Wani lokacin mutane ba sa son a zauna lafiya; Kusan kowane lokaci akan samu masu tayar da kurar siyasa a Jihar Kano, musanman a kafafen watsa labarai na zamani, inda suke fara zunguro rikicin zage-zagen siyasa.
Daga nan sai su janye jiki su bar ’yan bana bakwai na bangarorin siyasar da aka taba ko tsokana da cin zarafin iyayensu da jagororinsu na siyasa, wanda hakan kuskure ne.
- Shaguben Shekarau ga Ganduje: Wane ne jagoran cushe-cushe?
- DPO ya lashe musabakar Alkur’anin ’yan sanda ta farko a Kano
Siyasar nan fa babu wani mutum da ba ya neman mafitarsa a cikinta bisa irin fahimtarsa, hakan kuma ya zama ruwan dare a wajen ’yan siyasa manya da ’yan jagaliyarsu.
Duk wanda ya ga hanya ko zuciyarsa ta raya masa sai ya sauya sheka ko ubangida, ala-barshi idan ya gama zagayensa, kaddarar haduwa ta kara hadowa shi da wanda ya ci zarafi jiya a kuma zo a tafi tare; Har takai an saba da yin hakan ya zama jiki a rayuwar ’yan siyasa da mabiyansu.
Don Allah ku fahimci lamarin nan da kyau, babu wani dan siyasa da bai rawa a layinsa na siyasa, don haka ku daina ji a ranku cewa duk wanda ya bar gidanku na siyasa kamar ya tafka babban sabo ko ridda.
Yadda Kwankwaso ya zama Uban Siyasar Kano
Juye-juyen siyasar Kano a fakaice ya sa kowane dan siyasa a Kano ya zama yaron Kwankwaso.
Yanzu haka idan ba ka gidan Kwankwaso to kana gidan Ganduje, kuma Gandujen nan daki ne guda a gidan siyasar Kwankwaso, tunda yaron Kwankwaso ne.
Su Shekarau da su Takai da ire-irensu da suke tare da Ganduje ko APCn Kano, kuma duk jikoki ne a gidan Kwankwaso, tunda juyin siyasa ya mayar da su ’ya’yan Ganduje.
Gandujen nan kuma babban da ne ko yaro a gidan Kwankwaso, su kuma irin su Abba Gida-gida da su Malam Abdullahi Rogo da Alhajin Baba da su Tukur Fagge da Ali Madaki kannen shi Gandujen ne.
Don haka mene ne laifin masu sauya shekar siyasa ko ubangida a nan?
Don Allah ku daina yunkurin tayar da fitina a da’irar siyasar Kano ta soshiyar midiya.
Ku mayar da hankali wajen nuna wa ’yan uwa mabambanta ra’ayi muhimmancin zumunci da kaunar juna a tafarkin dimokuradiyya ba tare da an ci zarafin kowa ba, kuma kowa ya samu sukunin gudanar da ra’ayinsa kamar yadda ya zaba.