✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mai digiri ya samar wa matasa 130 aikin yi

Babagana Abba Dalori wani wanda ya kammala karatun digiri ne daga Jami’ar Maiduguri da ke Jihar Barno. Bayan ya kammala karatunsa a fannin injiniya, ya…

Babagana Abba Dalori wani wanda ya kammala karatun digiri ne daga Jami’ar Maiduguri da ke Jihar Barno. Bayan ya kammala karatunsa a fannin injiniya, ya yi aikin yi wa kasa hidima ne (NYSC) a Jihar Kogi a shekarar 2010.
Yayin da yake NYSC, yakan ziyarci kawunsa wanda yake zaune a Babban Birnin Tarayya Abuja akai-akai, kuma daga nan ne ya fahimci gibin da ake da shi ta fuskar sufuri a birnin.
Ya ce, “daga kudin alawus da ake biyanmu lokacin NYSC na tara na sayi Keke NAPEP guda (wato babur mai kafa uku, ko Adaidaita Sahu).”
Ya ce daga nan ne bayan  wata shida sai ya kara sayen wani. “Amma yanzu kamfanina yana da kekuna kusan guda 116,” inji shi.
Babagana ya fara tunanin kafa kamfanin kansa ne tun lokacin da yake aikin yi wa kasa hidima a Jihar Kogi.
Ya ce: “Na san cewa bayan na kammala aikin NYSC samun aikin zai iya ba ni wahala saboda yadda na ga takwarorina sun fuskanci hakan. Hakan ya sa na fara shirya wa kalubalen.”
Ya ce a lokacin da yake tafiyar da kekensa na fari, ya fara aikin koyarwa a wata makaranta koyar da ilimin kwamfuta, inda daga nan ne ya kara samun kudin shiga, wadanda da su ne ya hada ya sayi kekensa na biyu bayan wata shida da sayen na farko.
Saboda yadda harkar ta samu ci gaba cikin sauri, ’yan uwa da abokan arziki sun rika sanya kudinsu a ciki. Daga bisani ya sanya wa kamfaninsa suna Galady Transportation  and Construction Serbices.
“Ba na tuka kekunan da kaina, amma ni nake daukar direbobinsu, inda suke kawo balans din Naira 17,500 a kowane mako. Kuma idan aka yi shekara guda ana hakan, ya zama nasu,” inji shi.
Hakazalika, ya ce kowane mutum zai iya shiga harkar. “Mutum zai fara ne da biyan Naira dubu 435 a asusun bankinmu. Inda mu kuma za mu saya masa Keke NAPEP guda. Daga nan za mu samu direba mu ba shi keken. A kowane mako kuma za mu rika ba shi Naira 15,000 daga Naira 17,500 da direban ya tara masa. Muna ajiye Naira 2,500 don gyaran babur din. Ka ga bayan shekara guda, mutum zai samu fiye da Naira dubu 700 ke nan. Daga nan ne kuma babur din ya zama na direban. Ka ga da haka mun samar da ayyukan yi ga direbobin keke guda 106.”
daya daga cikin direbobin da suka amfana da wannan shirin shi ne: Kashim Tahir wanda yake da mata biyu da kuma ’ya’ya biyar. Ya ce: “Na amfana matuka da wannan kamfanin na Babagana. Ana ba mu kekunan ne mu rika biyan Naira dubu 17,500 kowane mako da shirin bayan shekara guda sun zama namu,” kamar yadda Tahir ya bayyana cikin annashuwa.
Abdulkarim Useni wanda yake da ’ya’ya biyu shi ma yana aiki ne a kamfanin. Ya ce bayan ya kasance direban keke a kamfanin har sau biyu da kuma mallakarsu daga karshe. Yanzu shi ne manajan kamfanin mai kula da bangaren kayan gyara.
Babagana ya ce daga kafa kamfanin zuwa yanzu, direbobi akalla guda 500 sun amfana da shirin. “A yanzu haka muna da ma’aikata 130. Muna da baburan Adaidaita Sahu akalla guda 116,” kamar yadda ya bayyana.
Har ila yau, Babagana ya ce yana da burin samar wa mutane akalla dubu biyar aikin yi nan da shekara biyar.
Daga nan ya ce shawarsa ga matasa wadanda suka kammala karatunsu shi ne su fara dogaro da kansu ta hanyar kafa kananan sana’o’i. Ya ce “karamar harkar ce take zama babba wata rana.”