✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka gano gawar danmu da aka yi garkuwa da shi

Al’ummar Rafin Guza a karamar Hukumar Kaduna ta Arewa sun tsinci kansu cikin tashin hankali da kaduwa a sakamakon samun gawar wani yaro dan shekara…

Marigayi Amar Baba AliAl’ummar Rafin Guza a karamar Hukumar Kaduna ta Arewa sun tsinci kansu cikin tashin hankali da kaduwa a sakamakon samun gawar wani yaro dan shekara bakwai da mai suna Amar Baba Ali da aka yi wanda ake zargin dan kanin mahaifinsa ne ya sace shi daga bisani ya halaka shi.

An sace Amar ne a gidan mahaifinsa a ranar 2 ga wata Nuwamban wannan shekarar. Aminiya ta gano cewa lokacin da aka gano gawar Amar binne a cikin yashi a kusa da kogin Kaduna har ta fara rubewa.
‘Yan Sanda ne suka tuno gawarsa bayan kama wani mai suna Abba, wanda dan kanin mahaifinsa ne. Bayanai sun nuna cewa a lokacin da aka ciro gawar yaron daga inda suka binne shi an ga hannayensa biyu daure a bayansa, sannan an cika bakinsa da ledoji.
Aminiya ta gano cewa, wadanda suka sace shi sai da suka bukaci mahaifinsa da ya biya su naira dubu hamsin, amma kuma daga baya sai suka ce sun kara kudin zuwa naira miliyan daya da rabi. Da mahaifin yaron ya fada musu cewa ba shi da wannan kudi sai suka ce sun rage zuwa naira miliyan daya. Da bai biyasu ba ne sai suka kashe yaron.
Mahaifin marigayin, Alhaji Baba Ali wanda yake sana’ar sayar da motoci a Unguwar Shanu Kaduna, ya bayyana wa Aminiya yadda abin ya faru, inda ya nuna cewa, yaron dan uwansa mai suna Abba ne ya je gidansa ya sace yaron suka kai shi wani kango suka boye shi suka ce sai an biya kudi kafin su sako shi.
Ya ce,” Ranar Asabar ne 1 ga watan Nuwamba suka sace shi a gidana, a lokacin mahaifiyarsa ta yi tafiya zuwa Kano, ni kuma na tafi wajen sana’ata da ke Unguwar Shanu. Na bar yarana su biyar a cikin gida suna wasa, amma da na koma gida da rana sai babbarsu Mama ta fada min cewa Abba sun fita da Amar kuma ba su dawo ba. Ta fadamin cewa, Abba ya je gidan ne tare da wani abokinsa wanda ya bari a kofar gida. Har ta ce wai Abban bayan ya ci abinci sai ya cigaba da wasa da yaran daga baya sai abokin Abban da ke waje ya aiko a kirawo shi amma sai Abban ya ki fita, sai ya aika masa da wayarsa ta hannu cewa zai nemi shi. Daga nan sai ya ce Amar ya raka shi waje kuma tun da suka fita ne ba su dawo ba,” inji shi.
Mahaifin yaron ya kara da cewa, shi da farko bai yi zargin komai ba, domin yana ganin Abba zai dawo da shi gida, saboda haka sai ya koma wajen sana’arsa, amma da ya dawo da yamma kimanin karfe biyar sai ya tarar yaron ba ya gida. Saboda haka sai ya umarci sauran yaran da su tafi makarantar islamiyya har sai ya dawo daga aiki.
“Bayan na koma gida da misalin karfe 9 na dare na tarar Amar bai dawo ba, sai na wuce gidan yayana, watau mahaifin Abba, na sanar da shi abin da ke faruwa. Daga nan ne muka kira Abba aka tambaye shi ko ya san inda Amar yake, ya ce a’a shi bai sani ba. Tare da Abban muka yi ta yawo cikin dare muna neman yaron amma ba mu ganshi ba. Da safe sai muka sanar da ‘Yan sanda da sauran jami’an tsaro. Washegari ranar Lahadi da yamma sai wani ya kirawo lambar wayata ya ce Amar na hannunsu kuma sai na biya Naira dubu hamsin za a sako mana shi. Na amince zan biyasu ba tare da bata lokaci ba har na tambaye su wace hanya zan bi wajen tura musu kudin? Mutumin da ya kira ni sai ya ce zai sake kirana.’’ Mahaifin yaron
