✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na kera KEKE-NAPEP mai amfani da lantarki – Okafor

Aminiya ta zanta da wani matashi mai suna Ifeanyi Nnamdi Okafor, dan garin Achalla Umuchi da ke Karamar Hukumar Aguata, jihar Abiya, wanda ya kammala…

Aminiya ta zanta da wani matashi mai suna Ifeanyi Nnamdi Okafor, dan garin Achalla Umuchi da ke Karamar Hukumar Aguata, jihar Abiya, wanda ya kammala karatun digiri a Jami’ar Najeriya da ke Nsukka, inda ya bayyana yadda ya kera KEKE-NAPEP mai amfani da lantarki mai mamakon man fetur.

 

Me ya ja hankalinka har ka kera KEKE-NAPEP mai amfani da lantarki?

Wannan KEKE-NAPEP din da kake gani ba ya fitar da hayaki. Na fara tunanin ne tun ina karamin yaro. Na kasance ina hada motar kwali. Sai in yi amfani da na’urar da ke kai lantarki cikin fanka har ya bayar da iska wato kwayel in sanya a motar kwalin in ga yadda zai juya tayar motar.

Bayan zaben 2015, an samu matsalar rashin man fetur. Ina da KEKE-NAPEP da ake min aiki da su, amma sai matsalar mai ya kawo mana matsala. Daga nan sai na fara tunanin yadda zan magance matsalar. Sai na tuna yadda nake hada motar kwali ina yaro. Sai na ce idan na gwada a KEKE-NAPEP, zan iya samun sa’a. Dagan an sai na shiga bincike.

Da na hada na farko sai bai yi ba. Na sake gwada na biyu, shi ma bai yi ba, sai gwiwata ta yi sanyi. Amma kuma daga baya sai na sake gwadawa a karo na uku, a nan ne aka dace.

Ya ka ji bayan ka kammala aikin?

Bayan na kammala, sai na gwada tuka KEKEn a cikin garin Aba. Da na ga abu ya yi, na yi matukar murna da farin ciki, wanda hakan ya sa na fara shiri a kan na biyu.

Mene ne matsalolin da ka fuskanta?

Matsalar kawai ita ce rashin kudi. Ba ni da isasshen kudi, sannan kuma in bukatar baban fili, wanda rashinsa ya sa ban fara aiki a kan bas ba. Don haka ne ma nake bukatar tallafi.

Yaya kake samun kayan aiki?

Yawancin kayan aikin a nan cikin gida nake samu. Kashi 90 na kayan aikin a kasuwar Aba nake samu, kamar fanka da sauransu. Runfar ma duka a Aba ake hadawa. Wasu abubuwan kuma da kaina nake hadawa. Taya ce kawai nake sayowa wanda daga waje ne. Sannan kuma za a iya yin amfani da batirin mota.

Me kake tunanin wannan KEKE-NAPEP din zai jawo wa Najeriya?

Idan ka dubi bangaren muhalli, wannan KEKE-NAPEP din zai tsabtace muhalli domin ba ya fitar da iskar sinadarin carbon monodide da ke fita daga hayakin mota da babur, wanda kuma yana da illa ga muhalli da lafiya. Yanzu duniyar ma abin da ake magana ke nan, wato koriyar takanga; magance matsalar gurbacewar muhalli. Na biyu kuma zai rage tsadar kudin tafiya domin babu maganar sayan man fetur, ko canja man inji. Kawai sai dai ka rika caja batirin. Sannan batirin zai iya yin aikin kwana biyu ko kuma tafiyar kilomita 120 kafin ya yi sanyi. Sannan akwai na’urar samar da lantarki daga hasken rana wato solar panel. Da wannan batirin zai rika yin caji da kanshi idan kana tafiya. Sannan kuma ina kokarin samar da wajen caji na kudi kamar gidan mai inda za a rika yi wa KEKE-NAPEP caji a kasa da minti 15. Yanzu haka mun kera KEKE-NAPEP guda uku, kuma muna da daftarin shirin kera motar bas mai amfani da lantarki.