Akalla mutum biyar rahotanni suka nuna sun mutu a ranar Juma’a yayin da masu zanga-zangar #EndSARS da zauna gari banza suka yi wasoson dukiya da kayan abincin da Gwamnatin Tarayya ta bayar tallafi domin rage radadin annobar coronavirus.
Mutum uku sun mutu yayin da aka cinna wuta a ofishin Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kuros Riba (SEMA) inda aka ceto wasu mutane bayan sun shaki hayaki.
- Buhari ya fadi adadin mutanen da aka kashe a zanga-zangar EndSARS
- EndSARS: Dalilin da ya hana Buhari magana a kan harbin Lekki
A safiyar Asabar, masu zanga-zangar sun kone wani gidan mai mallakar Gwamnan Jihar Kuros Riba, Ben Ayade.
Ba su tsaya nan ba, sun koma gidajen Sanatoci masu ci yanzu da suka hadar da gidan Sanata Genshom Bassey da ke Asari Edo da na Sanata Victor Ndoma Egba.
Kazalika bayan kona bankin First Bank reshen 8miles a Kalaba a ranar Asabar, sun kuma kai hari didan dan Majalisar Wakilai, Essien Ayi.
Haka Kuma sun koma kantin zamani na matar tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba Sanata Liyel Imoke sannan suka fantsama sauran wurare a birnin Kalaba suna ci gaba da tafka ta’asa.
Daga cikin sauran wuraren da aka kai hari sun hadar da Ofishin Hukumar Kwadago (NLC), da na Hukumar Zabe (INEC) da kuma Ofishin ‘Yan Sanda na Atakpa.