✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Mauladin Nyass na duniya ya gudana a Kebbi

A ranar Asabar da ta gabata ce mabiya Darikar Tijjaniya da Sidi Ahmad Tijjani ya assasa a 1784 a kasar Aljeriya da ke da dimbin mabiya…

A ranar Asabar da ta gabata ce mabiya Darikar Tijjaniya da Sidi Ahmad Tijjani ya assasa a 1784 a kasar Aljeriya da ke da dimbin mabiya a Afirka ta Yamma suka gudanar da Mauludin mutum na biyu mafi daraja a darikar, Sheikh Ibrahim Nyass.

Taron Mauludin ya samu halartar manyan malaman darikar daga sassan duniya da suka hada da Muritaniya da Masar da Senigal da sauran kasashen Afirka.

Wakilinmu ya ruwaito cewa al’amura sun tsaya cik a Birnin Kebbi fadar Jihar Kebbi yayin gudanar da Mauludin na wuni biyu da aka  gudanar a filin wasa na Sarki Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi, inda dandazon jama’a ta sanya hatta jami’an tsaro da masu kula da ababen hawa suka kai ga rufe hanyar shiga filin da ake Mauludin, illa hanyar da manyan malamai ke shiga.

Makarantu da gidajen mabiya darikar sun gaza daukar bakin da suka Mauludin inda yadda dubban mutane suka rika kwana a filin Mauludin. A gefe guda kuma masu sayar da abinci da ruwan sha sun tsauwala farashi ga jama’ar da suka halarci Mauludin, wadanda suke yin rububin sayen su.

A jawabin Sheikh Muhammadu Maki Nyass daga kasar Senigal ya ce sun zo Najeriya kuma a Jihar Kebbi domin tattauna rayuwar Manzon Allah (SAW), kuma soyayyar Manzon ita ce gaba a Musulunci.

Shehun Malamin ya ce bai taba ganin Shehu ya rubuta wani abu akan kasarsu ta Senigal ba, amma ya rubuta a kan wannan kasa taku Najeriya mai albarka, saboda haka a kullum muna yi wa Najeriya addu’a a kan fitinun da suke damunta na Boko Haram da masu satar mutane da sauran ’yan ta’adda.

“Mu ’yan Najeriya ne ba baki ba ne, da na ji cewa za a yi Mauludi a Najeriya kuma a karkashin Shehu Tijjani, sai na ce da yardar Allah sai na je, domin son Manzon Allah,” inji shi.

Ya ce sun yi godiya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya tura Ministan Shari’a Abubakar Malami ya wakilce shi da kuma Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, inda ya yi addu’ar Allah Ya sa su kara cin zaben da za a yi a watan gobe, kuma Allah Ya tona asirin dukan azzalumai da ’yan ta’addan kasar nan maza da mata.

Shi kuwa Sheikh Abubakar Nyass ya yi kira ne ga shugabanni su ji tsoron Allah kuma su yi koyi da halayen Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu a kan girmama Manzon Allah, lura da dimbin mutanen kasashe daba-daban da ya shirya walima kowa ya samu abinci ya ci har tsawon kwana biyu, wannan ya nuna son Manzon Allah da kuma alayensa.

A karshe ya ce “Jama’ar Musulmi mu rike Kur’ani, a kauce wa rashin gaskiya, domin wasa da Kur’ani yana haddasa fitinu su yi yawa a kasa, kullum abubuwan sai kara yawa suke yi, saboda haka mu koma ga Allah.”

A jawabin, Sakataren Kungiyar ta Kasa, Alhaji Muhammad Alkasim Yawuri ya yi godiya ga Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu kan hadin kan da suka samu da kuma gudunmawar da ya ba su domin gudanar da wannan muhimmun taro da aka yi.

Ya yi kira ga Gwamna Atiku Bagudu ya taimaka musu da filin da za su gina babbar makaranta domin ci gaban ilimi a jihar, kamar yadda sauran kungiyoyin Musulunci suke da su.

A jawabi Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya nuna farin ciki kan ganin yawan jama’ar da suka halarci Mauludin. Gwamna Bagudu ya yi fatan Allah Ya mai da kowa gidansa lafiya  kuma ya tabbatar da zai ba kungiyar filin da suka nema domin gina makaranta, inda ya kara godiya ga dukan shehunnan da suka zo daga kasashen waje da na gida Najeriya, kuma ya ce a shirye gwamnantinsa ta ke a duk lokacin da suka nemi wani taimako.

A sakon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Minista Abubakar Malami ya gabatar a wajen Mauludin, ya bukaci ’yan Najeriaya su zauna lafiya da juna don ci gaban kasar nan. Sannan ya yaba wa mabiya Darikar Tijjaniyya kan shirya Mauludin wanda ya ce zai taimaka wajen karfafa soyayya da girmama juna a tsakanin mabiya. Kuma ya yi kira ga Musulmi su ci gaba da yi wa kasar nan addu’a tare da yin koyi da koyarwa marigayi Sheikh Ibrahim Nyass wanda ya yada addinin Musulunci ta hanyar nuna kauna da soyayya, kuma ya isa ga dukan al’ummar duniya baki daya.

Manyan shehunan da suka halarci Mauludin, baya ga wadanda suka fito daga jihonin Najeriya, akwai wadanda suka zo daga kasashen Senegal da Nijar da Ghana da Kamaru da kuma Birtaniya, kamar Sheikh Abubakar Nyass da Sheikh Muhammadu Maki Nyass da Sayyadi Ali Nyass Muhammad Sise da Sheikh Alkaliru Cota da kuma Sheikh Muhammadu Suru.