✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mata ke fin maza ɗaukaka a finafinai a Nijeriya

Rasuwar Darakta Aminu S. Bono ta kara nuna akwai matsala a masana’antar Kannywood.

A harkar finafinai a Nijeriya da ma duniyar fim baki daya, an fi ambaton mata da zarar an yi maganar jarumai.

Aminiya ta ruwaito yadda a Kannywood za a iya cewa matan ma sun fi mazan samun daukaka, idan ana batun yawan wadanda suka samu daukakar.

Wannan dai na kan madogarar cewa da zarar aka cire irin su Ali Nuhu da Sani Danja da Adam A. Zango, daidaikun wasu jaruman ne za a iya kwatantawa da irin daukakar da jarumai mata irin su Rahama Sadau da Nafisat Abdullahi da Hadiza Gabon suka samu, a cikin kankanin lokacin da suka shigo masana’antar.

Sai dai ba kasafai matan suke dadewa suna jan zarensu ba a masana’antar, inda ake samun wasu suna rufe su, suna cikin tashe.

Aminiya ta ruwaito har yanzu ba a samu jaruma da ta dade tana jan zare a masana’antar Kannywood kamar Fati Muhammad ba, duk da ita ma idan aka kwatanta ta da jarumai maza, irin su Ali Nuhu za a ga ta bace ta bar su, suna ci gaba da yayi.

Sai dai ana ganin jarumai matan sun fi tara dukiya, musamman ganin yadda ake ganin suna watayawa a kasashen duniya, yayin da wasu mazan da dama da suka dade a masana’antar suke komawa Allah-ba-ku-musamu da zarar sun fara tsufa, harkar ta daina yi da su.

Rasuwar Darakta Aminu S. Bono ta kara nuna akwai matsala a masana’antar, kasancewar duk da ya dade sai bayan rasuwarsa aka saya wa iyalinsa gida kyauta, sannan kuma dama can mawaki Dauda Kahutu Rarara ne ya saya masa motar hawa.

Aminiya ta ruwaito a masana’antar fim ta Kudu, wato Nollywood, an samu zaratan masu bayar da umarni da suka yi shuhura.

Akwai irin su Mo Abudu, mai Kamfanin Ebonyi Life wadda ta shirya ta kuma bayar da umarni a wasu manyan finafinan Kudu.

Daga cikin finafinanta akwai ‘Blood sisters’ da ya samu makallata sama da miliyan 11 a manhajar Netflid a cikin awanni kadan da fitar da shi.

Ita ma Kemi Adetiba fitacciyar darakta ce a masana’antar shirya fim ta Kudu. Daga cikin finafinanta akwai irin su King of Boys da Wedding party da sauransu.

Idan aka dawo bangaren shirya finafinai kuwa, jarumai mata na Kudu su ne kan gaba wajen shirya finafinai da suka samar da kudade.

Ba-zatar mata a fim

A Masana’antar Kannywood, fim din Rahama Sadau, Mati a Zazzau ne fim na farko da ya samu shiga manhajar Netflix.

Kannywood ta dade tana fama da matsalar tabarbarewar tattalin arziki da rashin kasuwancin finafinanta, inda da dama daga cikin masu ruwa da tsaki a masana’antar suka yanke shawarar cewa manhajar Netflix ce kadai za ta magance musu matsalarsu.

An dauki shekaru ana kai-kawo a kan samun shigar da finafinan Hausa manhajar, amma ba a samu nasara ba.

A karshen shekarar da ta gabata ce kwatsam aka samu sanarwa daga Rahama Sadau cewa, fim dinta ya samu karbuwa a manhajar, wanda da farko an dauka wasa ne.

Idan ba a manta ba, jarumar ce ta fara tsallakawa finafinan Indiya da Amurka a Kannywood bayan na Kudancin Nijeriya da take yi, duk da cewa Ali Nuhu ya riga ta fara zuwa Kudu.

Sai dai nasarar ta so ta kawo baraka a masana’antar, kasancewa ana ta batun Rahama ce, inda wasu suka yi zargin an yi watsi da marubucin fim din da kuma darakta.

Darakta Yaseen Auwal ne ya ba da umarni, sannan Yakubu M. Kumo ne ya tsara labarin.

A bangaren Kudu kuma, Aminiya ta ruwaito cewa, fim din Funke Akindele mai suna A Tribe Called Judah ya samar da kudi sama da Naira biliyan daya, wanda shi ne mafi yawa da fim din Nijeriya ya samar a tarihin finafinai baki daya a kasar.

A bara ma Aminiya ta ruwaito cewa, fim dinta mai suna Battle on Buka Street shi ne fim wanda ya fi samar da kudi, inda ya samar da Naira miliyan 668,423,056.

Haka kuma fim dinta mai suna Omo Ghetto: The sage ya samar da Naira miliyan 636,129,120.

Rahama Sadau ta shirya finafinai manya, irin su Mati a Zazzau da ya yi tashe a sinima.

Haka ita ma Nafisat Abdullahi ta shirya fim din Yaki a soyayya wanda shi ma ya yi tashe matuka.

Yanzu haka jaruma Aishatu Humaira ta shirya tsaf domin fara daukar shirinta na A cikin biyu, wanda ya kunshi manyan jarumai irin su Ali Nuhu da Adam A. Zango da sauransu.