Masarautar Kaltungo da ke yankin Karamar Kaltungo a Jihar Gombe tana kokari a kan wani shiri da Sarkin Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad ya bullo da shi da nufin yakar yunwa da fatara da talauci cikin al’ummar masarautar ta hanyar noman rogo.
Wakilin jaridar Aminiya ya gana da sarki Uban kasa, Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakuna ta Jihar Gombe, Injiniya Saleh Muhammad Umar cikin talakawansa da ke aikin gayya a gonarsa rike da fatanya ya duka yana nome ciyawa.
Sarkin Saleh ya yi karin haske kan wannan aiki da suke yi a masarautar.
Ya ce, “Mun soma noman rogo ne lokacin da yunwa ta fara bayyana a cikn al’ummarmu, sai muka lura da cewa noma ba ya yiwuwa a wannan zamani sai kana da takin zamani, shi kuma takin zamanin nan ba za ka iya samun sa ba sai kana da kudi masu yawa, kuma al’ummarmu mafi yawa ba su da wadannan kudade sai muka juya zuwa ga noman rogo cikin wannan masarauta.
“Saboda mun lura shi noman rogo ba ya bukatar takin zamani kuma ba ya bukatar kulawa kamar noman shinkafa ko masara ko dawa ko gero da sauransu, amma shi rogo da ka shuka shi sai ka juya baya, in dai ba damo ko dabbobi suka lalata maka ba, in shekara ta yi sai ka je, ka cire rogon rututu ya nuna, saboda ka san shi rogo shekara guda yake yi kafin ya haihu”.
Ya kara da cewa, “Akwai wani lokaci da aka ce mana akwai rogon da yake yi a wata uku, muka yi ta nema ba mu samu ba, muka yi ta neman iri ba mu samu ba, sai muka je Adamawa, muka samu wani iri muka shuka amfanin da ya fito ya ba mu mamaki don mun samu motar tirela 20.”
Sarki Saleh ya ce, “Kuma shi wannan rogon muna iya yin garin kwaki da alabo da garin filawa, ana yin biredi da komai da shi don ka samu kudi ko abinci.
“Daga nan muka koma kuma muka je kasar Taraba nan ma suna da irin rogo mai ba da amfani manya-manya, muka nemo shi, muka gwada sai ya ba mu amfani mai yawa saboda sabuwar dabarar noman rogo da muka samo.
“Wannan sabuwar dabara da muka samu ita ce yadda muke yin shukar kuma ya fito da yawa, ya ba da amfani mai yawa.
“Da muna dasa irin rogon a tsaye sai muka fahimci cewa, asalin shi noman rogon jijiyoyin da suke kama kasa su ne suke samar da ’ya’yan rogon, sai maimakon mu sa shi irin a tsaye, sai muke sa shi a kwance in muka yi haka duk jikinsa sai ya ba da ‘ya’yan rogon.
“Kuma yana magance mana yunwa kwarai da gaske, kuma kowane gari idan muka noma mukan bai wa al’ummar wajen kyauta, ka ga noman da muka yi tare da su ya zama ‘yar manuniya, mun nuna musu hanya ke nan, mu kuma mun sami nasara saboda da ma neman iri muke yi na rogon wadanda muke turawa in suka je Taraba ko suka je Adamawa sai su samo mana irin kamar buhu 20.
“Idan suka samu sai su toro mana, mu kuma in mun noma ka ga wannan al’ummar tamu da muka yi noma tare da su ka ga su sun samu iri kyauta. Sai kuma in muka sake samowa mu koma ga wasu al’ummar.
“Ta haka za mu jawo hankalin al’umarmu zuwa noman rogo”.
Mai Kaltungo ya kara da cewa, “Ka ga rogon nan in ka noma za ka iya sayar da shi, kudin da ka sayar da shi ka sayi abincin da kake so kamar shinkafa ko gero ko dawa ko masara har ma ka samu kudin cefane, kuma ga rogo abinci a gida kana da shi.
“Yadda na fahimta bayan mun gwada shi, sai na ga noman rogo duk ya fi noman shinkafa da gero da dawa da masara riba.
“Shi noman rogo yana bukatar manya manyan kunya saboda jijiyoyin da suka shiga cikin kasa su girma.
“Sai dai in ba ka sa da wuri ba ciyawa za ta tsiro. Ka ga in ta tsiro dole sai ka cire ta sannan wani lokaci in mun yi noma ni ma nakan sa wake a ciki to waken shi ne nawa.”
Sarki Saleh ya ce, “Mun fara gwajin noman ne cikin al’ummar Ture Kwaldi, sai Ture Kwalam su ne suka ce in zo wajensu za su ba ni fili, kuma mun yi shukar, ka san shi rogo indai ya kama, ya fito sai dagawa kawai zai yi, ya yi rututu bayan shekara daya.
“Muna kuma kokarin yadda za mu samu rance daga Babban Bankin Kasa mu bunkasa noman rogo.
“Mun tanadi fili eka dubu biyu, za mu sama wa matasa da dama aikin yi.
“Muna fatan za a samu na kuma taba kawo fa’idar noman rogo a Jihar Gombe kuma gwamna ya karba ya ce kowace karamar hukuma ta je ta noma eka 20.
“Mun san gwamnati na kokari wajen noma, amma kudin noman ya kamata a rika amfani da shi wurin noma, in aka yi haka za a samu nasarar wadata al’ummarmu da abinci.”
A kowane lokaci kamar yadda ake yi a zamanin Sarkin Kaltungo yana kiran al’ummarsa daga wurare dabandaban cikin kasarsa kamar unguwannin Termana da Banganje da Kalorgu da Kamo.
Haka ma al’umma daga kauyukan Adarawa da Kukuki/Sada da Birwai da Kobdon da Kublo da Tukade da Sheshore da Jauro Yaya duk a cikin gundumar Kamo.
A Karamar Hukumar Kaltungo karkashin jagorancin hakimin cikin garin Kaltungo, Alhaji Amadu Ibrahim duk sun yi noman a gonar Sarki wadda take kasar Kamo a Karamar Hukumar Kaltungo da sauran wurare suna amsa kiran gayyar, suna yin noma da addu’ar Allah ya sanya wa gonar albarka, Allah ya kara wa Uban kasa son al’ummarsa.
Wasu daga cikin matasa da aka gani na dauke da ganga suna kida a yayin da suke aikin gayya a gonar Sarkin Kaltungo ta Shinkafa sun nuna farin cikinsu da irin yadda mai martaba Mai Kaltungo ke taimaka musu kuma yake gayyatar su aikin gayya, inda suka ce duk lokacin da Sarki ya yi kira su abin farin ciki ne a wurinsu su amsa wannan kira na sarki kuma su je su ba da tasu gudunmawar ta noma a gonar sarki.
Sun ce Shinkafar ma in Sarki ya noma a karshe su al’ummar yake taimakawa ya ba su kyauta don su sami abinci.
Haka kuma sun ce shi kansa Sarkin da ’ya’yansu da yayunsu da iyayensu duk kowa na farin cikin da amsa kiran Sarki don yin aikin gayya.