Wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na Jihar Zamfara sun ce sun koma cin ciyawa saboda tsananin yunwa lokacin da masu garkuwa da su suka gudu suka barsu babu abinci.
Daya daga cikinsu, mai suna Iklima Murtala, ta kuma yi ikirarin cewa mutum 17 daga cikinsu ma tuni suka mutu saboda azabar yunwa.
- Kotu ta tsare dan Shahrukh Khan kan miyagun kwayoyi
- Yanzu garau nake, inji Tinubu bayan jinyar wata uku a Birtaniya
Lokacin da yake karbar mutanen a madadin gwamnati, Sakataren Gwamnatin Jihar ta Zamfara, Alhaji Kabiru Balarabe ya ce gwamnati zata ci gaba da matsa lamba ga ’yan bindigar har sai ta ga bayansu.
Shi kuwa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Ayuba Elkanah, ya ce tsananin rashin abinci ya sa ’yan bindigar sun kasa yin sakat a Jihar.
Lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya, Kakakin Gwamnan Jihar, Zailani Bappah, wanda ya tabbatar da ceto mutum 185 daga hannun masu garkuwar ya kuma ce gwamnatin Jihar ta dauki nauyin kula da su a asibiti.
Ya ce, “Mutanen da muka kubutar sun kai 185. Abin da muke fara yi a duk lokacin da muka kubutar da mutane daga hannun ’yan bindiga shi ne mu kai su asibiti don a duba lafiyarsu, don tabbatar da ko sun kamu da wata cuta.
“Duk wanda aka gano ba shi da lafiya, gwamnati kan dauki nauyinsa a asibita, har sai ya warke.
“Sannan mukan basu abinci yadda ya kamata lokacin da suke asibitin. Bayan sun warke kuma, a kan yi musu gwajin kwakwalwa saboda yanayin da suka shiga a hannun masu garkuwar da su, in sun warke kuma mu damka su ga iyalansu,” inji Kakakin Gwamnan.