✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda masu yaki da barayin shanu suka koma masu jihadi  a Sakkwato

Amakon jiya ne aka samu rahotannin bullar wata kungiyar masu da’awar jihadi a wasu yankunan kananan  hukumomin Tangaza da Gudu da ke Jihar Sakkwato. Aminiya…

Amakon jiya ne aka samu rahotannin bullar wata kungiyar masu da’awar jihadi a wasu yankunan kananan  hukumomin Tangaza da Gudu da ke Jihar Sakkwato. Aminiya ta samu labarin cewa  tun wata biyu da suka gabata bakin mutanen wadanda ’yan banga ne suka je yankin da nufin fatattakar barayin shanu da masu garkuwa da mutane, amma sai suka rikide zuwa masu da’awa da ikirarin jihadi.

Aminiya ta samu labarin cewa, mutum 10 ne suka fara zuwa yankin don yaki da barayin amma yanzu sun fi 150, kuma sun fito da wasu abubuwa na addinin Musulunci da suke son mutanen yankin su rika yi kamar daina sauraren wakoki sai wa’azi da karatun Kur’ani. Suna kuma hana bukukuwan aure na al’ada, musamman kide-kide da raye-raye kuma suna tantance limamai da masu kiran Sallah. Duk wanda ba su gamsu da shi ba su hana masa ci gaba da yi a yankin, suna kuma karbar da Zakka a yankin daga duk wani mai dabbobin da suka kai adadin fitar da Zakkar.

Lokacin da Aminiya ta ziyarci yankin, ta samu mutane suna harkokinsu cikin lumana ba wata fargaba. Hasali ma suna jin dadin mutanen da ake zargi sun zo ne daga kasar Mali, wadanda suke cikin kungiyar Mujawu. Bakin suna zaune ne a cikin dajin kan iyakar Najeriya da Nijar kuma suna shigowa kauyukan da ke zagaye da su don sayen ruwa ko lemu ko sigari amma babu ruwansu da kowa sai barayi. Majiyarmu ta ce da an nuna musu barawo ko aka kai musu labarinsa, ba zai sha ba sai sun kashe shi ko ya bar yankin.

Daya daga cikin hakiman garin (an sakaya sunansa) ya ce: “Mutanen nan su ne suka kori Zamfarawan da suka addabe mu da sata da garkuwa da mutane. Ba mu da wata matsala yanzu, mutanen ba su taba kowa in ba wata matsala daga baya ba. Gara mutanen nan da wadanda suka addabe mu, su ba su shiga harkar kowa duk da suna da bindigogi tare da su, lafiya lau muke da su.”

Wani da ya nemi a sakaya sunansa da ke zaune a yankin ya shaida wa wakilinmu cewa bakin suna cikin yankin nasu kuma ana jin dadin zama da su, domin sun kawar da tsoro da fargaba da yankin ke fama da shi.

“A garin Mullawa aure uku suka yi, an yi auren kamar yadda shari’a ta tanada. Sadaki kawai suka bayar aka daura aure, suna barin mace gidansu ne don su a daji suke da hemominsu. In miji yana bukatar matarsa yakan zo gidansu, don su ba su son zina.

“In sun zo fitar da Zakkar dabbobi, a gaban mai dukiya sai su ce ya nuna musu “Tokereji” (dabbobin kiwo, wadanda ba mallakin mutum ba), sannan su fitar da Zakka su tafi da ita. In sun gano liman ko ladan bai san abin da yake yi ba, sukan kore shi. A garin Maitseka ma sun dakatar da ladani daga kiran Sallah. In sun kama barawo ko mai hulda da shi, kashe shi suke yi,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa “Mutanen nan Larabawa da Fulani da Buzaye ne amma yanzu sun fara samun Hausawa da Fulani a cikinsu daga cikin mutanen garin Tangaza, har sun sanya wakilinsu mai suna Jankobare. Ko sun yi tafiyarsu shi ne zai kula da tsare garin don sun fadi cewa hukuma ba ta iya tsare mutane dole ne mutane su tsare kansu. Kafin su zo yankin, barayi sun addabi dukan garuruwan da ke kan iyakar Nijar da Najeriya, sun kori barayin amma sun ce su ba su yarda da hukuma ba, domin ta Nijar ta yaudare su. Kan haka Sarkin Yamman Balle ya kira su suka ki zuwa.

“Mafi yawan wadanda muka gani, harshen Mali Bambaranci da Fullanci da Turancin Faransa suke yi, ’yan kadan daga cikinsu suna Hausa. Mun fahimci akidarsu ta Salafiyya ce kuma duk lokacin da za su ba ka hujja, sai ka ji sun ce Ibn Taimiyya ya ce kaza. Sun fi shiga da zama a kauyukkan Salewa da Wayege da Tunegara. Duk wanda ya aminta suka ba shi horo har aka kare bai gudu ba suna ba shi babur na hawa, irin wanda suke amfani da shi. Tun bayan Sallah Karama suke yankin,” inji shi.

