✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ma’aikatan WAEC ke taimaka wa satar jarabawa

Hukumar Shirya Jarabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) ta bayyana yadda wasu jami’anta ke taimakawa wajen satar amsar satar jarabawa. Hukumar ta ce ta bankado yadda…

Hukumar Shirya Jarabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) ta bayyana yadda wasu jami’anta ke taimakawa wajen satar amsar satar jarabawa.

Hukumar ta ce ta bankado yadda wasu wakiltanta masu kula da daliban da ke rubuta jarabawa ke bari dalibai suke fitar da tambayoyi domin samun satar amsoshi ta barauniyar hanya.

Kakakin WAEC a Najeriya Kakakinta a Najeriya, Demianus Ojijeogu, a cikin wata sanarwar ya ce an kama wasu da ke taimakon masu “satar amsar jarabawar a jihohin Nasarawa, Ribas da Bauchi kuma za a gurfanar da su a kotu”.

Ya yi bayanin ne a yayin da rahotanni ke yaduwa kan bullar takardun tambayoyin jarabawarta lokacin da da aka fara a ranar 17 ga watan Agusta, 2020 ke gudana.

Hakan ya sa ake zargin jami’an hukumar da sace takardun tambayoyin jarabawar tun kafin ranar yin jarabawar darussan.

Sanarwar da ya fitar a ranar Juma’ar, ta ce babu wata jarrabawar da aka fitar ko aka sace kafin lokacinta.

Demianus ya ce amma akwai bara gurbi cikin wakilan hukumar da a wasu lokutan suke bai wa dalibai damar daukar hoton takardun tambayoyin a lokacin da jarabawar ke gudana kuma su tura wa wasu da ke taimaka masu a waje.

Ya ce ana turo wa da daliban amsoshin ne ta sakon waya ko kafafen sadarwa na zamani, wanda a cewarsa shiga dakin jarrabawa da wayar hannu ma ya saba wa dokokin da hukumar.