Mai daukar hoton fitaccen mawakin Kudancin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, mai suna Fortunate Ateumunname Peter, ya rasu.
Fortune mai shekara 24 fitaccen mai daukar hoto ne kuma yana cikin na hannun damar mawakin.
Mamacin ya rasu ne bayan ruwa ya ci shi a lokacin da yake kokarin daukar hoto a wani wajen daukar hoto a Jihar Legas da ba a tantance ba har lokacin hada wannan labari.
Rasuwar Fortune ta zo ne kimanin wata uku bayan rasuwar wani na hannun damar Davido, mai suna Habeeb Ademola Uthman, wanda aka fi sani da Obama DMW, a sakamakon ciwon zuciya.
A watan Disamban bara, dogarin mawakin mai suna Ogbeide Tijani Olamilekan, wanda aka fi sani da Teejay ya rasu bayan fama da jiyan.
Davido ya kadu matuka da rasuwar Teejay, inda ya rubuta a shafinsa cewa, “Ku ce mi mafarki nake yi. Tj dina ya rasu? Me zan iya yi ba tare da Tj ba; Shekara 11 kana dawainiya da ni, ka sa ni a gaban komai,” inji shi.
Sannan ya kara da yadda Tj ya taimaka masa wajen karfafa masa gwiwa domin gudanar da wasu abubuwa da suka dace.
– Abokansa uku sun mutu a mako daya
A ranar 3 ga Oktoban shekarar 2017, a ranar bikin zagoyowar ranar haihuwar abokin mawakin mai suna Tagbo Umeike, sun je Shisha Lounge da ke Lekki a Jihar Legas tare da DJ Olu da Chime Amechina da shi Davido din.
A daren ne aka ce sun yi gasar shaye-shaye, wanda da wayewar gari aka samu labarin rasuwar Tagbo.
A lokacin, budurwar Tagbo mai suna Caroline Danjuma ta bukaci ’yan sanda sun bincika yanayin yadda saurayinta ya rasu.
Ana cikin jimamin rasuwar Tagbo ne sai aka samu labarin rasuwar DJ Olu da Chime.
An tsinci gawarsu ne a cikin motar DJ Olu a ranar 8 ga Oktoban shekarar, kwana hudu bayan rasuwar abokinsu Tagbo.
Sau biyu a lokacin ’yan sanda na gayyatar Davido domin amsa tambayoyi, sannan daga baya suka tabbatar da cewa Tagbo ya mutu a sanadiyar rashin iska (suffocation).
Sai dai an yi ta kai-komo a lokacin tsakanin ’yan sanda da lauyoyi da sauransu, inda a karshe lauyan Davido, Bobo Ajudua ya ce ’yan sanda sun kammala bincikensu kuma sun wanke Davido daga zarge-zargen da ake masa.