Shi kuwa Abdullahi Musa, ya ce mutanen suna nan a dajin Tagimba, sun kai su 200. Ba su fi wata biyu a wurin ba, kuma akwai fararen Buzaye a cikinsu. “Ina ganin suna da alaka da Mujawu ’yan tawayen Mali, suna karantar da yara da manya addini a yankin. Ko jiya (Lahadin da ta gabata) sai da aka yi karatu kuma ba su karbar kudin Zakka, ni ban gani ba,” inji shi.

Wani mutum a kauyen Masallacin Gunguno ya ce yana tsammanin mutanen na da alaka da kungiyar Boko Haram, domin a kauyen Jimajimi ne suka sanya liman yin hudubar Jumu’a har sau biyar. “Duk hanyar da jami’an tsaro suke ba su bi da babur, in za su shiga Nijar. Ana zargin wani dan limami ya shiga kungiyarsu. Barayi kawai suke nema, sukan shiga Tagimba da Ruwawuri da Tunga ta Kaurawo, ba ruwansu da kowa. Tashin hankali guda ne a rika ganin farar hula da wadannan miyagun makamai tare da shi,” inji shi.

Da wakilinmu ya tuntubi Sheikh Abubakar Usman Mabera, Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Izala Reshen Sakkwato ya ce: “Da na samu labarin bullar mutanen a Tangaza da Balle, kasancewar muna da almajirai a wurin, mun bincike su kan samuwar kungiyar jihadi dauke da makamai; suka fada mana cewa asali mutanen an gayyato su ne su kori barayi masu garkuwa da mutane. An ce wani mutum ne da aka sace masa wani nasa ko ’yarsa ce, ya je Nijar ya gayyato su, suka zo.

“An ce sun fada wa jami’an tsaro za su zo, aka ba su dama suka yi wannan aikin na kama barayi, suka kashe na kashewa wuri ya yi lafiya. Ba komai, sun yi abin kwarai ta wani bangare. Ba barayi, sai suka fara shiga masallatai suna jawabai. Ba su jin Hausa sai Larabci da wani yare da ba mu ji, dukansu ba ’yan Najeriya ba ne, daga kasar waje ne Mali ko Nijar. Su masu jihadi ne, suna daukar mai dukiya saman babur su tafi inda dabbobinsa suke, a fitar masa da Zakka,” inji shi.

Ya ce “To babu matsalar da ta kai jingina wannan da jihadi, domin dukan tsarin jihadi na Musulunci ba su kan ko daya. Wannan ba jihadi ba ne, tarzoma ce ko fitina ko tawaye a addini; domin littattafan addini ba haka suka zo da tsarin jihadi ba.”

Ya ci gaba da cewa “Shi mai kira karantarwa ce kawai tasa, haka samun mutane saman addininsu na Musulunci in suna kuskure, gyara musu amma ba wuce gona da iri ba. Zakkar da suke karba wa ya sanya su? Tana da tsari baa ba  kowa ba sai jagora ko kasar nan ba ta da jagoranci ne kowa ya zo ya diba da kansa?”

“Karatun littattafan Ibn Taimiyya da suke yi ko shugaban Boko Haram haka ya yi, ya yi gabas suka yi yamma. Sanin Larabci daban, fahimta daban. Ina kira ga hukuma ta kame hannayensu, ta hana su wannan. In wani abu suke so na gyara, su yi yadda addini ya aminta, kada reshe ya juye da mujiya ka ji sun hada kai da ISIS ko Alka’ida,” inji Sheikh Mabera.

Game da cancantar limamai da ladanai, ya ce “Da wane matsayi suke yin wannan? Su ne Sarkin Musulmi ko gwamnati ne su? Canja liman ko ladan aikin Sarkin Musulmi ne, ko wanda ya wakilta, yin wannan ba su da hakki. Fitina ce suke son su kawo cikin kasa, ina kira ga gwamnati ta dauki matakin zama da su kada su yi karfi su zama ’yan tawaye da ba su biyayya ga hukuma. A zauna da su kada a yake su. Idan  da’awa suke yi, su bi ka’idar kasa.”

Jami’ar hulda da jama’a ta ’yan sandan Jihar Sakkwato, Cordelia Nwawe ta ce ba wata matsala a yankin Tangaza. Ta ce Kwamishinan ’Yan sanda da mutanensa sun tafi yankin, kowa na harkokinsa lafiya lau. Ta ce babu wata kungiya ta masu jihadi wurin, ba komai. “Su zauna lafiya, in akwai wani abu su sanar da jami’an tsaro don daukar mataki kuma za mu ci gaba da sanya ido a wurin don tabbatar da zaman lafiya,” inji ta.