✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kungiyar ’yan Arewa suka mallaki muhalli a Ekiti

Alhaji Adamu, shugaban kungiyar ‘yan Arewa mazauna Jihar Ekiti ya shaida wa Aminiya alfanun da suka samu a sakamakon kungiyar da suka kafa ta taimakon…

Alhaji Adamu, shugaban kungiyar ‘yan Arewa mazauna Jihar Ekiti ya shaida wa Aminiya alfanun da suka samu a sakamakon kungiyar da suka kafa ta taimakon kai da kai.
Ya ce kimanin shekaru goma da suka wuce ’yan Arewa na zaman kara zube ne a jihar, “musanman a babban birnin jihar wato Ado Ekiti. A wannan lokacin mutum biyu ne kawai ’yan Arewa masu gidajen kansu. Ba mu mallaki ko rumfa daya a kasuwa ba, don haka muka ga ya dace mu kafa kungiya. Sai aka zabe ni na jagoranci kungiyar, kodayake da fari na so na ki duba da irin harkokin da ke gabana amma da aka matsa sai na yarda kuma ya zuwa yanzu babu abin da za mu ce sai dai mu gode wa Allah.  Tun a shekara ta 2000 kungiyarmu ta yi cinikin wani katafaren fili bayan mun biya kudin, mun fara aiki sai muka gane ashe filin na gwamnati ne, wanda ya karbi kudinmu damfararmu ya yi. Daga nan na je na sami gwamnan jihar na wannan lokacin na fada masa mun sayi filin ne don yi wa ’yan Arewa muhalli da kasuwa. Sai ya ce mu je mu bi ka’idar mallakar fillin, in mun yi haka za a ba mu wajen, shi kuma wancan mutumin da ya karbi kudinmu, mu je ya dawo mana da su.
“A haka na bi duk mataken da ake bi har Allah Ya taimake mu muka mallaki wajan, gwamnati ta ba ni cikakkun takardun mallaka. Shi kuwa wancan mutumin da ya karbi kudinmu da farko, muka rabu da shi  tun daga wannan lokacin muka dinga yanka fulotu, muna bai wa ’yan Arewa suna gina gidaje ba tare da mun karbi ko sisin kwabo ba. Kuma har gobe kyauta muke ba da fili, muddin mutum zai gina ya zauna ne, in dai har dan Arewa ne. A yanzu ’yan Arewa sun mallaki gidaje sama da 100 a wannan yunkuri namu. Muna kuma da kasuwanni a wajen da mayankar shanu da kasuwar kayan gwari da ta shanu da masallatai da sauran kayan more rayuwa.” Inji shi.
Aminiya ta samu halartar sabuwar unguwar Hausawan Ado Ekiti, wacce take a unguwar Fago, wacce ba ta wuce nisan tafiyar mintuna 15 daga kwaryar birnin Ado Ekiti a mota ba. Na ga tarin sabbin gidajen ’yan Arewa da kasuwanninsu da masallatai, jama’a na ta hada-hada. Wasu daga cikinsu da muka tattauna, sun yaba wa shugaban kungiyar bisa wannan gata da ya yi musu. Sun kuma yi kira ga gwannatin jihar da ta hada yankin da wutar lantarki, domin a cewarsu babbar matsalarsu ke nan, rashin wutar lantarki.
Kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, bayan zaben 2015 ne Gwamnan Jihar Ayodele Fayose ya ba da umarnin rushe tsohuwar unguwar da ’yan Arewan ke zaune, inda a nan ne suke kasuwancinsu. Tun daga wannan lokacin ne da yawansu suka yi kaura zuwa sabuwar unguwar ta Fago. Sai dai har ya zuwa yanzu akwai daidaikunsu da suke adawa da sabuwar unguwar, bisa dalilansu na cewa ba za su bar inda suka saba ba, su koma sabon waje.