✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mayaƙan Hamas suka shafe sa’a 6 suna kai hari a Isra’ila

- Wasu daga cikin kayan hangen nesa ko dai ba su aiki ko kuma maharan Hamas sun lalata su cikin sauki.

Shekara ɗaya kenan da kai harin ranar 7 ga watan Oktoban 202 da mayakan Hamas suka kai Isra’ila, kuma har yanzu akwai tambayoyi game da yadda mummunan harin ya shammaci sojojin kasar.

Kafar labaran BBC ta ji labaran abin da ya faru da wasu iyalai a wani sansanin soja da ke gadin iyakar kasar da Zirin Gaza.

Mayakan Hamas sun fatattaki sansanin Nahak Oz a safiyar 7 ga watan Oktoba, kuma an samu rahoton cewa an kashe sojoji fiye da 60 tare da yin garkuwa da wasu.

Rundunar sojin Isra’ila ba ta wallafa sakamakon bincikenta kan abin da ya faru ba tukunna a ranar, amma ta sanar da iyalan mutanen da aka kashe a wurin, kuma wasu daga cikinsu sun bai wa BBC labarin abin da aka faɗa musu.

A yunkurin BBCn na kara zakulo abubuwan da suka faru, ta kuma yi magana da waɗanda suka tsira, tare da ganin wasiyyar waɗanda suka rasu, sannan ta jiyo sautin muryar waɗanda suka ga abin da ya faru a lokacin da yake faruwa, domin fayyace takamaiman abin da ya auku.

Ga abubuwan da BBC ta gano:

– Da yawa daga cikin sojoji sun lura da bakin ayyuka a sansanin kafin 7 ga watan Oktoba, ba kawai ‘yan matan da ke aikin sa idon kan kyamarorin tsaron kan iyaka ba.

– Sojoji sun lura mayakan Hamas sun dakatar da ayyukansu kacokan ‘yan kwanaki kafin harin.

– Da yawan sojojin Isra’ila da ke wurin ba su ɗauke da makamai kuma umarnin da ake ba su shi ne su ja baya idan aka kawo musu hari maimakon matsawa gaba.

– Wasu daga cikin kayan hangen nesa ko dai ba su aiki ko kuma maharan Hamas sun lalata su cikin sauki.

Bayanan sun jawo karin wasu tambayoyi game da matakan da suka haɗa da – me ya sa dakaru kalilan ne ke rike da makamai a sansanin da ke kusa da iyaka, me ya sa ba a ɗauki karin matakai ba bayan samun bayanan sirri, ta yaya aka ɗauki lokaci kafin dakarun kai ɗauki su karasa wurin, da kuma ko shi kansa tsarin ginin ba irin wanda zai ba su tsaro ba ne.

BBCn ta nuna wa rundunar sojin Isra’ila da ake kira Israel Defense Forces (IDF), wadda ta ce tana ta gudanar da “cikakken bincike game da

abubuwan da suka faru, ciki har da na sansanin Nahal Oz, da ma sauran.”

A ranar 7 ga watan Oktoba, Sharon – ba sunanta na gaskiya ba ne – ta fara aiki a Nahal Oz mai nisan kilomita ɗaya daga iyakar Gaza, da misalin karfe 04:00 na rana.

Tana cikin rukunin sojoji mata da ake kira Tatzpitaniyot a harshen Hibru, kuma aikinsu shi ne nazartar bidiyon da kyamarori suka ɗauka a kan iyaka.

IDF ta faɗa wa ‘yan’uwan mutanen da aka kashe a wurin cewa ranar da aka kai harin babu makamai a hannun ma’aikatan.

Janar Israel Ziɓ, tsohon shugaban sashen ayyuka na IDF, ya faɗa wa BBC cewa a lokacin da yake aiki, ba a taɓa samun wani lokaci da za a ce wani soja ba shi da makami ba a kan iyaka.

“Wannan shirme ne…Aikin soja shi ne makami,” in ji shi.

A baya BBC ta ta ba da rahoton cewa bataliyar Tatzpitaniyot ta lura da wasu bakin ayyuka a ɗaya ɓangaren na iyakar, amma yanzu ta gano cewa wasu sojojin ma daga wasu sansanonin sun lura da hakan.

“Komai ya tsaya cak kuma hakan ya fara tsorata mu,” kamar yadda wani sojan kai hari ya faɗa, wanda ke sansanin. “Kowa ya fahimce cewa akwai bakon abin da ke faruwa. Abin ba shi da ma’ana.”

Abin da ya sa IDF ta kasa gane abin da ke shirin faruwa shi ne kawai “tsantsar girman kai”, a cewar Janar Ziɓ, “tunanin cewa Hamas ba za su iya kawo hari ba, kuma ma ba su da karfin yin hakan”.

“Mun fara barci a ranar 6 ga wata da tunanin maguna ne a tsallake kawai sai muka farka muka ga sun zama damisa.”

Da misalin karfe 05:30 na asuba, dakarun barikin Golani sun fara shirin fita sintiri kamar yadda suka saba, sai shugabanninsu suka ba su umarnin jinkirtawa saboda ana zargin an harbo makami mai linzami, a cewar uku daga cikinsu.

“An ba da gargaɗi. Haramun ne mutum ya hau kan titin da zai kai shi katangar iyaka,” in ji ɗaya daga cikinsu.

Wani kuma mai shekara 21 Shimon Malka, ya ce wannan gargaɗin abin mamaki ne duk da cewa ba bakon abu ba ne, saboda haka sai ba su ba shi wani muhimmanci ba.

