Daurruwan Musulumi da Kiristoci ne suka gudanar da addu’o’in rokon ruwan sama a Karamar Hukumar Shendam da ke Jihar Filato.
Rashin ruwan sama na tsawon makonni ya sa Musulmi da Kirsitoci sun yi tururuwar gudanar da addu’o’in ne sakamakon yadda amfanin gonakinsu ke bushewa saboda karancin ruwan.
Musulmi sun gudanar da Sallar Rokon Ruwa da addu’o’i ne a filin idi, a yayin da Kirsitoci suka yi nasu addu’o’in a coci-coci sakamakon rashin ruwan na tsawon makonni.
A halin da ake ciki, amfanin gona irin su masara, gero, doya da sauransu sai bushewa suke yi a yankin, wanda hakan ya sa manoma da sauran al’umma komawa ga Allah.
- Kisan masu zanga-zanga: A hukunta jami’an tsaro —HURIWA
- Yanzu-Yanzu: An janye dokar hana fita a Kaduna da Zariya
Limanan da suka jarogranci ibadar rokon ruwan sun gabatar da huduba tare da kira ga jama’a da su koma ga Allah su tuba daga zunuban da suke aikatawa.
Sun kara da cewa aikata sabo da na daga cikin dalilan da ke sa daukewar ruwan sama, don haka jama’a su tuba ga Allah.
Babban Limamin Babban Masallacin Yelwa, Abdulkareem Salihu, ya jaddada muhimmancin jin tsoron Allah, wanda ya bayyana a matsayin daya daga cikin sabubban amsa addu’a da samun biyan bukata.
Malamin ya ci gaba da cewa laifukan da ake aikaitawa na iya zama dalilin da Allah Ya dauke wa al’ummar yankin ruwan sama.
Shi ma Fasto Isaac Luka na Cocin RCC da ke yankin Lakichi, ya bayyana cewa saba alkawari, zubar da ciki da kisan ba gaira babu dalili suna daga cikn manyan laifukan da ake aikatawa a yanzu, “shi ya sa muka samu matsala da Mahallicinmu, wanda hakan shi ne dalilin da ya haddasa mana rashin ruwan sama.“