri game da irin matakan da gwamnatinsa take dauka yana mai cewa kasancewarsa wanda ya yi fama da cutar coronavirus kuma ya warke, nauyi ya rataya a wuyansa da ya tabbatar da kiyaye lafiyar jama’ar jihar.