“Ranar litinin da ya kira sai ya ce sun kara kudin daga Naira dubu Hamsin zuwa Naira miliyan daya da rabi. Na fada musu cewa ba zan iya biyan wannan kudi ba, daga nan sai ya ce ban shirya ganin yarona ba, sai ya kashe wayarsa. Sun sake kiran wayata a ranar Talata suka ce sun sake rage kudin zuwa Naira miliyan daya, na sake fada musu cewa ba zan iya biya ba,” inji shi.
Mahaifin yaron ya cigaba da cewa, wadanda ake zargi sun cigaba da aika masa sakonni ta wayarsa watau tes, amma a ranar lahadin makon jiya sai daya daga cikin wadanda suka sace yaron ya kira shi inda ya bayyana masa cewa dansa ya rasu.
“ Bayan ya fada min sakon sai kuma ya ce idan ina da sha’awar sanin wadanda suka sace min yaro in karbi wayar hannun Abba in duba sakonninsa. Daga nan sai na wuce gidansu inda na karbi wayar hannun Abba na duba, abin mamaki kuma sai na ga dukkan sakonnin da aka aika min da wayarsa aka yi amfani,” inji shi.
Ya ce, yana ganin sakonni sai ya tambayi Abba ina ya kai Amar? Sai ya tabbatar masa da cewa shi ne ya sace shi. Daga nan sai suka sanar da ‘yan sanda, su kuma suka je suka kama shi. Daga nan sai Abba ya sanar da ‘yan sanda inda suka binne gawar Amar, aka je aka tuno shi domin yi masa sutura kamar yadda musulunci ya tanadar.
Wata majiya a ofishin ‘yan sanda ta bayyana wa Aminiya cewa, kila Amar ya rasu ne kwana daya kacal da sace shi, sannan suka binne shi washegari da misalin karfe biyu na rana a cikin wani yashi da ke kusa da kogin Kaduna.
Game da sanadin mutuwarsa kuwa, majiyar ta shaida mana cewa ana ganin kamar yunwa ce ta kashe shi ko kuma kila maciji ne ya sare shi a inda suka boye shi ko kuma wani abu mai guba ya cije shi. “Yana kuma iya rasuwa a sanadiyyar sanyi ko kuma sun buge shi da wani karfe, domin akwai jini a bakinsa lokacin da aka tono gawarsa,”inji majiyar
Haka kuma wata majiya ta shaidawa Aminiya cewa, matasan da ake zargi sun yi niyyar sayen mota ce kirar Honda Cibic da kudin da suke neman a biya su.
Kangon da aka yi garkuwa da yaron kafin a kashe shiDa Aminiya ta nemi jin ta bakin mahaifin Abba wanda shi ne ake zargi da aikata wannan aika-akan, mai suna Malam Aliyu, ya tabbatar da cewa ‘yan sanda sun kama dansa Abba bayan ya amince da aikata wannan laifin. “ Na dade ina rokonsa da ya kaurace wa abokanen banza amma ya ki ji,” inji shi.
Mai Unguwar Rafin Guza, Malam Ya’u, ya ce wannan shi ne karo an farko da suka taba samun irin wannan laifi a yankin. Ya kuma bayyana cewa, dukkan al’ummar yankin na cikin damuwa da kaduwa saboda abin da ya faru da wannan yaro.
Ya ci gaba da cewa, duk abin da ya faru ba shi da labari sai da aka je tono gawar Amar, wanda hakan ya sanya ya zama dole masu unguwannin yankin su zauna domin su gano yadda za a magance aukuwar irin lamarin nan gaba.
Kwamishinan ‘Yan sandan Jahar Kaduna Olufemi Adenaike ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce rundunarsa ta yi nasarar cdanafke wasu daga cikin wadanda ake zargi, a yayin da suke cigaba da neman sauran.Wurin da aka rufe yaron bayan an kashe shi