✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mata suka daure dan kishiya a turken awaki

Kishishoyi uku sun hada baki da mahaifin yaron suka daure shi tare da dabbobi

’Yan sanda a Jihar Kebbi sun tsare wasu mata uku da mijinsu bisa zargin daure dan kishiyarsu a turke na tsawon shekara biyu.

Yanzu haka ana binciken ma’auratan da ke zaune a Unguwar Badariyya inda suka daure yaron tun bayan rabuwar mahaifiyarsa da mahaifinsa.

“’Yan sanda sun kama mahaifin wani yaro dan shekara 11 da matansa uku da suka hada baki suka daure yaron na fiye da shekara biyu a Unguwar Badariya da ke gar Birnin Kebbi

“An kai yaron Asibitin Tunawa da Sir Yahaya ana kuma bincike domin gano abun da ya sa suka daure yaron tare da dabbobi har shekara biyu,” inji Kakakin rundunar DSP Nafi’u Abubakar.

A ranar Lahadi ne jami’an hukumar kare hakkin bil-Adama suka kubutar da yaron daga inda aka turke shi, bayan fitar uwarsa daga gidan.

Hotunan da aka yada a shafukan zumunta sun nuna shi yana tafiya da kyar saboda azabar daurin da ya sha.

— ‘Yaron na da tabin hankali’

Iyayen dai sun shaida wa ’yan sanda cewa yaron tababbe ne kuma yana fama da larurar farfadiya wanda hakan ne ya sa suka yanke shawarar daukar matakin.

Amma DSP Nafi’u Abubakar ya ce bincike ne kawai zai tabbatar da zargin da suka yi.

“Yanzu haka yana asibiti shi yaron…. muna so mu ji sakamakon asibiti me zai nuna ko rashin abinci ne da tsangwama suka sa shi halin da yake ciki”, inji DSP Nafi’u.

— Gwamnatin Kebbi ta shiga ciki

Tuni dai Gwamnatin Jihar Kebbi ta ba da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin.

Gwamna Atiku Bagudu a cikin wata sanarwa ta bakin hadiminsa kan harkokin watsa labarai bangaren shafukan sada zumunta, Aliyu Bandado ya bayyana lamarin a matsayin ‘rashin imani’.

Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda yaron ya shiga mawuyacin hali ba kawai a hannun iyayensa ba, har ma da gazawar makwabtansu na sanar da hukumomi halin da ake ciki.

“Gwamnatin Kebbi ta kadu da labarin yaron da aka daure tare da dabbobi ba tare ba shi abinci ba na tsawon shekaru biyu”, inji Mai ba wa Gwamnan Jihar Shawara kan Harkokin Mata da Walwalar Jama’a Zara’u Wali.

Gwamnatin Jihar ta kuma yi alkawarin daukar nauyin kula da lafiyar yaron da kuma ba shi kulawa har sai ya dawo hayyacinsa.