✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mutum miliyan 22 za a zabi sabon Shugaban Kasar Kenya

Zaben zai yi zafi tsakanin mataimikin shugaban kasa William Ruto da madugun adawa, Raila Odinga

Al’ummar kasar Kenya sun fara bin layin kada kuri’ar zaben shugaban kasar karo na biyar, domin jagorantar su a shekaru biyar masu zuwa.

Masu zabe miliyan 22.1 ne za su kada kuri’a a ranar Talata domin zaben shugaban kasar da gwamnonin kananan hukumomi da ’yan majalisar dokoki da sauran mukamai.

Zaben zai gudana ne daga karfe shida na safe zuwa karfe biyar na yamma kuma za a bukaci kowane mai kada kuri’a ya mallaki katin shaida ko fasfo da jami’an hukumar zabe mai zaman kanta (IEBC) za su yi amfani da su domin tantance shi.

Har ila yau, za a yi amfani da na’urorin KIEMS guda 55,100 da aka rarraba a fadin kasar domin tantance hoton fuska da kuma zanen yatsun masu kada kuri’a wajen tantance bayanan jama’a don fara kada kuri’unsu.

’Yan takara hudu ne ke fafatawa domin maye gurbin Shugaba Uhuru Kenyatta wanda ya kare wa’adinsa biyu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade.

Wadanda ke kan gaba a zaben sun hada da tsohon madugun adawa Raila Odinga mai shekara 77 da mataimakin shugaban kasa William Ruto mai shekara 55.

Manazarta sun yi hasashen cewa za a iya yin kam-kan-kan tsakanin manyan ’yan takarar wanda kuma zai iya sawa a yi zagaye na biyu a karon farko a tarihin zaben kasar.

Za a sanar da sakamakon zaben a hukumance cikin mako guda da kada kuri’a.

Domin samun nasara kai tsaye, dole dan takara ya samu sama da kashi 50 cikin 100 na dukkan kuri’u da kuma akalla rubu’in kuri’un da aka kada a fiye da rabin kananan hukumomi 47 da ke kasar ta Kenya.

Sai dai kuma za a gudanar da zagaye na biyu domin fidda gwani a cikin kwanaki 30 idan babu daya daga cikin ’yan takarar da ya yi nasara kai tsaye.