Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana irin rawar da ya taka wajen ganin an saki tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo daga kurkuku a 1998.
Obasanjo na daga cikin shugabannin da gwamnatin Janar Sani Abacha ta garkame a gidan yari bisa zargin hannunsu a yunkurin yi masa juyin mulki.
- Sojoji sun yi raga-gara da mayakan ISWAP a Dajin Kainji
- Waiwaye: Yadda Rufe Hanyoyin Sadarwa Ya Shafi Harkokin Kasuwanci
Bayan mutuwar Janar Abacha a 1998, Abdulsalami ya karbi ragamar mulkin kasa tare da sakin wasu fursunoni ciki har da Obasanjo.
A wata hira ta musamman da ya yi da TRUST TV, Abdulsalam ya bayyana yadda aka canja tunanin Obasanjo tare da wasu fursunoni.
“Mun saki Obasanjo da sauran fursunoni kuma muka yi musu afuwa. Don haka, da aka saki Obasanjo ya zo ya same ni, ya ce zai kai gwamnati kotu.
“Na tambaye shi, me ya sa za ka yi haka? Ya ce sojoji sun durkusar da kasuwancinsa, an tauye masa hakkinsa, bai yi juyin mulki ba, amma an kama shi an daure.
“Na ce masa yallabai, don Allah a bar wannan magana, na gode wa Allah da kake a raye, ka manta da wadannan abubuwan. Wasu batutuwan da ka ambata, a cikin ikona zan duba hakan, don haka muka bar shi a haka”.
Da aka tambaye shi ko me yake nufi da sauya tunanin Obasanjo a gidan yari, Abdulsalami ya ce, “Tabbas ba shi kadai ba, duk mutanen da aka daure ta wata hanya, mun yi kokarin gyara su; domin taimaka musu.”