✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda matashi ya damfari mata 6 Naira miliyan 4 a Legas

Mun gano ya sayar da kowacce waya kan N900,000.

Ana zargin wani matashi mai suna Ifeanyi Ezennaya, da damfarar wasu mata kawayen juna su shida wayoyin salula kirar iPhone da sarkar zinari da darajarsu ta kai Naira miliyan hudu.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa ta bayyana cewa, sai da Ezennaya ya shayar da su abin gusar da hankali kafin ya samu ya wawushe wayoyi da sauran kayayyakinsu ya kara gaba.

Ta ce lamarin ya faru ne a yankin Surulere da ke Jihar Legas, bayan da Ezennaya ya gayyace su shakatawa a wani daki da ya kama a wani otel.

Ta kara da cewa isar su dakin ke nan, sai ya ciro kwalbar giya a firinji ya zuba musu suka kwankwade.

Tun daga lokacin da suka sha giyar, hankalinsu ya gushe, inda suka shafe sa’o’i shida suna sharbar barci, wanda hakan ya bai wa Ezennaya damar kwashe wayoyinsu, inji ta.

Ta ce, “Tun farko mun soma haduwa da shi ne a wajen wani bikin murnar zagayowar ranar haihuwa, inda ya gabatar mana da kansa a matsayin Emeka, sannan ya ce mana dawowarsa kenan daga kasar Switzerland.

“A nan ne biyu daga cikinmu suka bashi lambobinsu na wayar salula,” inji ta.

“Bayan mun je dakinsa na Otel din, mun sha giyar da misalin karfe 7:00 Yamma, amma da muka soma barci ba mu muka farka ba sai karfe daya na dare.

“A daidai wannan lokaci ne muka fahimci an yi mana sata, an kwashe mana wayoyi kirar iPhone guda shida da agogo da sarkar zinari da sauransu.

“Daga nan muka fahimci an zuba kwaya a cikin abin da muka sha,” inji ta.

Kazalika, ta ce Ezennaya ya yi amfani da katin cirar kudi na ATM na daya daga cikinsu, inda ya sace mata Naira 50,000 daga asusun ajiyarta na banki.

Ta ce, “Daga bisani, mun gano ya tura wayoyinmu Anaca inda ya sayar da kowacce kan N900,000.”

Ofishin ’yan sanda na Surulere ya ce an cafke Ezennaya a wani otel da ke yankin Ikeja, inda a nan din ma ya yi yunkurin damfarar wasu.