Rahotannin da ke fitowa daga kananan hukumomin Isa da Sabon Birni da Gwaronyo da wani yanki na Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara na nuna sojoji suna ci gaba fattatakar ’yan bindigar da suka addabi yankunan, inda aka kashe da dama daga cikinsu aka jikkata wadansu, sannan wadansu suka tsere.
Haka Aminiya ta samu rahoton cewa kasurgumin dan bindigar nan, Bello Turji ya rubuta wata wasika inda yake naman a yi sulhu a daina kashekashen.
Sai dai wadansu mutanen yankin sun ce duk da suna da labarin harin da ake kai wa ’yan bindigar, har yanzu su ma suna kai hare-haren.
Wata majiya ta ce a ranar Lahadi ma mahara sun shiga garin Gaje, inda mutanen garin suka watse.
Ta ce a Isa har abin da ya kai Bafarawa ba a kai ga ’yan bindigar ba, jagororinsu irin su Dan Bokolo, babu wani sahihin labari kan kashe su.
Amma da aka samu labarin sojojin, mutanen Gatawa da Tara sun fara komawa garuruwansu.
‘Ana samun nasara’
Bashir Altine Guyawa Isa ya ce sojoji sun shiga yankin Kamarawa da Tozai da Surudubu da gefen Take Tsaba.
Ya ce a yankin akwai abubuwa na karfafa gwiwa duk da babu tabbacin kama daya daga cikin jagororin ’yan bindigar.
“Fada ake yi, ba a tsammanin a samu nasarar da mutane suke bukata cikin kankanin lokaci, amma mu da lamarin ya shafa kaitsaye muna da hujjojin sojoji sun shiga yankin.
“Misali in ka bar garin Sakkwato ka je Kwanar Maharba zuwa ’Yar Rimawa da Makuwana da Gatawa zuwa Karamar Hukumar Isa da Lambun Malam Sule da Dan Dabi wato iyakar Isa da Shinkafi, ka bi ta Shinkafi daga Sabon Birni tun daga Gidan Bawa har Teke da Maikasuwa da Mai Fuloti zuwa Rijiyar Malam Ladan dukkan wadannan kauyukkan wurare ne da ’yan bindigar suke cin zarafin al’umma, amma tunda sojoji suka shiga dajin gabashin Sakkwato ba a sake cin zarafin jama’a ba.
“Wannan ne ma’auninmu na sojoji suna cikin yankin, muna fata sojojin su ci gaba da zama a dajin,” inji shi.
‘Turji da dabarsa suna nan a kauyen Fakai’
Wani tsohon Shugaban Karamar Hukumar Sabon Birni Alhaji Idris Muhammad Gobir ya ce, “Muna godiya kan kai mana sojoji a yankin, da fatar a samu nasara a kan ’yan bindigar, amma magana ta gaskiya ba a sare gwiwa ba.
“Ka kalli abin da ake ta yayatawa kan lamarin, abin da suke yi a Sabon Birni ban gamsu ba saboda ba wani abu da ya sauya.
“Ana maganar sojoji sun shiga daji, amma maharan sun sace mutane an biya kudin fansa Naira miliyan 8.
“Sun shiga garin Gyangyadi a Isa sun yi wa wata mace fyade suka kashe ta sun kuma yi garkuwa da wadansu mutum hudu.”
Ya ce ya kamata kafin Gwamna ya nuna gamsuwarsa ya yi bincike a kai.
“A ranar Litinin mutanen Unguwar Lalle da Dan Tudu a tsaye suka kwana don maharan sun shiga.
“Kauyukkan Burkusuma da Dama da Gidan Gyara da Makwaruwa da Sha-dawa ba a zo garin da yaki ba, kuma akwai dabobin barayi a wuraren.
“Dabar Turji da ke Fakai bai taba barin wajen ko ya matsa ba.
A ranar Litinin sai da Dan Kwaro (daya daga cikin kwamadojinsa) ya shiga garin Satiru sannan ya koma daji,” inji Gobir.
Mun yaba kokarin sojoji — Gwamna Tambuwal
Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yaba kokarin sojojin kan fatattakar ’yan bindigar da suke yi.
A wani bayani da aka fitar wanda shi da kansa ya sanya wa hannu, Gwamna Tambuwal ya ce a madadin gwamnati da jama’ar Sakkwato suna jinjina wa jami’an tsaro kan nasarar da suke samu.
Ya ce shi da mutanen jihar suna tare da jami’an tsaron tare da yi musu addu’ar samun nasara daga Allah inda ya ba su tabbacin samun goyon baya har zuwa lokacin da za a samu zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
Har lokacin hada wannan rahoto, Rundunar Soji a yankin ba ta ce komai ba.