6:20

Zuwa karfe 06:20 na safiya, Hamas ta fara harba makaman roka amma Sharon ta ji kamar ba wani muhimmin abu ba ne, saboda ta taɓa ganin harin roka kuma sansaninsu na ba su kariya.

“Akasari minti biyar ake yi sai kuma a tsahirta,” in ji ta. Amma wannan karon babu sassauci.

6:30

Zuwa 06:30, Sharon ta ce sai ta fara ganin dakarun Hamas na kokarin karasowa. Sai Tatzpitaniyot suka faɗa wa dakarun kasa abin da ke faruwa.

“Mutum huɗu na nufowa katangar iyaka, ku lura,” kamar yadda ɗaya daga cikin matan ta sanar cikin rawar murya. “Ina iya ganin mutum biyu ɗauke da makamai, ku gane.”

Wannan katangar ta karfe, IDF da sauran Isra’ilawa na ganin ba za a iya tsallaka ta ko karya ta ba, amma duk da haka sojoji sun fara ba da rahoton an karya ta a daidai wannan lokaci.

Janar Ziɓ ya ce saurin da kuma karfin da mayakan Hamas suka nuna wajen karya shingen ya nuna gazawa wajen gina katangar da aka yi tunanin ba za a iya ɓalla ta ba.

“Kamar yadda kuka gani, motoci biyu kan zo su tunkuɗe ta. Ba wata aba ba ce. Da a ce akwai ko da ababen fashewa ne hakan zai dakatar da su na ‘yan awanni.”

Sharon ta tuna cewa ɗaya daga cikin kwamandojin barikin da kayan barci ta karaso wurin bayan dakarun kai hari sun karaso wurin.

Wata balambalan ta leken asiri a Nahal Oz da ta fi leko Gaza na aiki ba dare ba rana. Amma a ranar 7 ga Oktoba, tana cikin uku da ba su aiki a ranar.

“Balambalan ɗin da ke Nahal Oz ta lalace, amma da aka yi korafi sai aka faɗa wa sojojin cewa za a gyara ranar Lahadi,” a cewar Mista Ben Shitrit.

Da ta koma kan teburinta, Sharon ta ci gaba da sanar da dakarun da ke kasa. “Ina kuka ina sanarwa a lokaci guda,” in ji ta.

‘Yan mintuna bayan karfe 7:00 mayakan Hamas suka isa kofar Hamal – ɗakin harkokin yaki na sansanin.

Sharon ya tuna lokacin da aka ba su umarnin: “Ku mike, mahara sun iso bakin kofa.

Nan take aka ba su umarnin kowa ya bar inda yake ya koma wani ɗaki da ke ciki Hamal.

7:20

Da misalin karfe 07:20 mahara sun far wa wurin da ake kira garkuwa – wani wurin ɓuya da ke wajen Hamal.

Cikin waɗanda ke zaune a ciki akwai dakarun da ba su kan aiki da ke samun kariya daga wasu “gwarazan dakaru

mata”.

IDF ta faɗa wa iyalai cewa dakarun mata su kaɗai ne ke da makami kuma su ne suka hana maharan motsawa tsawon lokaci har zuwa lokacin da makamin gurneti ya kashe ɗaya daga cikin kwamandojin kuma ya raunata sauran.

A daidai lokacin ne kuma 10 daga cikinsu suka tsere zuwa cikin barikin, amma duk sauran da suka tsaya a cikin maɓoyar, ko dai an kashe su ko kuma an kama su.

8:00

Mintuna kafin 8:00, jirage marasa matuka na Isra’ila suka karaso amma suka kasa tantancewa tsakanin sojoji da mayakan Hamas, a cewar IDF, abin da ya sa suka kasa kai wa Hamas hari.

9:45

Sama da awa uku da fara kai harin, da karfe 09:45 jirgin helikwafta na IDF ya fara harbi kan mayakan Hamas, kuma an faɗa wa iyalan cewa jirgin ya yi harbi kan sansanin sau 12.

Shimon da wasu shida, har da kwamandansu, sun gudu daga sansanin kuma suka koma daga baya a kafa.

Baya ga ɓarin wuta na manyan bindigogi, sai ga maharbin ɓoye na Hamas na yin ɗauki ɗai-ɗai. “Duk lokacin da ya harbo sai ya kashe abokin aikina,” in ji Shimon.

Shi kaɗai ne ya tsira cikin waɗanda suka fafata tare a lokacin.

11:00

Zuwa karfe 11:00, ɗakin yaki wato Hamal ya zama cikin duhu saboda mayakan Hamas sun katse lantarkin da ke ba da damar rufe kofofinsa. Nan take suka fara ɓarin wuta a ciki da kuma jefa abubuwan fashewa.

IDF ta faɗa wa iyalan mutanen cewa dalilin da ya sa kenan ɗakin ya kama da wuta kuma ya kone kurmus.

12:30

Wajejen karfe 12:30, mutum bakwai cikinsu har da Sharon suka nemi tagar banɗaki kuma suka fice ta cikinta, kamar yadda waɗanda suke wurin a ranar suka bayyana.

A faɗin Isra’ila a wannan ranar, kusan mutum 1,200 – cikinsu akwai sojoji 300 – aka kashe kuma aka yi garkuwa da 251.

Tun daga lokacin, an kashe Falasɗinawa sama da 41,000 sakamakon hare-haren Isra’ila na ramuwa a Zirin Gaza, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta yankin ta bayyana.

Mun ciro labarin daga BBC